07/09/2026
A yammacin yau, Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alh. Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da shirin tallafa wa mata 5,200 da jarin naira dubu hamsin (₦50,000) kowacce, domin bunkasa sana’o’insu da inganta rayuwarsu.
Wannan shiri wani bangare ne na jajircewar gwamnatin Mai Girma Gwamna wajen karfafawa mata gwiwa, samar musu da hanyoyin dogaro da kai tare da bunkasa tattalin arzikin iyalai a fadin Jihar Kano.
ABBA GIDA GIDA Machineries