Gawuna kawai forever

Gawuna kawai forever Allah ya qara wa Dr. Naseru yusuf Gawuna lpy amen amen
Gawuna kawai forever
(11)

Mai Girma Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya na jam'iyyar NDC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya karɓi zaiyarar kungiyar Kwank...
04/09/2026

Mai Girma Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya na jam'iyyar NDC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya karɓi zaiyarar kungiyar Kwankwasiyya Red-Line ƙarƙashin jagorancin Hon. Sadik Nahaja waɗanda s**a zo har gida domin jaddada ƙarfafa zumunci da tattauna muhimman batutuwan da s**a shafi siyasa da ci gaban al’umma, adaren Juma'a nan.

Abubakar Musa DK
Media Aide to H.E Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.
4/Satumba/2026.

Wadanan Sune Mutane Yan Asali  Jahar Kano Wanda Mai Girma Dr Naseru Yusuf Gawuna Ya Samarwa Aiki a Mortgage Bank Kuma Ha...
03/09/2026

Wadanan Sune Mutane Yan Asali Jahar Kano Wanda Mai Girma Dr Naseru Yusuf Gawuna Ya Samarwa Aiki a Mortgage Bank Kuma Har Yanzu Suna Aiki A Can Tabbas Mai Girma Dr Naseru Yusuf Gawuna Idan Yazama Sanatan Kano ta Tsakiya Tabbas Zai Kawo Wa Jahar Kano Cigaba da Kasa Baki Daya Da Yardar Allah

Na Rantse Da Allah Nidai Bazan Taba Yafe Maka ba Kuma Zaku Yafe Masa ko Aa
03/09/2026

Na Rantse Da Allah Nidai Bazan Taba Yafe Maka ba Kuma Zaku Yafe Masa ko Aa

INASON GAWUNA KUMA NI GAWUNA BAICI AMANA TA BA BAIYI MUN BUTULCI BAWanan Shine Kalaman Da Mai Girma Dr Abdullahi Umar Ga...
03/09/2026

INASON GAWUNA KUMA NI GAWUNA BAICI AMANA TA BA BAIYI MUN BUTULCI BA

Wanan Shine Kalaman Da Mai Girma Dr Abdullahi Umar Ganduje Yayi Akan Mai Girma Dr Naseru Yusuf Gawuna Bayan Tambayar sa Da Yan Jarida S**ai Akan Ko Gawuna Yayi Masa Butulci.

Ita Kwa(Abida) Kalaman Da Uban Gidanta Yayi Akan Ta Na Karshe Bayan Taci Amanarsa Ta Koma Wata Jam'iyyar Shine (ABIDA BUTULU CE MACIYA AMANA ) Wanan Sune Kalaman Da Mai Gidan ta Yay Akanta Da Yan Jarida S**a Tambaye Shi.

Allah ka Kawo Mana Karshen Mulkin Abida Amen

03/09/2026

Insha Allahu Abba Gida Gida ne Zai Fara Faduwa Zabe a Cikin Gwamnonin Arewa Duk Mai Kaunar Annabi Yace Amen

03/09/2026

Naji Ance Abida Ta Siyo Hular Kwano Tirela 2 Domin Rabawa Mutanan ta Domin Gujewa Jifan Da Za ai Musu a Ranar Kamfen 🤣🤣🤣

Irin Hallancin Da Mai Girma Kwankwaso Yayi Mana Lokacin Da Jam'iyyar Da Muke S**a Nuna Bamu da Kima a Wajen su Haka a Lo...
03/09/2026

Irin Hallancin Da Mai Girma Kwankwaso Yayi Mana Lokacin Da Jam'iyyar Da Muke S**a Nuna Bamu da Kima a Wajen su Haka a Lokaci Daya Muka Dawo Jam'iyyar NDC Wajen Mai Girma Kwankwaso Haka ya Karbe Mu Hannu Biy Biyu Sanan Ya dauki Babbar Kujera Ya Bawa Mai Gidan Mu Dr Naseru Yusuf Gawuna Ta Sanatan Kano ta Central Kujerar Da Kowanne Dan Siyasa Yake Fatan Yasamu a Haka Mai Girma Kwankwaso Ya Tsaya Tsayin Daka Akan Dole Sai An Bawa Gawuna Wanan Kujerar, Wanda Yayi Maka Wanan Hallacin Shine Kuke Tunanin Dr Naseru Yusuf Gawuna Zai Bari Ya Koma wata Jam'iyyar To Wanan Bazai Taba Yiwuba Mai Gidan Mu ba Butulu Bane Shi Magana Daya Yake Kuma Baya Magana Biyu Saboda Haka Mai Raba Mai Girma Kwankwaso da Gawuna Saidai Mutuwa Wlh

02/09/2026

Naji Ance Kawu Sumaila Zai Koma Jam'iyya Mai Alamar Rogo 🤣🤣🤸‍♂️

SANARWAR MANEMA LABARAI TA HUKUMABATUN: BARIN JAM’IYYA DA WATA ƘUNGIYA TA YI BA ASARA BA CE A GARE MU — BAYANIN GASKIYA ...
02/09/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI TA HUKUMA

BATUN: BARIN JAM’IYYA DA WATA ƘUNGIYA TA YI BA ASARA BA CE A GARE MU — BAYANIN GASKIYA KAN ABIN DA AKE KIRA “GAWUNA TEAM” DA SAKE TABBATAR DA CIKAKKEN SHIRIN NDC NA ZABEN 2027

Hankalin Kwamitin Gudanar da Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna ya kai ga wasu rahotanni da kalamai masu yaɗuwa a kafafen yaɗa labarai daban-daban, waɗanda ke ikirarin cewa wasu daga cikin “manyan jiga-jigan Gawuna” sun fice daga Nigeria Democratic Congress (NDC), kuma suna shirin komawa All Progressives Congress (APC) bayan wata ziyarar nuna goyon baya da s**a kai wa Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Domin fayyace gaskiya da kuma kare al’umma daga yaudarar siyasa, muna bayyana karara cewa ƙungiyar da ake kira “Gawuna’s Team” da ake ta magana a kanta a kafafen yaɗa labarai, ta dade da raba gari da sahihin tsarin siyasar Mai Girma Dr. Nasiru Yusuf Gawuna. Sun rabu da wannan tsarin tun a watan Yuni, bayan da Mai Girma Dr. Gawuna ya yi watsi da wasu buƙatunsu na kashin kansu waɗanda ba su da wani ingantaccen dalili. Hakan ya sake nuna irin mutuncinsa, gaskiyarsa da kuma tsayuwarsa kan ƙa’idojin siyasa.

Babban abin da ya haifar da rashin jituwar da aka samu tsakanin Mai Girma Gawuna da waɗannan mutane shi ne yadda s**a fara yin wasu tuntuɓar sirri da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ba tare da saninsa, amincewarsa ko izinin Dr. Gawuna ba. Sun yi ƙoƙarin shawo kansa ya karɓi tikitin ADC na takarar Gwamnan Kano. Sun kuma yi masa alkawarin cewa ADC za ta ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓensa gaba ɗaya, tare da tanadar musu guraben takarar majalisa domin biyan buƙatun siyasar kashin kansu, da kuma wasu alawus-alawus ko wasu abubuwan alfanu.

Bayan da waɗannan yunƙure-yunƙuren da aka yi ba tare da izini ba s**a gaza, ƙungiyar ta mayar da hankalinta wajen shirya komawa APC. Yayin da mutane uku daga cikin wannan rukuni s**a zaɓi ci gaba da kasancewa cikin tsarin NDC, sauran kuma s**a ci gaba da neman wata hanyar siyasa da za ta biya musu buƙatunsu na kashin kansu.

A bayyane yake cewa ayyukansu sun fi karkata ne ga son zuciya da neman moriyar kansu, maimakon wata manufa ta siyasa ta bai ɗaya ko kuma biyayya ta gaskiya ga Mai Girma Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

Yayin da muke ci gaba da gina ƙarfin siyasa da shirye-shiryenmu domin babban zaɓen 2027, muna tabbatar wa dukkan ‘yan jam’iyya, masu ruwa da tsaki na matakin ƙasa da kuma magoya bayanmu masu kishin gaskiya cewa tsarin gudanar da ayyukanmu, tsarin yaƙin neman zaɓe da kuma dukkanin tsarin cikin gida sun kafu ne tun kafin waɗannan mutane su bar tsarin.

Saboda haka, ba mu da wata fargaba game da yiwuwar fitar wasu muhimman bayanan siyasa ko amfani da su wajen kawo cikas ga shirye-shiryenmu na tunkarar zaɓe.

Bugu da ƙari, tafiyar siyasar Gawuna na ci gaba da samun gagarumin ci gaba cikin sauri. Kullum muna ƙara maraba da manyan ‘yan siyasa, shugabannin al’umma da kuma ƙwararrun masu tattara magoya baya daga matakin ƙasa a dukkan ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

Waɗannan sabbin shigowa da ake samu akai-akai sun fi maye gurbin duk wani gibi da ake tunanin ficewar wannan rukuni ta haifar, tare da ƙara ƙarfafa tafiyarmu da kuma tabbatar da cewa muna kan hanya madaidaiciya zuwa nasara a zaɓen 2027.

Muna kira ga al’ummar Kano, masu lura da harkokin siyasa da kuma kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da duk wani ikirari da ke danganta wannan rukuni da Mai Girma Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ko kuma sahihin tsarin gudanar da ayyukan NDC.

Abin da muka mayar da hankali a kai shi ne samar da ingantaccen shugabanci mai ma’ana, da kuma kawo ci gaba na gaskiya ga Jihar Kano.

Sa hannu:

Dist. Sanata Saleh Adamu Kwaru
DG/Chairman, Gawuna Campaign Coordinating Team

02/09/2026

Yaran Abida Sunata Kirani Wai akan Dole Saina
Mayar d Machine Din Da S**a Bani Ni Kuma Nace Naki na Mayar naci Banza 🤣🤣🤣

Address

Kofar Ruwa
Kano
700101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gawuna kawai forever posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share