APC Social Media Organisation Katsina State

APC Social Media Organisation Katsina State All Progress Congresses

An Ƙaddamar da Gasar Cin Kofin Dikko Falle Biyu Unity Cup a Ingawa, Wanda Mustapha Ingawa Ya Ɗauki NauyiA ranar Asabar 1...
16/08/2026

An Ƙaddamar da Gasar Cin Kofin Dikko Falle Biyu Unity Cup a Ingawa, Wanda Mustapha Ingawa Ya Ɗauki Nauyi

A ranar Asabar 15 ga watan Augustan 2026, aka ƙaddamar da gasar ƙwallon ƙafa ta Dikko Falle Biyu Unity Cup tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Ƙaramar Hukumar Ingawa, wadda Babban Mai Taimaka wa Gwamnan Jihar Katsina kan Kafafen Sadarwa na Zamani, Hon. Mustapha Sama’ila Ingawa, ya ɗauki nauyin gudanarwa.

Kwamishinan Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Jihar Katsina, Injiniya Surajo Yazid Abukur, ne ya ƙaddamar da fara gasar a garin Ingawa.

Wasan farko na gasar ya fafata tsakanin FC New Generation Ingawa da New Academy Yandoma, inda aka tashi kunnen doki 1–1.

A yayin bikin ƙaddamar da gasar, Kwamishina Surajo Yazid Abukur da Hon. Mustapha Sama’ila Ingawa sun bayyana muhimmancin wasanni wajen haɗa kan matasa, bunƙasa hazaka da samar da damammaki ga matasa.

Sun kuma jinjina wa irin ƙoƙarin da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ke yi wajen bunƙasa harkokin wasanni da samar da damammaki ga matasa a faɗin jihar.

ZAGAYEN GODIYA A INGAWA Tare Da Hon Mustapha Samaila Ingawa A jiya Asabar, cikin ikon Allah da kaddarawarSa, mun samu na...
16/08/2026

ZAGAYEN GODIYA A INGAWA Tare Da Hon Mustapha Samaila Ingawa

A jiya Asabar, cikin ikon Allah da kaddarawarSa, mun samu nasarar gudanar da zagayen rangadi a mazabu biyar daga cikin mazabu goma sha ɗaya da ke Ƙaramar Hukumar Ingawa, domin gaisawa da Iyayen Ƙasa, Dagattai, Masu Unguwanni da Limamai, ƙarƙashin jagorancin ɗan takarar Majalisar Jiha na Jam’iyyar APC, Hon. Akilu Muhammed Yandoma.

Mun samu rakiyar shugabannin Jam’iyyar APC, tare da Kansilolin mazabun da muka ziyarta. Mazabun sun haɗa da Kurfeji/Yankaura Ward, Agayawa Ward, Dugul Ward, Dara Ward, da Daunaka/Bakin Kwari Ward.

A yayin wannan ziyara, mun samu gagarumar tarba daga Iyayen Ƙasa, dattawa, matasa da mata. An gudanar da ziyarorin ne a fadar Dagattai biyar na mazabun, inda s**a bayyana matuƙar farin cikinsu da jin daɗinsu bisa wannan ziyara.

Haka kuma, Dagattai da Iyayen Ƙasa sun miƙa saƙon cikakkiyar godiyarsu ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, bisa ayyukan alheri da ci gaba da gwamnatinsa ke gudanarwa a mazabunsu.

Sun bayyana shirin Community Development Program (CDP) a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen da s**a fi tasiri wajen sauya rayuwar al’ummar da ke ƙarƙashin gundumominsu. Sun bayyana cewa shirin ya kawo ayyuka da s**a haɗa da gina sabbin rijiyoyin burtsatse da fanfunan ruwa, gyaran tsofaffin fanfunan ruwa, gyaran makarantu, gina kwalbatoci, gyaran masallatai, Islamiyyoyi da sauran ƙananan ayyukan raya al’umma da s**a dace da buƙatun jama’a.

Sun kuma yaba da yadda shirin CDP ke bai wa al’umma damar bayyana muhimman buƙatunsu tare da ganin an aiwatar da su cikin ingantaccen tsari.

A ƙarshe, mun gode wa Iyayen Ƙasa, Dagattai, shugabannin Jam’iyya, Kansiloli, matasa, mata da daukacin al’ummar mazabun da muka ziyarta bisa kyakkyawar tarba, goyon baya da addu’o’in da s**a yi mana.

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya yi alƙawarin gwamnatin sa zata bada cikakken goyon baya wajen kafa asibi...
15/08/2026

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya yi alƙawarin gwamnatin sa zata bada cikakken goyon baya wajen kafa asibitin kula da jarirai domin karfafa kiwon lafiya yara ƙanana da kuma rage mutuwar su

Gwamnan ya bada wannan tabbacin ne a ranar laraba a lokacin da ya karɓi bakuncin shugabar gudanarwa ta asibitin kula da ƙananan Yara, Dakta Efunbo Dosekun da tawagar ta a gidan gwamnatin jihar Katsina

Haka kuma Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana wannan yunkuri a matsayin wanda ya zo akan lokaci da ake buƙata bunƙasa kiwon lafiya ƙananan yara sabuwar haihuwa a faɗin jihar Katsina.

"Wannan tunani abin a yaba ne, zai taimaka wajen samar da kyakkyawar sakamako na rage mutuwar ƙananan yara a fadin jihar Katsina' inji Raɗɗa

A cewar gwamna, zuwa yanzu gwamnatin sa ta zuba jari na naira biliyan 3 domin samar da abinci mai gina jiki bayan bullar rahoton da ke cewa jihar Katsina na sahun gaba akan matsalar karancin abinci mai gina jiki (Tamowa)

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin sa ta kafa wani kwamiti akan matsalar abinci mai gina jiki inda aka ƙara yawan cibiyoyin kula da masu lalurar wanda hakan ya bada gagarumin cigaba akan wannan yaƙi da cutar tamowa

Da take jawabi shugaban gudanarwa ta asibitin kula da ƙananan yara Dakta Dosekun ta bayyana cewa an samar da ayyukan kula da jarirai sabuwar haihuwa a jihar Katsina

Haka kuma ta yaba ƙoƙarin gwamnan na zuba jari a akan kula da jarirai sabuwar haihuwa, inda ta ce gwamnatin ta faɗaɗa gine-gine da samar da kayan aiki a asibitoci kula da lafiya matakin farko.

Kazalika Dakta Dosekun ya bayyana cewa shirin samar da kiwon lafiya ya zo wani sabon tsarin kula da jarirai sabbin haihuwa, wanda zai inganta samun kulawar gaggawa cikin lokaci ga jariran da ke fama da rashin lafiya da kuma waɗanda aka haifa kafin lokacin haihuwa, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin matakan kiwon lafiya daban-daban.

A cewar ta, tsarin zai mayar da hankali wajen ƙara yawan cibiyoyin kula da jarirai cikin gaggawa, kafa ingantacciyar hanyar haɗa ma’aikatan lafiya da cibiyoyin kiwon lafiya, inganta tsarin kula da rabon kayan aiki da kuma ƙarfafa tsarin tura marasa lafiya daga wata cibiyar lafiya zuwa wata a faɗin jihar Katsina

Labari ciki Hotunan Yadda gwamnatin Jihar Katsina ƙarkashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa Phd ta samar da Ingantacce...
14/08/2026

Labari ciki Hotunan

Yadda gwamnatin Jihar Katsina ƙarkashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa Phd ta samar da Ingantaccen ruwan sha a fadi jihar Katsina.

APC Social Media Organisation Katsina State

Gwamna Radda Ya Halarci Rufe Gangamin Yaƙin Neman Zaɓen Oyebamiji, Ɗan takara Gwamnan Jihar Osun A Jam'iyyar APC  Gwamna...
14/08/2026

Gwamna Radda Ya Halarci Rufe Gangamin Yaƙin Neman Zaɓen Oyebamiji, Ɗan takara Gwamnan Jihar Osun A Jam'iyyar APC

Gwamnan Jihar Katsina, kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa maso yamma, Malam Dikko Umar Radda, ya bayyana goyon bayan shi ga ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan Jihar Osun, Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji.

Gwamna Radda ya halarci babban gangamin jam'iyyar APC da aka gudanar a Osogbo, tare da takwarorinsa na Kano da Jigawa, Injiniya Abba Kabir Yusuf da Alhaji Umar Namadi, da sauran gwamnonin jam’iyyar.

13/08/2026

Idan ni ke samun kudin shigar da jihar Legas ke samu a kowane wata to da sai mun rasa aikin da za'ayi an fara raba ma mutane kudi a jihar Katsina, sabo da sai munyi wata tara kafin mu samu abun da suke samu a wata daya - Gwamna Radda

Labari ciki Hotunan Na yadda aikin fadada titin hanyar Kofar Kaura zuwa Green House inda tuni har an fara zuba kwalta wa...
13/08/2026

Labari ciki Hotunan

Na yadda aikin fadada titin hanyar Kofar Kaura zuwa Green House inda tuni har an fara zuba kwalta wadda gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda PhD,CON, take gudanarwa domin inganta zirga-zirga.

Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ta gudanar da taront...
12/08/2026

Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ta gudanar da taronta na 13 a yau, Laraba 12 ga Agusta 2026, inda ta amince da wasu muhimman tsare-tsare da ayyuka, ciki har da:

1. Majalisar ta amince da rahoton kwamitin da aka kafa domin daidaita harkokin makarantun Alqur’ani da Tsangaya, tare da samar da tsarin ba wa daliban da s**a kammala karatu takardun shaida da za su taimaka musu wajen ci gaba da karatu da samun sana’o’i.

2. An amince da biyan diyya ga mutanen da gine-ginensu ko kadarorinsu s**a shafa sakamakon aikin hanyar Albaba zuwa Unguwar Alkali dake cikin birnin Katsina, domin tabbatar da gudanar da aikin cikin sauki.

3. Katsina United FC: Majalisar ta amince da sake fasalin tafiyar da ƙungiyar wasa ta Katsina United domin kara kwarewa da inganta harkar kwallon kafa. Hakan ya hada da samar da sabuwar motar CNG, jigilar tawaga ta jirgin sama a wasannin nesa da kuma inganta tsarin gudanarwar ƙungiyar.

4. An amince da shirin hukumar KASEDA na “Catch Them Young” don koyar da harkokin kasuwanci da sana’o’i a makarantun sakandare na gwamnati, tare da horas da malamai domin su koyar da dalibai dabarun dogaro da kai, kirkire-kirkire da samar da hanyoyin magance matsalolin al’umma.

5. Majalisar ta amince da shirin Katsina-One-Person-One-Tree (KT1T) na dasa bishiyoyi a fadin kananan hukumomi 34. Matakin farko zai kunshi dasa da kula da bishiyoyi miliyan biyu a shekarar 2026 a wurare 6,652, yayin da babban shirin shi ne dasa bishiyoyi akalla miliyan 11 tsakanin 2026 zuwa 2030, tare da samar da inganta tattalin arziki ga wadanda za su amfana.

6. An amince da bayar da kwangilolin ayyukan dakile zaizayar kasa da ambaliyar ruwa a wurare 17 da ke fadin jihar.

7. Majalisar ta amince da kafa tsarin bada scholarshi ga ɗalibai mafi hazaƙa (Subject-Based Merit Scholarship), da farfado da Asusun Tallafin Karatu na Jihar Katsina. Haka kuma, an amince da daftarin dokar Katsina State Scholarship and Loans Board Bill, 2026, da kuma tsarin kafa gidauniyar ilimi (Education Endowment Trust Fund), tare da kafa kwamitin aiwatarwa. An kuma amince da kafa Sports Scholarship Programme domin tallafa wa matasa masu hazaka a fannin wasanni.

Matakan sun nuna kudirin gwamnatin Malam Dikko Radda na kara inganta ilimi, wasanni, muhalli, ababen more rayuwa da bunkasar tattalin arzikin matasa a Jihar Katsina.

Mustapha Samaila Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

August 12, 2026.

Address

Kofar Kaura Layout Katsina
Katsina

Telephone

+2349039416720

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when APC Social Media Organisation Katsina State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to APC Social Media Organisation Katsina State:

Shortcuts

Share