07/09/2026
SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR KURFI YA ZIYARCI IYALAN YARA BIYU DA AKA KASHE A GARIN ’YAR LIYA’U.
Mai Girma Shugaban Ƙaramar Hukumar Kurfi, Malam Babangida Abdullahi Kurfi, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan yara guda biyu da wani marar imani ya yi wa kisan gilla a garin ’Yar Liya’u.
A yayin ziyarar, Mai Girma Shugaban ya bayyana matuƙar alhininsa da wannan mummunan lamari, yana mai cewa irin wannan aika-aika babban abin takaici ne kuma rashin imani ne da tausayi.
Mai Girma Shugaban ya kuma bayar da umarni ga jami’an tsaro da su ƙara kaimi wajen gudanar da bincike, domin gano wanda ya aikata wannan mummunan aiki tare da tabbatar da cewa ya fuskanci hukunci a gaban doka.
Malam Babangida Abdullahi Kurfi ya roƙi Allah Ya bayyana wanda ya aikata wannan aika-aika, Ya bai wa jami’an tsaro damar gano shi, sannan Ya bai wa iyalan marigayin ƙarfin hali da haƙurin jure wannan babban rashi.
Allah Ya jiƙan waɗannan yara, Ya gafarta musu, Ya sanya Aljannatul Firdausi ce makomarsu. Allah Ya tona asirin wanda ya aikata wannan mummunan aiki, Ya kuma kawo ƙarshen irin waɗannan ayyukan ta’addanci a cikin al’umma.
Amin Ya Rabbal Alamin.
OFISHIN YAƊA LABARAI NA SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR KURFI
07/09/2026.