20/05/2026
NDC ta tantance Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa daya tilo na jam'iyyar
Kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ya amince da Peter Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa guda daya tilo kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Obi ya isa hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja da misalin karfe 6:45 na yammacin ranar Talata tare da rakiyar Sanata Victor Umeh.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya gurfana a gaban kwamitin tantancewar karkashin jagorancin tsohon ministan ilimi, Sam Egwu.
Da yake magana bayan tantancewar, Egwu ya ce kwamitin ya gamsu da yadda Obi ya amsa tambayoyin da aka yi masa, yana mai cewa ya cika dukkan sharuddan kundin tsarin mulkin Najeriya da dokar zabe.
A cewarsa, kwamitin ya tabbatar da Obi a matsayin wanda ya cancanci shiga zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar domin zaben shekarar 2027.
Daga nan ne aka mika wa Obi takardar shaidar amincewa tare da fom din tsayawa takara mai lamba 001 na jam’iyyar.
A ranar Lahadi 17 ga watan Mayu ne Obi ya karbi fom din nuna sha’awa da na takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC kafin wa’adin farko da aka sanya.
Sai dai a ranar Litinin jam’iyyar ta kara wa’adin karbar fom ga sauran masu neman takara zuwa ranar 24 ga watan Mayu, tare da bayyana cewa karbar cikakkun fom daga wadanda aka tantance zai fara daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Mayu.
Duk da haka, jam’iyyar ta ce ba za a kara wa’adin karbar fom din takarar shugaban kasa ba domin tuni an rufe shi.