25/08/2026
Shugaban Jam’iyyar NDC na Jihar Kano, Hon. Husaini Isah Mai Riga, ya halarci babban gangamin taron ƙaddamar da ƙungiyar Obi/Kwankwaso Inter Community Alliance Network da aka gudanar a yankin Sabon Gari, Kano. Taron ya samu halartar dimbin magoya baya da masu ruwa da tsaki, inda aka jaddada muhimmancin haɗin kai da ƙarfafa alaka tsakanin al’umma domin samun ci gaba.
Wannan halartar na daga cikin ƙoƙarin da Hon. Husaini Isah Mai Riga ya mayar da hankali a kai wajen bunƙasa da faɗaɗa ayyukan Jam’iyyar NDC a faɗin Jihar Kano. Shugaban ya ci gaba da ƙarfafa haɗin kai da sadarwa da ƙungiyoyi da al’ummomi daban-daban, domin samar da ingantacciyar fahimta da haɗin gwiwa wajen gina jam’iyyar da kuma ƙarfafa matsayinta a tsakanin al’ummar jihar.
The Chairman of the NDC in Kano State, Hon. Husaini Isah Mai Riga, attended the grand launch of the Obi/Kwankwaso Inter Community Alliance Network held in Sabon Gari, Kano. The event brought together supporters and stakeholders, with emphasis on unity, community engagement, and cooperation for the development of the people.
His attendance is part of the initiatives the NDC Kano State Chairman has continued to prioritize towards strengthening and expanding the party across Kano State. Hon. Husaini Isah Mai Riga has remained committed to engaging with different communities and groups, building stronger relationships, and promoting unity as part of efforts to further advance the growth and development of the NDC in the state.
Adam Said Adam,
Media Aide.