Team Eng. Muttaƙa Rabe Darma

Team Eng. Muttaƙa Rabe Darma A platform dedicated to supporting the vision, leadership, and community service of Engr.

Muttaƙa Rabe Dama towards a better and more prosperous Katsina and Nigeria in general.

A cikin kwanaki 100 kacal, Ministan Gidaje da raya Birane na Najeriya Engr. Muttaqha Rabe Darma ya taka muhimmiyar rawa ...
16/08/2026

A cikin kwanaki 100 kacal, Ministan Gidaje da raya Birane na Najeriya Engr. Muttaqha Rabe Darma ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa rayuwar al'ummar Jihar Katsina da ma kasa baki daya musamman Matasa.

Gwamnatin Tarayya da Kamfanin China Hyway Sun Tattauna Shirin Gina Gidaje 10,000 a NajeriyaMinistan Gidaje da Raya Biran...
14/07/2026

Gwamnatin Tarayya da Kamfanin China Hyway Sun Tattauna Shirin Gina Gidaje 10,000 a Najeriya

Ministan Gidaje da Raya Birane na Tarayya, Engr. Muttaqa Rabe Darma, ya gana da tawagar Kamfanin China Hyway Group Limited domin tattauna wani shiri na gina gidaje 10,000 a Najeriya.

A yayin ganawar, kamfanin na ƙasar Sin ya gabatar da kudirinsa na samar da waɗannan gidaje domin samar da gidajen a wani mataki da ake sa ran zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin gidaje da kuma samar da ingantattun wuraren zama ga al'umma.

Shirin na daga cikin ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da masu zuba jari na ƙasashen waje wajen bunƙasa harkar gidaje da samar da matsuguni ga 'yan Najeriya.

Labarin HotunaMinistan Gidaje da Raya Birane na Tarayya, Injiniya Muttagha Rabe Darma, PhD, ya karɓi baƙuncin tawagar UN...
29/06/2026

Labarin Hotuna

Ministan Gidaje da Raya Birane na Tarayya, Injiniya Muttagha Rabe Darma, PhD, ya karɓi baƙuncin tawagar UN-Habitat ƙarƙashin jagorancin Mista Oumar Sylla, Daraktan Ofishin Yankin Afirka, a yayin wata ziyarar girmamawa da s**a kai ma’aikatar a ranar Litinin, 29 ga Yunin 2026.

Ministan Gidaje Ya Duba Sabon Tsarin Gudanar da Bayanai Kan Filaye Kafin KaddamarwaMinistan Gidaje da Raya Birane na Tar...
18/06/2026

Ministan Gidaje Ya Duba Sabon Tsarin Gudanar da Bayanai Kan Filaye Kafin Kaddamarwa

Ministan Gidaje da Raya Birane na Tarayya, Injiniya Muttagha Rabe Darma, ya kai ziyarar duba aikin Centralised Land Repository and Management System (CLRMS) gabanin kaddamar da shi a hukumance.

Sabon tsarin na zamani an ƙirƙire shi ne domin inganta harkokin gudanar da filaye ta hanyar hanzarta bayar da takardun mallakar fili (Certificate of Occupancy - C of O), da ƙarfafa adana bayanai cikin tsari, da kuma inganta gaskiya da samun kuɗaɗen shiga ga gwamnati.

Ministan ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen fasahar zamani domin rage jinkiri, ƙara inganci a ayyuka, da samar wa al'umma ayyuka masu sauri da sauƙi a ɓangaren gidaje.

Engr  Dr.Muttaqha-Rabe Darma ministan gidaje da Raya birane ya kaddamar da Programs guda biyar da zasu taimaki al'ummar ...
09/06/2026

Engr Dr.Muttaqha-Rabe Darma ministan gidaje da Raya birane ya kaddamar da Programs guda biyar da zasu taimaki al'ummar jahar Katsina

1. Zai bada horo da tallafin kuɗi ga ƙananan ƴan kasuwa na jahar Katsina. Domin cikawa sai ashiga: https://mrdonline.ng/grants/69febbfb8b812e762756bd02

2. Zai ɗauki Malaman makaranta domin koyawa a makarantu. Domin cikewa ashiga: https://mrdonline.ng/careers/6a0a4ca3e6112610437fb3c7

3. Zai ɗauki likitoci domin duba mararsa life (Online Clinic). Domin cikawa ashiga: https://clinic.mrdonline.ng/register/practitioner

4. Makaranta da zata ringa koyarwa online: https://school.mrdonline.ng/

5. Asibiti likitoci zasu duba mararsa lafiya online: https://clinic.mrdonline.ng/

Yana da kyau mu yaɗa wannan domin mutanen mu su cika musamman MRD Mini and Macro Business Grant da kuma MRD Volunteer Teaching Programme.
Wannan damace ga mutanen jihar Katsina baki ɗaya.

Minista Darma Ya Tallafawa Dalibai 33 Kudin Rubuta Jarabawar NECO a KatsinaMinistan Gidaje da Raya Birane na Tarayya, In...
18/05/2026

Minista Darma Ya Tallafawa Dalibai 33 Kudin Rubuta Jarabawar NECO a Katsina

Ministan Gidaje da Raya Birane na Tarayya, Injiniya Muttaqha Rabe Darma, ya bayar da tallafin sama da Naira Miliyan ɗaya (1,072,000) domin biya wa dalibai 33 kudin rubuta jarabawar NECO a jihar Katsina.

An mika tallafin ne ta hannun mataimakin Ministan na musamman, Alhaji Gambo Garba, yayin wata ziyara da tawagarsa ta kai makarantar mata ta WTC da ke Katsina domin ganawa da shugabar makarantar, Hajiya Hadiza Nasir.

A cewar Gambo Garba, Ministan ya amince da bayar da tallafin ne bayan samun roko daga makarantar dangane da halin da wasu daga cikin daliban ke ciki, musamman marasa galihu da marayu da ke fuskantar barazanar rasa damar ci gaba da karatu.

Ya bayyana cewa Injiniya Darma na daga cikin masu bai wa harkar ilimi muhimmanci, yana mai ganin cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban al’umma da makomar matasa.

Da take jawabi bayan karbar tallafin, shugabar makarantar ta nuna godiyarta ga Ministan, tana mai cewa duk da ta nemi taimako daga mutane da dama, Injiniya Muttaqha Rabe Darma ne kadai ya amsa koken daliban tare da daukar nauyin kudin jarabawar nasu.

Address

Katsina
820001

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Team Eng. Muttaƙa Rabe Darma posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share