22/05/2026
Kungiyar Lamido Dikko Youths and Women Agenda for Tinubu/Dikko 2027 ta kai wata gagarumar ziyara ta musamman ga mai girma Hon. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri a gidansa da ke cikin garin Katsina, inda s**a bayyana manufar ziyarar tasu wadda ta ta’allaka kan ƙara ƙarfafa goyon baya ga jam’iyyar All Progressives Congress daga sama har ƙasa domin tabbatar da nasarar tafiyar Tinubu/Dikko 2027.
A yayin ganawar, shugabannin ƙungiyar sun jaddada cikakken goyon bayansu ga manufofin jam’iyyar APC tare da bayyana aniyarsu ta haɗa kan matasa da mata domin cigaban siyasa mai ɗorewa da kuma tabbatar da nasarar jam’iyya a zaɓuka masu zuwa.
Da yake jawabi, mai girma Hon. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri ya yaba da jajircewa da kishin jam’iyya da mambobin ƙungiyar ke nunawa, tare da basu shawarwari masu muhimmanci kan yadda za su tafiyar da harkokinsu cikin tsari, haɗin kai, biyayya da kuma mutunta juna domin cimma burin da s**a sanya a gaba.
Hakazalika, ya ƙarfafa musu guiwa kan muhimmancin juriya, riƙon amana da sadaukarwa wajen gudanar da dukkan ayyukan ƙungiyar, yana mai bayyana cewa nasara tana samuwa ne ta hanyar haƙuri, tsari da haɗin kai tsakanin shugabanni da mabiyansu.
Ziyarar ta gudana cikin yanayi na farin ciki, fahimtar juna da kuma nuna cikakken goyon baya ga tafiyar APC da manufofin cigaban al’umma.
✍️✍️
SAYYERDEE PRESDOR
FND TO LAMIDO FOUNDATION MOBILIZATION FOR TINUBU DIKKO RADDA