11/02/2026
📢 : Gagarumin Shirin Ayyukan Raya Kasa a Karamar Hukumar Tarauni.
Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya amince da aiwatar da gagaruman ayyukan raya kasa guda talatin da shida (36) a fadin Karamar Hukumar Tarauni, karkashin jagorancin majalisar karamar hukumar.
Wadannan ayyuka sun tabo bangarorin Ilimi, Lafiya, Ruwan sha, da kuma Gyaran magudanan ruwa (Drainages) domin kyautata rayuwar al'umma.
🏗️ Muhimman Ayyukan da Za a Gudanar:
Bangaren Ilimi:
Samar da kayan daki (Furniture) ga malaman makarantun firamare na Tarauni.
Gyaran dakunan karatu (Classrooms) a makarantun: Hausawa Model, Daurawa Primary, Rabiatu Primary (Kauyen Alu), da Gyadi-Gyadi Secondary.
Gina sabbin azuzuwa da dakin gwaje-gwaje (Laboratory) a GSS Darmanawa da Gyadi-Gyadi.
Samar da kujerun dalibai a makarantar GSSS Darmanawa.
Bangaren Ruwa da Lantarki:
Mayar da famfunan tuka-tuka guda 6 zuwa masu amfani da hasken rana (Solar).
Mayar da manyan rijiyoyin burtsatse (Boreholes) guda 8 zuwa masu amfani da Solar.
Gyaran babban Tiransifoma (Transformer) a Unguwa Uku.
Sanya na’urar hasken rana (Solar System) a masallacin Juma’a na Unguwar Gano.
Bangaren Magudanan Ruwa (Drainages):
Gina manyan
magudanan ruwa a:
Layin Shehu Zaranda, Karkasara, Gidan Ado Mako, Tasha, Gyadi-Gyadi Arewa, Yan-kifi, Yan-Awaki, da Zaria Road.
Sauran Ayyuka:
Gyaran babban dakin taro (Hall) na makarantar Sabilul Rashad Islamiyya.
Gyara da fadada masallacin Layin Yan-Awaki.
🙏 Godiya ta Musamman:
Muna mika godiyarmu ga Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan abun arziki da ya yi wa jama'ar Tarauni. Haka kuma muna godiya ga Hon. Ahmed Sekure, Shugaban Karamar Hukumar Tarauni, bisa jajircewarsa.
Sa Hannu:
✍️ Engr. Aminu Malami (Mai Gari)
Sakataren Karamar Hukumar Tarauni