16/02/2026
Maitaimakama Shugaban Kasa kan harkokin Siyasa, Ibrahim Masari Ya Raka Shugaba Tinubu Ziyara Ta Kwana Daya Domin Kaddamar Da Manyan Ayyuka a
Yola, Jihar Adamawa.
Mai Girma, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Al’amuran Siyasa da sauran Ayyukan yau da kullum, yabi sahun Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR) a wata ziyarar aiki ta kwana guda zuwa birnin Yola na Jihar Adamawa.
A yayin ziyarar, Shugaba Tinubu ya kaddamar da muhimman ayyuka da dama wadanda Gwamnan Jihar Adamawa, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri ya aiwatar. Wadannan ayyuka, sunshafi sassa daban-daban da s**a hada da samar da ababen more rayuwa, kyautata ayyukan gwamnati, an tsara su ne domin bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummar Jihar Adamawa.
Taron ya samu halartar Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan harkokin Tsaron Kasa (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, da gwamnoni, manyan jami’an gwamnatin tarayya da na jihohi, shugabannin siyasa, da sauran manyan baki.
Shugaba Tinubu ya jinjina wa gwamnatin Jihar Adamawa bisa jajircewarta wajen kawo sauye-sauyen ci gaba, sannan ya jaddada shirye-shiryen gwamnatin tarayya na karfafa hadin gwiwa da gwamnatin jihohi domin ciyar da tsarin "Renewed Hope Agenda" (Sabuwar Akidar Fatan Alheri) gaba.
Haka kuma Alh Ibrahim Masari ya nanata kudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da kwanciyar hankali a fagen Siyasa, hadin kan kasa, da shugabanci na kowa-da-kowa a matsayin muhimman ginshikan samar da ci gaba mai dorewa a fadin Najeriya.
16 ga Fabrairu, 2026
Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)