19/07/2026
Jagoranmu, Hon. Dr. Musa Lawal Jibia, PhD, FNIM, Adon Garin Katsina, ɗan takarar Majalisar Tarayya a Jam'iyyar ADC, tare da mai girma ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina na Jam'iyyar ADC, Distinguished SEN. Ahmad Babba Kaita sun halarci jana'izar marigayi Magaji Sauri, mahaifin Alhaji Ali Isa Girka, a garin Girka da ke Ƙaramar Hukumar Kaita.
Haka kuma Mahaifi ga Hon. Shamsu Abdallawa, ɗan takarar Majalisar Jiha na Ƙaramar Hukumar Kaita a Jam'iyyar ADC, ya kasance cikin tawagar.
A yayin ta'aziyyar, Hon. Dr. Musa Lawal Jibia ya bayyana cewa rasuwar Marigayi Magaji Sauri ba rashi ba ne ga al'ummar Girka ko Ƙaramar Hukumar Kaita kaɗai, illa rashi ne da ya shafi ɗaukacin al'ummar Jihar Katsina har ma da ƙasar Hausa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa, kasancewar marigayin mai riƙe da sarauta ne a masarautarmu ta gargajiya, ya bar kyakkyawan tarihi na shugabanci da gudanar da mulki cikin adalci, abin da al'umma da dama s**a shaida.
Muna addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya yalwata masa rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, Ya kuma bai wa iyalansa da ɗaukacin al'umma haƙurin jure wannan babban rashi. Ameen.