05/05/2026
Daga Adamu Media.
A yau, Najeriya na tunawa da cikar shekaru 16 da rasuwar tsohon Shugaban Kasa, , wanda ya rasu a ranar 5 ga Mayu, 2010 bayan fama da jinya.
Marigayi Yar’Adua, wanda aka haifa a ranar 16 ga Agusta, 1951 a , ya kasance daya daga cikin shugabannin Najeriya da s**a yi fice wajen nuna gaskiya, rikon amana da kuma jajircewa wajen tabbatar da adalci a mulki.
Kafin hawansa kujerar shugabancin kasa a shekarar 2007, Yar’Adua ya rike mukamin gwamnan Jihar Katsina daga 1999 zuwa 2007, inda ya gudanar da mulki cikin tsari da bin doka, abin da ya sa aka dauke shi a matsayin daya daga cikin gwamnoni mafi nagarta a lokacin.
A matsayinsa na Shugaban Kasa, Alh. Umaru Musa Yar'adua ya yi kokari wajen inganta dimokuradiyya tare da daukar matakai na yaki da cin hanci da rashawa. Daya daga cikin abubuwan da s**a ja hankalin al’umma shi ne yadda ya fito fili ya amince cewa zaben da ya kawo shi mulki na da kura-kurai, matakin da ya nuna gaskiyarsa da kaskantar da kai.
Haka kuma, gwamnatinsa ta mayar da hankali kan samar da zaman lafiya a yankin Niger Delta ta hanyar shirye-shiryen sulhu, wanda ya taimaka wajen rage tashe-tashen hankula a yankin.
Rasuwarsa ta jefa Najeriya cikin jimami, inda aka bayyana shi a matsayin shugaba mai kishin kasa da mutunta jama’a. Duk da gajeren lokacin da ya yi a mulki, gudummawar da ya bayar na ci gaba da zama abin koyi ga shugabanni na yanzu da masu tasowa.
Yayin da ake cika shekaru 16 da rasuwarsa, al’umma da dama na ci gaba da tuna shi a matsayin shugaba mai gaskiya, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa kasa.
Allah ya jikan, ya ba shi Aljannatul Firdausi.