20/08/2026
Tarihin Mazabar Gobirawa ba zata taɓa mantawa da Hon. Lawan Hussaini ba, saboda irin namijin ƙoƙarin da ya yi wajen gudanar da ayyukan alheri da ci gaban al’umma a mazabar.
Ga wasu daga cikin ayyukan da ya gudanar:
1. Gina makarantar Islamiyya a Kurna, Layin Dorawar Tsohon Soja.
2. Gina asibiti a kan titin Farin Bene, Gidan Dagaci.
3. Gina asibiti a Durumi, Umma Zaria Hall.
4. Aikin drainage a Kurna Masallaci, Layin Ɗan Agege.
5. Gina ɗakin duba marasa lafiya a ɗan asibitin da ke Tudun Bojuwa.
Waɗannan ayyuka shaida ne kan yadda Hon. Lawan Hussaini ke mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’umma da kawo ci gaba a mazabar.
Al’ummar wannan yanki na matuƙar godiya da wannan namijin ƙoƙari. Allah Ya saka masa da alheri, Ya ƙara masa ƙarfin gwiwa wajen yi wa al’umma hidima.
Gobirawa ba za ta manta da kai ba!
~Sufee