14/02/2024
BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO, ABBA KABIR YUSUF
Mai girma Gwamna ya akaji da jama'a? Allah Yayi jagora, ameen.
Sa'annan muna tayaka murna da fatan alkhairi bisa samun nasarar cigaba da mulkin jahar Kano mai albarka.
Mai girma Gwamna wani abune yake faruwa mai k**a da 'Rijiya ta bada ruwa amma guga na ƙoƙarin hanawa".
Mutane 1,500 suna cikin wani hali!
Mai girma Gwamna a ranar Juma'a 24 ga watan Nuwambar shekarar 2023., sababbin ma'aikatan da kabada umarnin a tantance aka shelanta dawo da mutane 9,333 bakin aiki databbatarwa da duniya cewa sun cancanci a ɗaukesu aikin gwamnati. Bayan ɗan lokaci an fitar da jerin sunayen waɗanda s**a tsallake a inda dama akwai waɗanda ba a biyansu albashi sak**akon rashin Biodata, amma a lokacin wannan sanarwa daga bakin Dr. Abdullahi Baffa Bichi yace irin waɗancan ma'aikata an umarci ma'aikatar kula da albashin ma'aikata dasu gayyace su domin shigar dasu tsarin biyan albashi.
To, mai girma Gwamna yau kimanin sati takwas kenan waɗannan bayin Allah suna gararamba suje aiki sannan suyi bibiya amma kullum haƙuri ake basu a yayinda takwarorin su tuni anci gaba da biyansu tsawon wata uku baya.
Mai girma Gwamna muna kirada a dubi halinda dubban mutane ke ciki sak**akon rashin aiwatar da umarnin daka bayar na a sanyamu a tsarin biyan albashi. Wanda hakan ya jefa mana shakku a zukatanmu.
Muna kira ga mai girma Gwamna ka duba koken kimanin mutum 1,500 daga ma'aikatu daban-daban ka tsawatar akan wannan al'amari da ayi ƙoƙari muma muga mun wuce wannan bigire.
Daga ƙarshe muna maka fatan alkhairi da addu'ar gamawa lafiya.
Zakari Ya'u Hassan Rimin-Gado
08160559991
Cc
Sanusi Bature D-Tofa
Barr. Muhuyi Magaji Rimingado
Arewa Radio 93.1
Premier Radio
Solacebase Hausa
Abdullateef Abubakar Jos
Nasir Salisu Zango
Dala FM Kano