27/12/2025
Masha Allah
Allah Yasaka da Alkhairi Jagora
Sponsored: Jagoran Kwankwasiyya na duniya, tsohon Gwamnan jihar Kano kuma tsohon Ministan tsaro, Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya gabatar da ƴan asalin jihar Kano waɗanda s**a kammala karatun digiri na uku mutum 318, waɗanda ya dauki nauyin karatunsu zuwa kasashe goma sha hudu (14) na duniya. Idan baku manta ba, Kwankwaso ya fito da tsarin bada tallafin karatu zuwa ƙasashen waje da kuma cikin gida, wanda aka yi shi bisa cancanta.
Daga cikin wayanda aka dauki cikakken nauyin karatun nasu, guda *20* tini sun kai matakin farfesa, guda *250* sun kai matakin manyan malaman jamiá, kuma suna gab da kaiwa matakin farfesa. Guda *48* suna matakai daban-daban na Jami’a, ma’aikatun gomnati, kamfanoni, da kuma masu kamfanonin kansu.
Jagora Kwankwaso ya gabatar da waɗannan manyan masu ilimi ne a yayin babban taron shekara-shekara na ƙungiyar waɗanda s**a amfana da tallafin karatu a gwamnatin Kwankwasiyya karo na farko karkashin jagorancin Dr. Mansur Hassan.
Taron ya gabata ne a dakin taro na Prof. Hafizu Abubakar dake Jami'ar Northwest da ke Kano, ranar 24 ga watan Disamba, 2025.
A yayin wannan taron, wasu daga cikin masu ilimin dake Nigeria sunyi bayanin nasarorin da s**a samu daga fara kartun nasu zuwa wannan lokaci. Wayanda suke a kasashen duniya daban-daban kuma sunyi nasu bayanin ta na’urar sadarwa ta Zoom). Sun kuma bayyana muhimmancin irin wannan tsarin na gina rayuwar Al’umma.
Ga jerin Farfesoshin da s**a ci gajiyar kamar haka:
1. Assoc. Prof. Engr. Zahraddeen Sufyanu, FUD Jigawa (Artificial Intelligence)
2. Assoc. Prof. Zahraddeen Nasiru Garba, ABU Zaria (Environmental Chemistry)
3. Assoc. Prof. Abdulrahman Abubakar Tahir, AU Katsina (Curriculum Studies)
4. Assoc. Prof. Surajo Sulaiman, NWU Kano (Mathematics)
5. Assoc. Prof. Engr. Ashiru Sani, ADUSTECH Wudil (Civil Engineering)
6. Assoc. Prof. Sulaiman Tukur Abdulkadir, FUD Jigawa (Applied Mathematics)
7. Assoc. Prof. Abdullahi Yusuf, FUD Jigawa (Applied Mathematics)
8. Assoc. Prof. Aliyu Isa Aliyu, NWU Kano (Applied Mathematics)
9. Assoc. Prof. Hamisu Sadi Ali, ABU Zaria, (Financial Economics)
10. Assoc. Prof. Ibrahim Haruna Sani, NWU Kano (Clinical Pharmacology/Public Physician)
11. Assoc. Prof. Zakariya Uba Zango, AU Katsina (Material and Environmental Chemistry)
12. Assoc. Prof. Nafiu Zakari, FUD Jigawa (Health and Medical Geography)
13. Assoc. Prof. Auwal Muhammad, ADUSTECH Wudil (Theoretical and Computational Biophysics)
14. Assoc. Prof. Mukhtar Bello Mai Sudan, BUK (Political Science)
15. Assoc. Prof. Murtala Muhammad, ADUSTECH Wudil (Biochemistry)
16. Assoc. Prof. Muttaqa Uba Zango, ADUSTECH Wudil (Civil Engineering)
17. Assoc. Prof. Ahmadu Sale, ABU Zaria (Veterinary Pathology)
18. Assoc. Prof. Suleiman Danladi, BUK (Pharmaceutical Sciences)
19. Assoc. Prof. Isma’il Aliyu Danmaraya, NWU Kano (Economics)
20. Assoc. Prof. Sani D. Iya, NWU Kano (Material Physics)
Kididdiga da akai, ta nuna cewa mutane sama da dubu 3 ne s**a ci gajiyar ilimi kyauta. Wayannan masana a fannoni daban daban sun bazu a jihohin Arewa guda 17 da na Kudu guda 4. A yayin da kaso kasa da 10% ne suke kasashen ketare guda 20 suna cigaba da samin kwarewar aiki don gina rayuwar al’umma. Wannan tsarin tallafin karatu ya zama daya daga cikin abubuwan da suke rage radadin talauci a arewacin Nigeria idan Mukai laákari da kididdigar da bankin duniya (World Bank) da kuma maáikatar kidid diga ta Nigeria (NBS) ta fitar daga shekara 2011 zuwa 2022. Cewa, ragin talaucin a arewacin Nigeria ya sauka daga kaso 87% zuwa kaso 65%.
A matsayina na wanda nasami gajiyar tallafin sama da sau 3, wanda ya hada da karatun digiri na 3 a kasar Malaysia; Ina nuna godiya da shugabanci na kwarai. Tabbas wannan tallafin ilmi ya canja rayuwar alúmma kuma ya kafa tushen nasarori a tarihin kasa baki daya.
Idan muka ajiye siyasa a gefe, zamu iya cewa Dr. RMK ya zama Baban ilmi a Nigeria.
*Zahraddeen Sufyanu (Triple Scholar)*
Giginyu Ward, Nassarawa LGA.
27/12/25