Abba Gida-Gida Young Reformers Congress

Abba Gida-Gida Young Reformers Congress GO AGAIN AKY✌️❤️

1) Bazai iya zuwa Villa ya gana da shugaban kasa ba—— Sai gashi yaje.2) Bazai Iya barin NNPP ba—— Sai Gashi ya barta. 3)...
13/05/2026

1) Bazai iya zuwa Villa ya gana da shugaban kasa ba—— Sai gashi yaje.

2) Bazai Iya barin NNPP ba—— Sai Gashi ya barta.

3) APC bazasu karbeshi ba sunce sai yazo da kwankwaso ———— Sai gashi sun karbeshi Hannu bibiyu

4) Bazasu Bashi Jamiyya ba———- Sai gashi Ya karbi 60%

5) Ganduje bazai yarda su Bashi Jagoranci ba———- sai Gashi Sunce shine Jagoransu yadda ya dama haka za’a sha.

6) Bazasu bashi takara ba ————- Sai gashi duk Yan takarar sun Janye sunyi masa Mubaya’a.

7) Saidai ya shiga primary election ————- sai Gashi duk yan takarar sun Janye sunce basu yarda wani yayi takara dashi ba.

8.) Tunda ya shiga APC yanzu zai Daina Ayyukan da yakeyi a gari ya koma Rabon Kudi————- Sai gashi Kullum sabbin Ayyuka ake sake fitowa dasu.

9) Bazai Iya Fitowa ya shiga Mutane ba saboda baa sonsa——— sai gashi duk inda yaje sai son Barka.

10)Bazai Iya zaben Deputy Gwamna ba saboda rikici, duk wanda ya dauka matsala ne, Jamiyyar zata lalace————- Sai gashi anyi lami lafiya, Harda Sanata Barau a Gurin Rantsuwar Murtala sule Garo

11)Ai bazai iya yin sulhun Yan takara ba———— Sai gashi anyi Lafiya

12) Ai duk wanda bai samu takara ba zai fice, Jamiyyar ta tarwatse ———- Sai gashi anyi sulhun Takara lafiya an gama Lafiya.

13) Bazai Iya sulhunta Rikicin ATM Gwarzo da Barau ba———— Sai Gashi Jiya anyi sulhu kowa na Murna.

Yanzu H.E Engr. Abba Kabir Yusuf Shine Maradonan Siyasar Jihar kano, Kowa da lokacinsa, Yanzu Allah shi ya Arawa dama kuyi Hakuri ku sallama.

Iya wannan Yakamata yan NDC su gane duk tunaninsu akan Mai girma Gwamna Alhaji Abba kabir Yusuf ba daidai bane.
Allah ne yace ya karrama Dan Adam, Saboda haka ku daina tunanin Kukadai ne ko kuma Jagora ne kawai ya iya, Allah yana bawa kowa Basira da Hikima da Nasara.

14) Zakuce Bazai Iya cin zabe ba———

Allah zai bashi Nasara duba da Irin Ayyukan Alkairi da yakewa Kanawa, Inada Tabbacin Zasu sake zabarsa.

Abba Kafin Allah Ne

AYRC

Me Girma Dan Takarar Majalisar Tarayya Dake wakiltar Gwale Hon. Muhammad Kasim Warure Ya samu damar kasancewa tare da Ma...
28/04/2026

Me Girma Dan Takarar Majalisar Tarayya Dake wakiltar Gwale Hon. Muhammad Kasim Warure Ya samu damar kasancewa tare da Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Eng. Abba Kabir Yusuf da kuma shugabannin jam’iyyarmu mai albarka ta APC Kano.

Wannan lokaci ba kawai hoto ba ne, yana nuna hadin kai, amana, da kuma jajircewar mu wajen ganin an kawo ci gaba ga al’ummarmu Ta Jahar Kano Mai Albarka

A Cewar Hon. Muhammad Kasim Warure

Inda yakecewa muna kara kusantar shekarar 2027, ina nan daram a kan kudurina na samar da wakilci nagari ga al’ummar mazabar Gwale ta Tarayya.

Tare da goyon bayan shugabanninmu da karfin gwiwar al’ummar kasa Tare da Matasa nasara ba kawai mai yiwuwa ba ce tabbatacciya ce Insha Allahu

Tafiya ta fara. Gwagwarmaya na kara bunkasa. Makoma tamu ce, Insha’Allah.

Muhammad Kassim

AYRC

For the progress of the people,For the development of AYRC youths,For the advancement of Kano State,For leadership with ...
23/04/2026

For the progress of the people,
For the development of AYRC youths,
For the advancement of Kano State,
For leadership with true passion and commitment…

Let us stand firm and remain with Abba Kabir Yusuf at all times.

He is a leader with vision, dedicated to bringing real change and sustainable development to both the people and the youth.

AYRC

AG_2027
22/04/2026

AG_2027

Tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya bayyana jin daɗinsa bisa matakin da Gwam...
22/04/2026

Tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya bayyana jin daɗinsa bisa matakin da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ɗauka na miƙa sunansa ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantance shi a matsayin Mataimakin Gwamna.

A cikin wata sanarwa, Garo ya bayyana wannan mataki a matsayin babbar karramawa da kuma nuna amincewa da ƙwarewarsa wajen hidima ga al’umma. Ya ce wannan dama za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da bada gudunmawa ga cigaban Jihar Kano.

Ya kuma miƙa godiya ga shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki da daukacin al’ummar Kano bisa irin goyon baya da addu’o’in da suke ba shi, yana mai cewa wannan tallafi na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa masa guiwa.

Haka kuma, ya yi kira ga dukkan mambobin jam’iyya da sauran al’umma da su ƙara haɗa kai cikin fahimta da zumunci domin tabbatar da cigaban Jihar Kano.

Garo ya jaddada cewa zai ci gaba da sadaukar da kai, biyayya da aiki tuƙuru domin tallafawa manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Abba Kabir Yusuf, tare da bayar da gudunmawa wajen bunƙasa ayyukan raya jihar.

ROAD TO 2027with AYRC❤️
22/04/2026

ROAD TO 2027

with AYRC❤️

21/04/2026

Har Ynz Kungiyar AYRC Batada Sani Akan Makomar ta

Barka da Shigowa Jam'iyyar mu ta APC mai Albarka Mal Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) Kowa ya shaida mal Mu2min kirki n...
19/04/2026

Barka da Shigowa Jam'iyyar mu ta APC mai Albarka Mal Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano)
Kowa ya shaida mal Mu2min kirki ne muna yimasa fatan Alkhairi da fatan Allah yasa Shigowarsa ta amfani jam iyyar dama Al'ummar jihar Kano baki daya.

AYRC

Sa Shiru Hana Kara Hayaki NooUsman Mustapha Jido PA ICT
15/04/2026

Sa Shiru Hana Kara Hayaki Noo
Usman Mustapha Jido PA ICT

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abba Gida-Gida Young Reformers Congress posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share