01/06/2026
KCF Ta Karrama Ministan Gidaje Da Raya Birane Engr. Muttaqa Rabe Darma Da Lambar Yabo A Katsina
Kungiyar tuntuɓa ta dattawan jihar Katsina Consultative Forum (KCF) ta karrama ministan gidaje da raye birane Injiniya Muttaƙa Rabe Darma.
Ƙarramawar ta biyo bayan irin gudunmawar da kungiyar ta ce ta lura sabon ministan ya bayar wajen cigaban jihar Katsina
Taron karrama injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya gudana a ɗakin taro na Masaukin Baki na Hellside a lokacin lafiyar cin abinci da aka shiryawa Jakadun Nijeriya guda biyu 'yan asalin jihar Katsina inda 'yan uwa da abokan arziki s**a shaida ƙarramawar.
Kazalika injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya bayyana wannan karramawa a matsayin karfafa gwiwa musamman a ayyukan da s**a shafi al'umma kai tsaye.
Sannan ministan ya yi kira ga al'ummar jihar Katsina da su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya wajen cigaban da gina jihar Katsina da kasa baki ɗaya.