13/07/2026
Daga KCPC
13/07/2026
KCPC TA GARGAƊI ƳAN KASUWA KAN SAYAR DA GURBATATTU KO MARASA INGANCIN KAYAYYAKI GA MASU SIYE
Sakataren Zartarwa na Hukumar Kare Hakkin Masu Saye ta Jihar Kano (KCPC), Dr. Ibrahim Garba Muhammad, ya gargaɗi ƙananan ƴan kasuwa da su daina sayar da gurbatattu ko marasa ingancin kayayyaki ga masu siye a faɗin jihar.
Dr. Ibrahim Garba Muhammad ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Ƙananan Ƴan Kasuwa ta Jihar Kano a ofishinsa.
Ya ce an kafa Hukumar Kare Hakkin Masu Saye ne domin kare al'umma daga kayayyaki da ayyukan kasuwanci da ka iya jefa lafiyarsu, tsaronsu da tattalin arzikinsu cikin haɗari
Ya ƙara da cewa wajibi ne ƴan kasuwa su tabbatar da cewa kayayyakin da suke sayarwa suna da inganci kuma sun dace da amfanin masu siye.
Sakataren Zartarwan ya yaba da ziyarar da ƙungiyar ta kai, tare da tabbatar musu da cewa hukumar a shirye take ta yi aiki tare da su domin inganta kare haƙƙin masu siye, tabbatar da adalci a harkokin kasuwanci da kuma bunƙasa tattalin arziki.
Babban Mataimaki na Musamman ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano kan harkokin Hukumar Kare Hakkin Masu Saye, Hon. Hassan Sadiq, ya buƙaci ƙananan ƴan kasuwa da su riƙa bai wa hukumar sahihan bayanai game da wuraren da ake sayar da gurbatattu ko marasa ingancin kayayyaki domin ɗaukar matakin da ya dace cikin gaggawa.
Da yake jawabi a madadin shugaban ƙungiyar, Sakataren Ƙungiyar, Abdulrahman Saleh Usman, wanda ya wakilci Shugaban Ƙungiyar, Malam Naziru Abdulkadir Da'awa, ya ce manufar ziyarar ita ce gabatar da ƙungiyar ga hukumar tare da neman ta sa baki kan tashin farashin kayayyakin masarufi, tsadar kuɗin hayar shaguna, da kuma ba ƙungiyar damar shiga cikin harkokin wayar da kan jama'a da sauran ayyukan hukumar.
sa hannu:
Tasi'u Jibo Dawanau
Jami'in Hulɗa da Jama'a
Hukumar Kare Hakkin Masu Saye ta Jihar Kano