Siyasar Kano Update

Siyasar Kano Update Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Siyasar Kano Update, Political organisation, Yalwa Unguwar Kulkul, Kano.
(2)

04/09/2026

Gobe APC a Kano zata karbi muhimman mutane: Kadan daga cikin wadanda za a karba….

1. Sen. Rufa’i Sani Hanga da Mutanen SA

2. Sen. Kabiru Ibrahim Gaya da mutanen sa

3. Hon. Ali Datti Yako, NDC State Deputy Chairman da sauran Exco na NDC

4. Hon. Badaru Umar, former chairman Ungogo LGA da ‘yan tawagar gidan Gawuna

5. Rt. Hon. Isyaku Ali Danja, former Speaker Kano State Assembly da mutanen sa.

6. Hon. Yusuf Bello Danbatta, former deputy gubernatorial candidate na PDP da mutanen sa.

Da sauran su

Sabature

🚨 LABARI CIKIN GAGGAWA | BREAKING NEWSTawagar jagoran siyasa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ta kai ziyarar bangirma ga Mai Gi...
01/09/2026

🚨 LABARI CIKIN GAGGAWA | BREAKING NEWS

Tawagar jagoran siyasa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ta kai ziyarar bangirma ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da Mataimakinsa, Alhaji Murtala Sule Garo, a wani bangare na shirye-shiryen komawarsu Jam’iyyar APC daga NDC.

Tawagar ta samu jagorancin Hon. Muhammad Badaru Umar da kuma Hon. Ali Datti Yako, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar NDC na Jihar Kano.

Ziyarar ta gudana ne a wannan yammaci cikin yanayi na girmamawa da nuna haɗin kai, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC.

🔥 Siyasar Kano na ci gaba da ɗaukar sabon salo!

31/08/2026

Abba Gida Gida ya futo taron Maulud.

Allah ya karba, Ya mai-maita masa kujera.

SAƘON MU NA LABARAI 📢Ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin siyasa masu fafutukar ganin Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagora...
31/08/2026

SAƘON MU NA LABARAI 📢

Ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin siyasa masu fafutukar ganin Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta samu nasara, wato 2 MILLION VOTES FOR AKY 2027, ta gudanar da muhimmin taron tattaunawa domin ƙara ƙarfafa tsarinta da kuma tabbatar da samun gagarumar nasara ga Mai Girma Gwamna a zaɓen shekarar 2027.

Taron ya haɗa shugabannin ƙungiyar daga matakin jiha, ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙungiyar na Jiha, Alhaji Bashir Hamza Batayya, tare da sauran shugabannin ƙungiyar mutum 25.

Daga cikin muhimman abubuwan da aka tattauna a yayin taron akwai bayar da umarnin gaggauta kammala tsarin shugabanci mai mutane 25 a kowace Karamar Hukuma ta Jihar Kano, domin ƙara faɗaɗa tushen ƙungiyar daga sama har ƙasa.

Haka kuma, an fara tattaunawa kan shirye-shiryen yadda ƙungiyar za ta bayar da nata gudunmawa wajen ƙarfafa ayyukan siyasa da kuma shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen da Jam'iyyar APC za ta gudanar a Jihar Kano.

MANUFAR MU A BAYYANE TAKE:

SAMAR WA MAI GIRMA GWAMNA ABBA KABIR YUSUF KURI'U MILIYAN BIYU A 2027! 💪

Wannan ƙungiya ta 2 MILLION VOTES FOR AKY 2027 ta haɗa kai ne domin nuna ƙauna, jajircewa da cikakken goyon baya wajen ganin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sake samun gagarumar nasara a zaɓen shekarar 2027.

Muna addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya albarkaci wannan kyakkyawar manufa, Ya ba mu haɗin kai da nasara, Ya kuma ci gaba da yi mana jagora a dukkan al'amuranmu.

Allah Ya sake bai wa Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf nasara cikin sauƙi, domin Jihar Kano ta ci gaba da amfana da alherinsa da kyawawan ayyukansa. Amin. 🤲

ABBA GIDA-GIDA — MUNA TARE DA KAI! 💪

✍️ Khatimu Kulkul
📅 31 ga Agusta, 2026

Kano ta zama kan gaba wajen kashe kuɗaɗe a fannin ilimi  a zangon farko na 2026Jihar Kano ce ta fi kowace jiha a Najeriy...
30/08/2026

Kano ta zama kan gaba wajen kashe kuɗaɗe a fannin ilimi a zangon farko na 2026

Jihar Kano ce ta fi kowace jiha a Najeriya kashe kuɗi kan harkar ilimi a zangon farko na shekarar 2026, inda ta kashe Naira Biliyan 59.11 .

Bayanan TheCable Index da aka samo daga kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) sun nuna cewa Lagos ce ta zo ta biyu da kashe Biliyan 39.93 , yayin da Delta ta kasance ta uku da Biliyan 33.34.

Oyo ta zo ta huɗu da Biliyan 28.24 , sai Benue da Biliyan 23.92 biliyan, yayin da Abia ta kashe N21.25 biliyan. Ekiti ta kashe N20.19 biliyan, Bayelsa N18.79 biliyan, Kaduna N18.05 biliyan, sannan Bauchi N17.71 biliyan.

Sauran jihohin da s**a kashe kuɗi masu yawa sun haɗa da Adamawa (N16.95bn), Ogun (N16.42bn), Kogi (N15.09bn), Katsina (N14.26bn) da Akwa Ibom (N14.21bn).

A ƙarshen jerin, Cross River ta kashe N3.87 biliyan, yayin da Imo ta kashe N3.52 biliyan.

Bayanan sun nuna cewa Jigawa ba ta samu wani adadin kashe kuɗi kan ilimi a zangon farko na 2026 ba, yayin da ba a saka adadin jihar Rivers cikin bayanan da aka fitar ba.

Ga jihohi 34 da aka samu bayanansu:

1. Kano – N59.11bn
2. Lagos – N39.93bn
3. Delta – N33.34bn
4. Oyo – N28.24bn
5. Benue – N23.92bn
6. Abia – N21.25bn
7. Ekiti – N20.19bn
8. Bayelsa – N18.79bn
9. Kaduna – N18.05bn
10. Bauchi – N17.71bn
11. Adamawa – N16.95bn
12. Ogun – N16.42bn
13. Kogi – N15.09bn
14. Katsina – N14.26bn
15. Akwa Ibom – N14.21bn
16. Nasarawa – N13.85bn
17. Gombe – N12.70bn
18. Osun – N12.42bn
19. Ebonyi – N12.36bn
20. Kwara – N12.09bn
21. Enugu – N9.12bn
22. Ondo – N8.66bn
23. Plateau – N8.46bn
24. Borno – N8.39bn
25. Yobe – N8.33bn
26. Edo – N7.84bn
27. Kebbi – N7.40bn
28. Taraba – N7.38bn
29. Niger – N7.15bn
30. Sokoto – N6.85bn
31. Zamfara – N5.74bn
32. Anambra – N4.79bn
33. Cross River – N3.87bn
34. Imo – N3.52bn

Official dai Anjanja Aminu Warkal 🔥
29/08/2026

Official dai Anjanja Aminu Warkal 🔥

Cikin Ayyukan alkairan da Gwamnan Jihar Kano Alh Abba Kabir Yusuf yake yi, kuyi mana Comments da aikin da ake a Kananan ...
29/08/2026

Cikin Ayyukan alkairan da Gwamnan Jihar Kano Alh Abba Kabir Yusuf yake yi, kuyi mana Comments da aikin da ake a Kananan hukumomin ku, San nan wanne kuke fata Idan an kammala wadan da ake ayi muku?

28/08/2026

Maidugu ne ya fara gabatarwa da Al'umar jihar Kano Asuwaju Bola Tunubu.

Shima ya Yarda da Nagartar sa.

Duk wanda ya gamsu da Abba Gida Gida yana taimakon mutane tare da ayyukan alkairi a jihar Kano yayi mana mana Comments n...
27/08/2026

Duk wanda ya gamsu da Abba Gida Gida yana taimakon mutane tare da ayyukan alkairi a jihar Kano yayi mana mana Comments na fatan alkairi.

PUBLIC ANNOUNCEMENTOFFICE OF THE STATE YOUTH LEADERALL PROGRESSIVES CONGRESS, KANO STATE CHAPTERCALL FOR REGISTRATION OF...
27/08/2026

PUBLIC ANNOUNCEMENT
OFFICE OF THE STATE YOUTH LEADER
ALL PROGRESSIVES CONGRESS, KANO STATE CHAPTER

CALL FOR REGISTRATION OF ALL APC YOUTH SUPPORT GROUPS IN KANO STATE

The Office of the State Youth Leader, APC Kano State hereby announces the commencement of a statewide registration exercise for all APC Youth Support Groups across Kano State.

This exercise is part of the ongoing efforts to properly structure, coordinate, and empower all youth groups working to promote the ideals of our great party and the “Kano First” agenda of His Excellency, Gov. Abba Kabir Yusuf.

REGISTRATION DETAILS

1. Who Should Register:
All APC Youth Support Groups - Male and Female - operating at Ward, Local Government, and State Level are eligible and expected to register. This includes professional groups, market associations, student groups, artisans, and community-based groups.

1. Registration Requirements:
Each support group is to come with:
1. Membership Register with names, phone numbers, Voter Identification Number (VIN)
2. Leadership Structure of not more than 11 people, stating their names, positions, phone numbers, and wards

1. Registration Venue:
APC Party Secretariat, Maiduguri Road, Hotoro, Kano

1. Date:
Commencement: Monday, 31st August, 2026
Closing Date: Monday, 7th September, 2026

1. Time:
10:00am to 6:00pm Daily including weekends

IMPORTANT NOTICE
1. Registration is FREE and MANDATORY for all groups seeking recognition, collaboration, and empowerment opportunities from the Party and Government.
2. All registered groups will be issued a *Unique Registration Code* and captured in the Central Database of the Office of the State Youth Leader.
3. For further inquiries, contact the Office of the State Youth Leader at the Secretariat.

This initiative is designed to bring all youth energy under one coordinated structure for effective mobilization, feedback, and service delivery to our people.

Let us work together to build a stronger APC and a greater Kano.

Signed
State Youth Leader
All Progressives Congress, Kano State

Dated: 27th August, 2026

Salisu Yahaya Hotoro

Address

Yalwa Unguwar Kulkul
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Siyasar Kano Update posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Siyasar Kano Update:

Shortcuts

Share