Katsina State Community Development Programme

Katsina State Community Development Programme Office of the State Coordinator, Katsina State Community Development Programme (KSCDP).

INNA LILLĀHI WA INNĀ ILAYHI RĀJIʿŪNIt is with deep sorrow and submission to the will of Allah (SWT) that we announce the...
18/08/2026

INNA LILLĀHI WA INNĀ ILAYHI RĀJIʿŪN

It is with deep sorrow and submission to the will of Allah (SWT) that we announce the passing of Hajiya Sa’adatu, the beloved stepmother of Assoc. Professor Kamaluddeen Kabir Katsina , State Coordinator, Katsina State Community Development Programme (CDP).

The funeral prayer (Janazah) will take place today at 11:00 a.m. at the family residence in Shaiskawa, Katsina.

May Allah (SWT) forgive her shortcomings, shower her with His infinite mercy, grant her Al-Jannatul Firdaus, and give the family the strength, patience, and fortitude to bear this great loss.

May Allah (SWT) grant her Al-Jannatul Firdaus,
AMEEN YA HAYYU YA ƘHAIYUM.

17/08/2026

SANARWA 🎤

Katsina State Community Development Programme, ƙarƙashin jagorancin Associate Professor Kamaluddeen Kabir Katsina, na gayyatar al’umma zuwa wajen ƙaddamar da rabon hatsi, wanda Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Mal. Dr. Dikko Umaru Radda, PhD, CON, zai ƙaddamar.

📅 Rana: Laraba, 19 ga Agusta, 2026
📍 Wuri: Kaita
⏰ Lokaci: 10:00 na safe

Ana maraba da kowa.

17/08/2026

ZIYARAR GANI DA IDO A GUNDUMAR SHEMA DUTSIN-MA (PART 4)

Mun ziyarci garin Ƙwimi, ƙarƙashin Shema Ward, domin ganin gyaran fanfon tuƙa-tuƙa da aka yi masu, tare da jin ta bakin al’ummar da ke garin game da gyaran da aka yi masu.

Wanda Community Level Committee (CLC) na Gundumar Shema s**a gudanar a cikin kuɗin da aka ware masu domin aiwatar da ƙananan ayyuka da gyare-gyare ƙarƙashin hukumar CDP, wadda Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir Katsina ke jagoranta.

16/08/2026

ZIYARAR GANI DA IDO A GUNDUMAR KUTAWA DUTSIN-MA (PART 2)

Mun ziyarci cikin garin Yar Ruma, ƙarƙashin Kutawa Ward, domin ganin gyaran fanfon tuƙa-tuƙa da aka yi masu, tare da jin ta bakin wani matashi dake zaune a garin dangane da gyaran da aka yi masu.

Wanda Community Level Committee (CLC) na Gundumar Kutawa s**a gudanar a cikin kuɗin da aka ware masu domin aiwatar da ƙananan ayyuka da gyare-gyare ƙarƙashin hukumar CDP, wadda Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir ke jagoranta.

15/08/2026

ZIYARAR GANI DA IDO A GUNDUMAR KUTAWA DUTSIN-MA

Mun ziyarci Asibitin Yar Ruma, ƙarƙashin Kutawa Ward, domin ganin gyaran da aka yi masu, tare da jin ta bakin shugaban asibitin dangane da gyaran da aka yi masu.

Wanda Community Level Committee (CLC) na Gundumar Kutawa s**a gudanar a cikin kuɗin da aka ware masu domin aiwatar da ƙananan ayyuka da gyare-gyare ƙarƙashin hukumar CDP, wadda Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir ke jagoranta.

13/08/2026

GANI 👀 YA KORI JI👂

Mun ziyarci Asibitin Dabawa, ƙarƙashin Dabawa Ward, domin ganin gyaran makewayi guda biyu da aka yi masu, tare da jin ta bakin shugabar asibitin game da gyaran da aka yi masu.

Wanda Community Level Committee (CLC) na Gundumar Dabawa s**a gudanar a cikin kuɗin da aka ware masu domin aiwatar da ƙananan ayyuka da gyare-gyare ƙarƙashin hukumar CDP, wadda mai girma gwamna Malam Dr. Dikko Umaru Radda PhD, CON ya ƙirƙira kuma Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir Katsina ke jagoranta.

12/08/2026

ZIYARAR GANI DA IDO A GUNDUMAR SHEMA DUTSIN-MA (PART 3)

Mun ziyarci unguwar garin Gizawa, ƙarƙashin Shema Ward, domin ganin gyaran fanfon tuƙa-tuƙa da aka yi masu, tare da jin ta bakin al’ummar da ke garin game da gyaran da aka yi masu.

Wanda Community Level Committee (CLC) na Gundumar Shema s**a gudanar a cikin kuɗin da aka ware masu domin aiwatar da ƙananan ayyuka da gyare-gyare ƙarƙashin hukumar CDP, wadda Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir Katsina ke jagoranta.

ZIYARAR WAKILAN CDP NA GUNDUMOMI 361 Mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda , Ph.D, CON, ya karɓi ...
11/08/2026

ZIYARAR WAKILAN CDP NA GUNDUMOMI 361

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda , Ph.D, CON, ya karɓi baƙuncin Wakilan Shirin Ci gaban Al’umma (CDP) na wards 361 a gidan Gwamnatin Jihar Katsina, yayin ziyarar godiya da s**a kai masa.

Mai girma Gwamna ya buƙace su da su cigaba da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, adalci, amana da haɗin kai, tare da tabbatar da dorewar ayyukan CDP da kula da ƙananan gyare-gyare a gundumomin su.

Shugaban CDP na Jihar Katsina, Associate. Prof. Kamaladdeen Kamaluddeen Kabir Katsina , ya gode wa Mai girma Gwamna bisa goyon baya, tare da tabbatar da cewa shugabannin za su ci gaba da aiki cikin gaskiya da ƙwazo domin ƙarfafa alaƙar gwamnati da al’umma.

Shugabannin sun kuma yaba wa Mai girma Gwamna, akan irin waɗannan ayyukan raya al’umma, tare da yin alƙawarin ci gaba da haɗa kai da sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, mata da matasa domin samun ci gaba mai ɗorewa a jihar Katsina.

Address

Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina State Community Development Programme posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share