04/06/2026
Wayo ko dabarar ka bashi ne ya kaika zuwa ni'imar da kake ciki ba haka xalika bashine zai fitar da kai daga cikin wata jarabtawa da Allah yayi maka ba .
Ibnul Jauziy(RA) ya ce; "Kar da ka rika ganin lokacin bala'i ya yi tsawo har ta kai ka ga gajiya da yawan addu'a, domin an jarabceka da wannan bala'inne kuma a ka bautar da kai da yin hakuri, don haka kar da ka yanke tsammani daga rahamar Allah ko da kuwa jarabawar ta jima."