Anti illicit drugs/ phone snatching force

Anti illicit drugs/ phone snatching force welcome to official page Anti illicit drugs/phone snatching force Kano state command Stay alert | Stay safe Fighting drug abuse & phone snatching.

18/08/2026
18/08/2026

Gaskiya wannan

KOSSAP Ta Gudanar da Muhimmin Taron Wayar da Kan Jami’antaAn gudanar da wani muhimmin taron wayar da kan jami’an runduna...
16/08/2026

KOSSAP Ta Gudanar da Muhimmin Taron Wayar da Kan Jami’anta

An gudanar da wani muhimmin taron wayar da kan jami’an rundunar Kano State Anti-Illicit Drugs/Phone Snatching Force (KOSSAP), domin ƙarfafa gwiwar jami’ai tare da samar da dabarun inganta kyakkyawar mu’amala, aiki tare da kuma sauran hanyoyin da za su taimaka wajen ci gaban rundunar.

Kwamandan rundunar Nura Salisu Sharada, ne ya jagoranci taron, inda ya jaddada muhimmancin ƙwarewa, biyayya, kyakkyawar mu’amala da kuma haɗin kai tsakanin jami’an rundunar domin samun nasarar ayyukan da aka damƙa musu.

Daga cikin manyan jami’an da s**a halarci taron akwai Sakataren Rundunar, DC Alhaji Bala Tofa; DC Parade Commander kuma Director Interlegence with Appointment, Bello Muhammad Karaye; DC Abduljalal Said Muhammad Director Operations, PPRO Ibrahim Garba Ahmad; DSK S.O Kabiru Musa Jalo; DSK OC Media, Idris Idris Jibril; da 2IC OC Media, ASP Abdulhalim Sulaiman Ibrahim, da 2IC OC S O Aliyu dan azumi tare da sauran jami’ai da membobin rundunar.

Taron ya kuma mayar da hankali kan ƙarfafa fahimtar juna, bin tsarin aiki, kyautata hulɗa da al’umma da kuma samar da sabbin dabarun da za su taimaka wajen inganta ayyukan rundunar

A nasa jawabin, Commander Nura Salisu Sharada ya ƙarfafa jami’an da su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, ladabi da kishin rundunar, domin cimma manufofin da aka kafa a kansu.

An bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki na ƙara inganta ƙwarewar jami’ai da kuma ƙarfafa haɗin kan rundunar wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi, satar wayoyi da sauran ayyukan da ke barazana ga tsaron al’umma.

16/08/2026

Sakkowar commander nura salisu sharada na Anti-Phone Snatching Force.

A irin wannan rana a shekarar 2025 rundunar Anti-Phone Snatching ta k**a buhuhunan wiwi. A ranar 14/08/ 2025 rana mai ir...
14/08/2026

A irin wannan rana a shekarar 2025 rundunar Anti-Phone Snatching ta k**a buhuhunan wiwi.

A ranar 14/08/ 2025 rana mai irin tayau rundunar Anti-Phone Snatching Force Kano ta samu nasarar cafke wata babbar mota dauke da tabar wiwi karkashin jagorancin margayi inuwa salisu sharada na rundunar.

Kuma aka mikata ga hukumar NDLEA ta kasa reshen Jihar Kano.

Haka zalika commander dake rike da rundunar ayanzu nura salisu sharada yaci gaba da kara shirya dabarun iri-iri ga jami'an rundunar domin yaki da shanmiya gun kwawowi fadan daba kwacan waya ajihar .

Address

Kano Nigeria Sharada Ado Bayaro House
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Anti illicit drugs/ phone snatching force posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share