20/05/2026
Gwamna Radda Yayi Kira Ga ’Yan Takarar APC Da Su Fita Neman Al’umma Gida-Gida Gabanin Zaɓen 2027
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, yayi kira ga dukkan ’yan takarar jam’iyyar APC masu neman mukamai a kujeru daban-daban da su fara Fita Neman Al’umma Gida-Gida Gabanin Zaɓen 2027
Gwamnan yayi wannan kiran ne yayin da yake karɓar wata babbar tawaga daga iyalan fitaccen ɗan kasuwa kuma mai ayyukan alheri, Alh Dahiru Barau Mangal, ƙarƙashin jagorancin dan takarar majalisa mai wakiltar mazabar Katsina, Barrista Abba Dahiru Mangal, a ziyarar godiya da s**a kai masa.
Gwamna Radda ya buƙaci ’yan takarar da su kusanci al’umma tare da neman addu’o’i da goyon baya daga masu ruwa da tsaki, shugabannin al’umma da malaman addini a faɗin jihar.
Haka kuma, ya yabawa ’yan takarar da s**a janye wa Barrista Abba Mangal a takarar kujerar Majalisar Wakilai, inda ya bayyana hakan a matsayin alamar haɗin kai da balagar siyasa a cikin jam’iyyar APC.
A nasa jawabin, Barrista Abba Mangal ya yabawa salon shugabanci na Gwamna Radda, yana mai cewa nagartaccen shugabancinsa ne ya tabbatar da gudanar da zaɓukan fidda gwani cikin nasara da lumana a faɗin jihar.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa idan aka zaɓe shi zuwa Majalisar Tarayya, zai bayar da wakilci nagari tare da kare muradun al’ummarsa yadda ya kamata.
✍️ Secretary APC YOUTH POLITICAL AWARENESS FORUM MATAZU
May 20, 2026.