Hukumar Zakkah Da Hubusi Ta Jihar Kano

Hukumar Zakkah Da Hubusi Ta Jihar Kano Hukumar Zakka da Hubusi ta Jihar Kano.

HUKUMAR ZAKKA TA KANO TA SAMU ƘARIN HUBUSI.Hukumar Zakka da hubusi ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Shugaban hukumar F...
14/01/2023

HUKUMAR ZAKKA TA KANO TA SAMU ƘARIN HUBUSI.

Hukumar Zakka da hubusi ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Shugaban hukumar Farfesa Ibrahim Muazzam Mai bushira ya jagoranci jami'an hukumar wajen duba wani hubusi na gida da wani bawan Allah da ya rasu ya bar wasiyya domin barinsa a matsayin hubusi ƙarƙashin hukumar ta zakka.

A yayin wannan ziyara ta gani da ido, Farfesa Mai Bushra yana tare da Kwamishinonin hukumar da Daraktocinsa da kuma sauran ma'aikata. Inda s**a duba wannan gida domin ganin yadda yake tare da tsara abin da ya dace a yi da shi.

A ƙarshe an yi addu'a ga wannan mamaci bisa ga wannan aikin alkhairi da ya bayar da wasiccin a yi da dukiyarsa.

HUKUMAR ZAKKA TA KARBI WANI HUBUSI DA AKA YI, SAMA DA SHEKARU 70.Hukumar Zakkah da Hubusi ta jihar Kano ta karbi wani Hu...
04/09/2020

HUKUMAR ZAKKA TA KARBI WANI HUBUSI DA AKA YI, SAMA DA SHEKARU 70.

Hukumar Zakkah da Hubusi ta jihar Kano ta karbi wani Hubusi na Masallaci da Makaranta da aka yi kimanin shekaru 70 da s**a wuce.

Da yake Gabatar da jawabi yayin mika wannan Hubusi ga Hukumar ta Zakkah, Alhaji Sa'idu Dattijo Adhama ya bayyana cewa wadannan wurare asali gidaje ne na zawiyyar Tijjaniya, inda Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi na 1 murabus ya siyi wurin aka sallami magada sannan ya bayar da wurin a matsayin Hubusi, inda daga bisani shi ma Alhaji Sa'idu Dattijo Adhama ya sayi wani bangare na wurin shi ma ya barsu a matsayin Hubusi. A lokacin Mai Martaba Sarki Alhaji Ado Bayero ne s**a bukaci da a Gina musu Makaranta, Kuma aka Gina ta kamar yadda take a yanzu.

Alhaji Sa'idu Dattijo Adhama ya ce sun yi tunanin mika wannan Hubusi ne ga Hukumar Zakkah domin kasancewar sune su ke da alhakin kulawa da ita Kuma domin kaucewa matsalolin da ka iya zuwa ko nan gaba.

Da suke karbar wannan Hubusi, Shugabannin Hukumar ta Zakkah bisa jagorancin Shugabanta, da Mataimakin sa da kwamishinonin Hukumar biyu da Kuma Babban Darakta, sun yabawa dukkan iyalin wannan Gida bisa ga yadda s**a Mika wannan Hubusi a gare su.

17/08/2020

Tattaunawar da Gidan Rediyon Aminci s**a Gabatar da Kwamishina na 2 a Hukumar Zakkah da Hubusi ta jihar Kano, Imam Muhammad Albakry Mika'il. Inda ya yi bayani game da ayyukansu da Kuma irin tanadin da Hukumar Zakkah ta yi ga Mabukata na jihar Kano.
A yi sauraro lafiya.

A saurari hira ta musamman da Kwamishina na biyu a Hukumar Zakkah da Hubusi na jihar Kano Imam Muhammad Albakry Mika'il,...
15/08/2020

A saurari hira ta musamman da Kwamishina na biyu a Hukumar Zakkah da Hubusi na jihar Kano Imam Muhammad Albakry Mika'il, Wanda zai Gabatar kamar haka;
A Aminci Radio da karfe 10-11 na dare. A yi sauraro lafiya.

07/08/2020

Hukumar Zakkah da Hubusi ta jihar Kano tana gabatar da sakon barka da Juma'a ga dukkan Musulmi Maza da Mata. Da fatan mun yi sallar Juma'a lafiya, Allah ya karbi dukkan ibadunmu Amin.

Haka kuma muna kara yin tunatarwa ga 'yan uwa Musulmi mu dage da yawaita salati ga Shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wa sallam domin dacewa da alkhairan da ke cikin wannan yini, domin kuwa akwai wani lokaci da Allah yake amsa addu'ar bayinsa a wannan rana, don haka mu dage kada mu yi sake.

Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya, Allah ya yi mana maganin dukkan abin da yake damun mu.

04/08/2020

Amadadin Hukumar Zakkah da Hubsi ta jihar kano muna yiwa al,umar musulmi Barka da sallah Allah ya maimaita mana.

04/08/2020

Address

Kano
700101

Telephone

+2347035700101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hukumar Zakkah Da Hubusi Ta Jihar Kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Hukumar Zakkah Da Hubusi Ta Jihar Kano:

Share