Kiru Bebeji First -KBF

Kiru Bebeji First -KBF Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kiru Bebeji First -KBF, Political organisation, Kano.

24/06/2026

Kiru -Bebeji

27/05/2026

⏳…!

A wakilcin Kiru da Bebeji, ya kamata mu hankalta domin mu zaɓi nagartaccen shugaba a 2027.Kada ka sayar da mutuncinka sa...
16/05/2026

A wakilcin Kiru da Bebeji, ya kamata mu hankalta domin mu zaɓi nagartaccen shugaba a 2027.
Kada ka sayar da mutuncinka saboda ƴan kuɗaɗen da za a baka.
Makomar al’umma tafi muhimmanci fiye da anfani na ɗan lokaci.

Kiru Bebeji First -KBF

Kiru–Bebeji FIRSTKiru–Bebeji FIRST is not just a movement, it is a struggle for the liberation, dignity, and progress of...
05/05/2026

Kiru–Bebeji FIRST
Kiru–Bebeji FIRST is not just a movement, it is a struggle for the liberation, dignity, and progress of our people.

For too long, the voices of Kiru and Bebeji have been ignored, our potential underutilized, and our future delayed by failed leadership and empty promises. That era ends now.

We are a movement built by the people and for the people determined to reclaim our mandate, restore accountability, and deliver leadership that truly represents the will of the masses. Follow us on Facebook 👇

https://www.facebook.com/share/1BbT6vJM9c/?mibextid=wwXIfr

Political organisation

Kiru Bebeji First -KBF[_/""A bold step to a better future.""\_]Me yasa dayawan mutane suke sunkuya wa farfelar helicopte...
30/03/2026

Kiru Bebeji First -KBF
[_/""A bold step to a better future.""\_]

Me yasa dayawan mutane suke sunkuya wa farfelar helicopter 🚁, duk da suna sane da cewa fankar a saman su take kuma bazata cutar da su ba?

Irin haka ne yake faruwa da al'ummar wannan yanki namu, muta jin tsoron fitowa a aikace mu kalubalanci mulkin rashin adalci, duk da muna sane dacewa masu zaluntar mu basu da komai sai rigar alfarmar da mukayi musu ta hanyar dangwalen kuriar mu.

Mu fito muyi aiki tukuru mu yaki zalunci, mu yaki jamiyancin sak, mu yaki saye da sayarwar kuri'a, mu yaki janye jiki a zabe. Mu jajirce mu karfafa, zabar cancanta na abin da ya bayyana agaremu a cikin yan takara a kowacce kujera, mu karfafi mutanen kirki masu takara a kananan jam'iyyu, mu karfafi al'umma wajen samar da shugabanni masu adalci, gaskiya da rikon amana, mu karfafi al'umma su fahimci karfin ikon dake hannun su.

Mu yi hobbasa wajen samar da gobe mai kyau ga yankin mu, mu yi kokarin kafuwar adalci wanda zai zama silar kawar da matsalar ruwan sha, ilimi, lafiya, noma da kiwo, aikin yi, kasuwanci, tituna da sauran abubuwan da muke da bukata domin samun ingantacciyar rayuwa.

Wannan shine kudirin kungiyar
KIRU/BEBEJI FIRST.

Allah ya bamu nasara🤲

KIRU/BEBEJI FIRST.//A bold step to a better future\\.A kowace al’umma, canji ba ya sauka daga sama kamar ruwan sama; sai...
29/03/2026

KIRU/BEBEJI FIRST.
//A bold step to a better future\\.

A kowace al’umma, canji ba ya sauka daga sama kamar ruwan sama; sai an neme shi a aikace da himma da juriya. A siyasa, matsalar da ta daɗe tana damun alumma ita ce sakaci da rashin tsayawa kan gaskiya. Amma karin magana na cewa: Ruwa baya tsami banza.
Wasu sun daina zabe saboda sun yanke kauna, wasu kuma suna sayar da kuri’arsu saboda talaucin da shugabacin zalunci ya ƙaƙaba musu wasu kuwa rashin fahimta.
Duk abin da ya lalace, akwai dalili. Don haka aikin wannan kungiya shi ne gano tushen matsalolin, sannan ta magance su ta hanyar aiki tukuru da ilimi da wayar da kai.

Wannan kungiya da nake magana a kai tamkar wata shuka ce da ake son dasawa a cikin ƙasa mai wahala, amma idan aka kula da ita da kyau, za ta zama itaciya mai inuwa da amfani ga kowa.

Manufar kafa irin wannan kungiya ita ce ta tara jajirtattun al'umma musamman matasa masu kishi, wadanda za su zama fitila a cikin duhu. Domin kamar yadda ake cewa, Matashi ginshikin al’umma ne, idan ginshikin ya yi ƙarfi, gini ba zai rushe ba.

A karshe mu tuna cewa:
Kuri’a amana ce. Idan aka sayar da ita, ko akayi sakaci da ita ta salwanta kamar an sayar ne ko salwantar da makomar al'umma, da ta ‘ya’ya da jikoki.

Kiru-Bebeji First
A bold step to a better future.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kiru Bebeji First -KBF posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share