03/07/2026
Shugaban Jam'iyyar NDC na Jihar Kano, Hon. Husaini Isah Mai Riga, Ya Mika sakon Ta'aziyyar Rasuwar Alhaji Mahadi Sani Dan Bappa.
Shugaban Jam'iyyar NDC na Jihar Kano, Hon. Husaini Isah Mai Riga, ya bayyana matuƙar alhini da jimamin rasuwar Alhaji Mahadi Sani Dan Bappa, Shugaban Sashin Mulki da Gudanarwa na Express Radio, wanda Allah Ya yi wa rasuwa.
Hon. Husaini Isah Mai Riga ya bayyana marigayin a matsayin mutum nagari, mai ƙwazo, gaskiya da kishin aikin jarida, wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen bunƙasa harkokin yaɗa labarai da wayar da kan al'umma.
A madadin jam'iyyar NDC ta Jihar Kano, shugabanninta, 'yan takara, mambobi da magoya baya, Hon. Husaini Isah Mai Riga ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan marigayin, shugabanci da ma'aikatan Express Radio, abokansa da daukacin al'ummar Jihar Kano bisa wannan babban rashi.
Ya yi addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa Alhaji Mahadi Sani Dan Bappa, Ya yalwata masa rahama, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, sannan Ya bai wa iyalansa da al'ummar da ya bari haƙurin jure wannan rashi.
"Lallai dukkan mai rai mamaci ne. Muna roƙon Allah Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya sanya wannan rashi ya zama kaffara gare shi, Ya kuma kare mu baki ɗaya da kyakkyawan ƙarshe."
Sa Hannu,
Adam Said Adam,
Mataimakin na musamman ga,
shugaban jam'iyar NDC Kano,
Hon Husaini Isah Mai Riga.