Yan Akidar Kwankwasiyya

Yan Akidar Kwankwasiyya This page promotes Kwankwasiyya ideology from grassroot.

KAIMA TUNDA KAMANTA MURADAN AL UMMA KAFADA CIKIN JAM IYAR A P C INSHA ALLAHU SAI UBANGIJI YAKAYAR DAKU BAKIDAYA ALFARMAR...
25/08/2026

KAIMA TUNDA KAMANTA MURADAN AL UMMA KAFADA CIKIN JAM IYAR A P C INSHA ALLAHU SAI UBANGIJI YAKAYAR DAKU BAKIDAYA ALFARMAR SHUGABA ANNABI MUHAMMAD SALLALAHU ALAIHI WASALLAM 2027

"A daina Izgilanci saboda jam'iyar APC tana da Gwamnoni 30, jam'iyyar PDP haka tace a baya, kuma aka kayar da ita, saboda su talakawa su ne masu zaɓe ba Gwamnoni ba.

--Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam'iyyar Apc.

24/08/2026

Da ɗumi-ɗumi: “Na taɓa cire gwamna kan zargin sace Naira dubu ɗari uku N300,000, amma A yau Naira Biliyan dari uku N300bn ba ta isa dalilin cire gwamna ba a Najeriya” — IBB

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya bayyana cewa a lokacin mulkinsa ba a yi mulkin da cin hanci da rashawa ba, yana mai cewa yana alfahari da irin matakan da gwamnatinsa ta ɗauka kan almundahana.

A cikin kalamansa, Babangida ya ce:

“Mu ba ’yan cin hanci da rashawa ba ne. Ina alfahari da faɗin haka, domin ni ko yaushe ina karatun jarida. Duk abin da na gani a jarida, idan gaskiya ne, zan ɗauki mataki.”

Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin abubuwan da yake alfahari da su shi ne yadda gwamnatinsa ta ɗauki matakin ladabtar da jami’an gwamnati kan ƙananan zarge-zargen almundahana.

A cewarsa, ya taɓa cire wani gwamna daga mukaminsa saboda zargin satar Naira dubu ɗari uku (N300,000).

Sai dai Babangida ya bayyana abin da ya kira babban sauyi a yadda ake kallon almundahana a yau, yana cewa:

“Amma yanzu Biliyan ɗari uku (N300bn) ba ta isa dalilin cire gwamna ba.”

Kalaman na Babangida sun sake buɗe batun yadda ake yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya da kuma irin matakin da ya kamata a ɗauka kan jami’an gwamnati idan aka samu zargin almundahana.

24/08/2026

Beta Edu, ministar da Shugaba Tinubu ya dakatar da ita daga mukaminta a watan Janairun 2024 bisa zargin badakalar kudaden da s**a kai biliyan 585 ta yi nasarar samun babban mukami mai gwabi a kwamitin yakin neman zabensa. Beta Edu wadda sunanta ya fito a lambata ta 97 a jerin sunayen 'yan kwamitin, an ba ta mukamin daraktan wayar da kan matan Nijeriya domin samun tazarcen Tinubu.

24/08/2026

Dan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su tashi tsaye wajen dakile matsalar rashin tsaro da ke ƙara kamari a sassan Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Obi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, inda ya ce hare-haren da ake kai wa al’ummomi na buƙatar ɗaukar matakin gaggawa da kuma haɗin gwiwa daga hukumomin tsaro da gwamnati.

Obi ya yi nuni da hare-haren baya-bayan nan a jihohin Benue, Plateau da Neja, yana mai cewa hukumomi na da alhakin kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.

Allah yakaimu lokacin dangwalan abanbance baccin makaho da mai Ido Kwankwaso ikon Allah ne ubangiji yakunyata mahassadan...
24/08/2026

Allah yakaimu lokacin dangwalan abanbance baccin makaho da mai Ido
Kwankwaso ikon Allah ne ubangiji yakunyata mahassadan sa da namu bakidaya

“Madugu ya fi mu ’yan media, amma mun fi shi ’yan dangwale a Kano.”

— Garzali Musa Obasanjo, Jigo a Jam’iyyar APC.

23/08/2026

YAN AKIDAR KWANKWASIYYA AREWA FROM KANO STATE CHAPTER

Address

No 6 C Gwammaja Tagwayen Gida, Amfani Plaza
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yan Akidar Kwankwasiyya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share