14/08/2026
ALƘALIN ALƘALAI YA YI ALƘAWARIN BAIWA HUKUMAR HISBAH GOYON BAYA
Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta kai ziyara ga Alƙalin Alƙalan Jihar ranar Laraba 12/8/2026.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Katsina, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar) ya bayyana maƙasudin wannan ziyara a matsayin neman shawarwari da yin aiki tare. Ya kuma yi bayanin irin ayyuka da nasarorin da Hukumar ta samu tun kafa ta. Sannan ya bayyana irin yadda Hukumar ta ke shirye wajen karɓar shawarwari daga sauran hukumomi da ɗaiɗaikun mutane.
Yayin da yake maida bayani, Alƙalin Alƙalan Jihar Katsina (Grand Khadi) Kabir Abubakar ya ba Hukumar shawarwari masu muhimmanci a wajen gudanar da ayyuka cikin nasara, sannan ya yi alƙawarin goyon bayan Hukumar Shari'ah da kotunan Shari'ah na Jihar ga Hukumar ta Hisbah domin ganin ta gudanar da ayyukanta cikin nasara.
✍️ Aminu Aliyu Albany,
ACG, ICT.