CRC Media Centre

CRC Media Centre This is official page of community re-orientation council (CRC,), Kano state

Mai girma gwamnan Kano Alhaji Abba K Yusuf ya gwangwaje masu kwaikwayonsa su uku da sabbin mashina da naira dubu ɗari bi...
25/08/2026

Mai girma gwamnan Kano Alhaji Abba K Yusuf ya gwangwaje masu kwaikwayonsa su uku da sabbin mashina da naira dubu ɗari biyar-biyar kowannensu don su sa lamba.

CRC Media Centre

Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na ci gaba da cika alkawuran da ya ɗauka Musamman Akan hanyoyi.Ayyukan hanyoy...
24/08/2026

Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na ci gaba da cika alkawuran da ya ɗauka Musamman Akan hanyoyi.

Ayyukan hanyoyin kilomita 5 da aka mayar da su manyan hanyoyi biyu (dual carriage): Daga cikin hanyoyi 38 da aka gada, an kammala guda 18, guda 17 kuma ana cigaba da aikin su, ya yin da aka soke guda 3 saboda gazawar ’yan kwangila.

Za a sake bayar da waɗannan ayyukan da aka soke ga wasu ’yan kwangila nan ba da jimawa ba domin tabbatar da kammala su. Hanyar ƙaramar hukumar Ghari ma ana ci gaba da aikin ta.

Madalla Da Gwamna Abba

Gwamna Abba K. Yusuf ya cimma wani babban tarihi a harkokin gudanar da mulki: ya kawar da dimbin bashin kudaden alawus n...
23/08/2026

Gwamna Abba K. Yusuf ya cimma wani babban tarihi a harkokin gudanar da mulki: ya kawar da dimbin bashin kudaden alawus na ritaya (gratuity) da fansho da s**a kai biliyoyin naira.

Gwamna Abba ya kuma aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi, sannan ya samar da guraben ayyukan yi a ma’aikatan gwamnati ga dubban matasa.

Dukkan waɗannan an gudanar da su ne da kuɗaɗen cikin gida 100%, ba tare da ɗaukar wani bashi da zai zama nauyi ga al’ummomin da za su zo nan gaba ba.

Madalla Da Gwamna Abba

Ana ci gaba da aikin ginawa da kuma zuba siminti a kan titin masu tafiyar kafa (sidewalk) da aka shimfiɗa da duwatsu a g...
23/08/2026

Ana ci gaba da aikin ginawa da kuma zuba siminti a kan titin masu tafiyar kafa (sidewalk) da aka shimfiɗa da duwatsu a gefen hanyar Airport Road dake birnin Kano.

.

An fara aikin titin  daya tashi daga janbulo first gate (Layin Gidan Sharu Sani) zuwa yamadawa (Bus Stop) Tutu. wanda za...
14/08/2026

An fara aikin titin daya tashi daga janbulo first gate (Layin Gidan Sharu Sani) zuwa yamadawa (Bus Stop)

Tutu. wanda zai hade zuwa janbulo second gate, karkashin jagorancin, Mai girma gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.

CRC Media Centre
14/08/2026

Gwamna Abba Yusuf ya kaddamar da cibiyar kula da masu fama da cutar sikila, ya raba na’urorin auna jini 300.Gwamnan Jiha...
03/08/2026

Gwamna Abba Yusuf ya kaddamar da cibiyar kula da masu fama da cutar sikila, ya raba na’urorin auna jini 300.

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da wata cibiyar musamman da za ta rika kula da masu fama da cutar sikila (Sickle Cell) a jihar.

Cibiyar za ta samar da cikakken kulawa ga masu fama da cutar, ciki har da gwaje-gwaje kyauta, ba da shawarwari, jinya, bibiyar lafiyar marasa lafiya, wayar da kai da kuma kula ta musamman ga masu fama da wannan cuta.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin ta bayyana cewa an kaddamar da cibiyar ne a wani bangare na kokarin gwamnatin Kano na inganta harkokin lafiya a jihar.

A yayin bikin da aka gudanar a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, Gwamna Abba Yusuf ya kuma kaddamar da rabon kayan tallafin kula da mata masu juna biyu, kayan gaggawa na hadura, sabbin zanen gadon asibiti da kuma na’urorin auna karfin jinin mutum masu amfani da fasahar zamani guda 300.

Gwamnan ya ce rabon na’urorin auna jinin ya samo asali ne daga damuwar da ake samu kan yawaitar rasuwar mutane sakamakon hawan jini, inda ya ce matakin zai taimaka wajen karfafa yin gwajin lafiya akai-akai da kuma samar da ma’aikata masu koshin lafiya.

Ya kuma tabbatar da cewa shirinsa na bayar da kayan kula da mata masu juna biyu da na gaggawa kyauta ya taimaka wajen ceton dubban rayuka a fadin jihar, yana mai alkawarin ci gaba da wannan shiri.

Kwamishinan Lafiya na Kano, Dakta Abubakar, ya yaba wa gwamnan bisa kokarinsa na inganta fannin lafiya, inda ya ce asibitoci da cibiyoyin lafiya a jihar sun samu gagarumin sauyi tun bayan fara mulkin gwamnatin yanzu.

Ya bayyana cewa yawan mace-macen mata masu juna biyu ya ragu matuka a karkashin wannan gwamnati, daga sama da 1,300 da aka samu a shekarar 2023 zuwa kusan 300 a shekarar 2026.

Shi ma Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Asibitocin Kano, Dakta Mansur Nagoda, ya ce ayyukan gwamnatin Abba Yusuf sun amfanar da dubban al’umma tare da sauya fannin lafiya a jihar zuwa wani sabon matsayi.


CRC Media Centre

Cigaba da aikin roundabout din Daula tare da sake fasalin sa da Mai girma gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, yake gudanarwa...
03/08/2026

Cigaba da aikin roundabout din Daula tare da sake fasalin sa da Mai girma gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, yake gudanarwa yanzu haka.


Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kaddamar da Rabon Takardun Filaye ga Masu Taimaka Masa da ’Yan Akwatu.A ranar Asabar ne mai g...
03/08/2026

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kaddamar da Rabon Takardun Filaye ga Masu Taimaka Masa da ’Yan Akwatu.

A ranar Asabar ne mai girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon takardun filaye ga masu taimaka masa a gwamnati, wadanda s**a hada da Manyan Masu taimaka masa na Musamman SSAs, SAs, Masu daukowa gwamna rahoto SSRs, SRs, da kuma PAs.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnatinsa na tallafa wa ma’aikata da masu bayar da gudunmawa wajen tafiyar da harkokin gwamnati.

A ranar Lahadi kuma, an ci gaba da shirin inda aka rabawa wasu daga cikin ’yan Akwatu takardun filaye, wadanda adadinsu ya kai kusan 1,600, domin su ma su amfana da wannan shiri.

Masu ruwa da tsaki sun yabawa wannan yunkuri, suna mai cewa zai taimaka wajen samar da damar mallakar gidaje da kuma inganta rayuwar wadanda s**a amfana.

~ CRC Media Centre

26/07/2026
04/04/2026

Abban Kanawa, Mun fito daga filin jirgin tun karfe 02:30 na rana yanzu karfe 07:20 na dare.

Address

Farm Center
Kano
700001

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when CRC Media Centre posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share