Ibrahim Masari Solidarity Organisation IMSO

Ibrahim Masari Solidarity Organisation IMSO Advancing the Renewed Hope Agenda through the office of H.E. Ibrahim Masari, S.A Political Matters

10/08/2026

Babu ruwan Tinubu idan kun ga ba'ayi maku daidai ba mu ne domin mune aka ba bamuba ku ba - H.E. Ibrahim Kabir Masari.

TSOHON SHUGABAN JAM'IYYAR PDP NA JIHAR KATSINA MAIWADA DAUDAWA, YA SAKE JADDADA GOYON BAYANSA GA APC, TINUBU DA GWAMNA R...
08/08/2026

TSOHON SHUGABAN JAM'IYYAR PDP NA JIHAR KATSINA MAIWADA DAUDAWA, YA SAKE JADDADA GOYON BAYANSA GA APC, TINUBU DA GWAMNA RADDA

​Tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Alh. Maiwada Daudawa, tare da mambobin kwamitin gudanarwarsa, sun kai ziyarar ban-girma ga Babban Mai Taimaka Wa Shugaban Kasa na Musamman Kan Al'amuran Siyasa da Sauransu, Alh. Ibrahim Kabir Masari.

​A yayin ziyarar, Alh. Maiwada Daudawa da mambobin tawagarsa sun sake jaddada biyayyarsu, inda s**a dauki alkawarin yin aiki tukuru da Alh. Ibrahim Masari domin nasarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a bisa tsarin Renewed Hope na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, gami da gwamnatin Mai Girma Gwamna Dikko Umaru Radda na Jihar Katsina.

​Ziyarar ta kara nuna azamar da suke da ita ta goyon bayan kokarin karfafa jam'iyyar APC da kuma ciyar da tsare-tsaren ci gaba na Gwamnatin Tarayya da na Jihar Katsina gaba.

​Sauran wadanda s**a halarci taron sun hada da Hon. Jabiru Tsauri, Hon. Ahmed Dayyabu Safana, Hon. (Dr.) Shehu Garba Matazu, Hon. Anas Isah Kankara, da kuma Dr. Abu Ammar.

​Sa hannu:
Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)

ALHAJI IBRAHIM KABIR MASARI YA ZAUNA DA HAƊAƘAR MATASAN IZALA DA ƊARIKA YAYIN DA ƘUNGIYAR TA SAKE TABBATAR DA GOYON BAYA...
08/08/2026

ALHAJI IBRAHIM KABIR MASARI YA ZAUNA DA HAƊAƘAR MATASAN IZALA DA ƊARIKA YAYIN DA ƘUNGIYAR TA SAKE TABBATAR DA GOYON BAYANTA GA APC A GABANIN ZAƁEN 2027

​Maigirma Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Al'amuran Siyasa da Sauran Al'amurra, ya karɓi bakuncin shugabannin Haɗaƙar Matasan Izala da Ɗarika na Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Dr. Abu Ammar, a wani zaman shawara na musamman da aka tattauna kan ci gaban siyasa, tattara goyon bayan mutanen karkara, da kuma shirye-shiryen zaɓen shekara ta 2027.

​Zaman ya tara mambobin haɗaƙar, jami'an siyasa, da waɗanda shugaban ƙasa ya naɗa daga Jihar Katsina domin tattauna batutuwan da s**a shafi buƙatun juma'a, tare da ba da muhimmanci wajen ƙarfafa Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), inganta haɗin kai, da ƙara ƙarfafa sadarwa da mutanen ƙarƙashin ƙasa a gabanin zaɓen 2027.

​A yayin zaman an tattauna yadda haɗaƙar ta sake jaddada goyon bayanta na tsayin daka ga Jam'iyyar APC, inda ta yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da duk waɗanda abin ya shafa wajen ƙarfafa jam'iyyar da kuma tabbatar da nasararta a zaɓe.

​A jawabin da ya yi, Shugaban Haɗaƙar, Dr. Abu Ammar, ya jinjina wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa jagorancinsa da ƙoƙarin da yake yi wajen ciyar da ƙasa gaba. Ya sake tabbatar da ci gaba da goyon bayan haɗaƙar ga Shugaban Ƙasa da kuma Manufofin Gwamnatinsa na 'Renewed Hope Agenda'.

​Haka zalika, Dr. Abu Ammar ya yi kira ga al'umar Jihar Katsina da su kasance tsintsiya madaurinki ɗaya, kuma su ci gaba da goyon bayan Gwamna Dikko Umaru Radda, gami da sauran yan takarar Jam'iyyar APC a zaɓen 2027.
Sannan ya sake jaddada muhimmancin haɗin kai, tatare da goyon bayan al'umar ƙarƙara, da haɗa hannu wajen dorewar nasarorin APC gami da ciyar da manufofin ci gaban gwamnati gaba.
​Taron ya sami halartar manyan 'yan siyasa da jami'an gwamnati daga Jihar Katsina, waɗanda s**a haɗa da Hon. Jabiru Tsauri, Barr. Murtala Kankia, Hon. Ahmed Dayyabu, Hon. Shehu Garba Matazu, Hon. Anas Isa, Dr. Mukhtar Habib, da kuma Sama'ila Abdu.

​Wannan zaman tattaunawa ya sake nuna muhimmancin ci gaba da yin shawara da haɗin gwiwa tsakanin 'yan siyasa da ƙungiyoyin al'uma wajen ƙarfafa APC da haɓaka shiga harkokin siyasa a gabanin Babban Zaɓen 2027.

​Sa hannu:
Ofishin Yada Labarai
Kungiyar Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)

30 ga Yuli, 2026​Maigirma Ibrahim Kabir Masari Ya Halarci Taron 'ALO Breaking Barriers to Trade & Leadership Summit 2026...
30/07/2026

30 ga Yuli, 2026

​Maigirma Ibrahim Kabir Masari Ya Halarci Taron 'ALO Breaking Barriers to Trade & Leadership Summit 2026', Ya Kuma Karbi Lambar Yabo Ta Shugabanci.

​Maigirma Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Babban Mai Taimakawa Shugaban Kasa kan Al'amuran Siyasa da Sauran Al'amurru, ya halarci taron 'ALO Breaking Barriers to Trade & Leadership Summit 2026' wanda aka gudanar a Abuja. A wurin taron, Kungiyar Shugabancin Afirka (African Leadership Organisation - ALO) ta ba shi Lambar Yabo ta Shugabanci (Leadership Award) don kwazonsa a aikin gwamnati, kyakkyawan shugabanci, da kuma gudummawar da yake badawa wajen ci gaban siyasar Nijeriya.

​Taron ya tara manyan shugabannin Afirka, jami'an gwamnati, jakadu, maza da mata 'yan kasuwa, da abokan ci gaba domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen fadada kasuwanci tsakanin kasashen Afirka, karfafa shugabanci, da kuma hanzarta ci gaban tattalin arziki mai dorewa a duk fadin nahiyar.

Masari ya halarci taron ne a tare da Maigirma Mai Mala Buni, CON, Gwamnan Jihar Yobe; Farfesa Mohammed Kabir Isa, Shugaban Ma'aikata a Ofishin Babban Mai Taimakawa Shugaban Kasa kan Al'amuran Siyasa da Sauran Al'amurru; da kuma Hon. Yahuza Ado Inuwa, Shugaban Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Nijeriya (SON).

​A jawabin da ya yi bayan karbar lambar yabon, Maigirma Ibrahim Masari ya mika godiyarsa ga Kungiyar ALO bisa wannan karramawa, inda ya bayyana ta a matsayin wata daukaka da ke nuna muhimmancin tsayawa tsayin daka wajen yi wa al'umma aiki da kuma nuna shugabanci na gaskiya. Ya kuma kara da cewa wannan karramawa za ta kara kwarin gwiwa wajen ci gaba da goyon bayan manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, da kuma ba da gudummawa mai inganci wajen samar da haɗin kan kasa, kwanciyar hankali, da ci gaba mai dorewa.

​Sa hannu:
Ofishin Yada Labarai,
Kungiyar Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)

28/07/2026

H.E Ibrahim Kabir Masari Special Adviser to the President on Political and Other Matters, said Osun State APC governorship candidate Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji and the party is united and fully prepared to reclaim Osun State after the inauguration of the APC National Campaign Council in Abuja.
Tuesday 28th July 2026.

An Nada Alh. Ibrahim Kabir Masari a Matsayin Mataimakin Shugaban Kwamitin Kamfe na Jam’iyyar APC domin Zaben Gwamnan Jih...
26/07/2026

An Nada Alh. Ibrahim Kabir Masari a Matsayin Mataimakin Shugaban Kwamitin Kamfe na Jam’iyyar APC domin Zaben Gwamnan Jihar Osun

​Ofishin Mai Girma, Alh. Ibrahim Kabir Masari, Mai Taimakawa Shugaban Kasa na Musamman kan harkokin Siyasa da Sauran Al'amura, yana farin cikin sanar da nadin da aka yi masa a matsayin Mataimakin Shugaban Kwamitin Kamfe na Kasa na Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) domin gudanar da zaben gwamna mai zuwa a Jihar Osun.

​Mai Girma Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma (CON), shi ne shugaban wannan kwamiti na kamfe na kasa.
​Wannan muhimmin nadi yana nuna kwarin gwiwa da amincewar da shugabannin jam'iyyar APC ke da ita a kan Alh. Ibrahim Kabir Masari, sannan yana nuna irin kwarewarsa ta siyasa, hangen nesa, da kuma kyakkyawar sadaukarwarsa ga muradun jam'iyyar, haɗin kanta, da ci gabanta.

​A matsayinsa na Mataimakin Shugaba, Alh. Ibrahim Kabir Masari zai yi aiki kafada da kafada da Shugaban Kwamitin, Mai Girma Sanata Hope Uzodimma, tare da sauran mambobin kwamitin domin samar da jagoranci na gaskiya, karfafa alaka da masu ruwa da tsaki, da kuma fito da tsare-tsaren da za su tabbatar da samun gagarumar nasara ga jam'iyyar APC a zaben gwamnan na Jihar Osun.

​A jawabinsa bayan samun wannan nadi, Alh. Ibrahim Kabir Masari ya mika godiyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR) da kuma shugabannin jam'iyyar APC abisa amincewa da kwarin gwiwar da s**a nuna masa. Ya sake jaddada aniyarsa ta sauke wannan nauyi da aka dora masa domin don ganin jam'iyyar APC takai ga matakin nasara.

​Bugu da kari, ya yi kira ga shugabannin jam'iyyar, mambobi, da sauran masoya a fadin kasar nan da su kasance tsintsiya madauraki daya, su ci gaba da kasancewa da kwarin gwiwa wajen neman nasara a zaben Jihar Osun, inda ya jaddada cewa haɗin kai, da sadaukarwa su ne ginshikin ci gaban jam'iyyar.

​Sa Hannu:
​Ofishin Yada Labarai
Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)

Alhaji Ibrahim Kabir Masari Ya Wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a Taron Tunawa da Marigayi Janar Hassan Us...
25/07/2026

Alhaji Ibrahim Kabir Masari Ya Wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a Taron Tunawa da Marigayi Janar Hassan Usman Katsina Karo na 3

Kaduna, Najeriya | 25 ga Yuli, 2026

Mai Girma Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa da Sauran Lamurra, ya wakilci Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a Taron Tunawa da Marigayi Janar Hassan Usman Katsina karo na uku, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna.

Taron ya haɗa fitattun dattawan ƙasa, jami'an gwamnati, malamai, sarakunan gargajiya da sauran manyan baƙi domin karrama gudunmawar marigayi Janar Hassan Usman Katsina, wanda jagorancinsa nagari, kishin ƙasa da sadaukarwarsa wajen yi wa ƙasa hidima s**a ci gaba da zama abin koyi ga al'ummomin Najeriya.

Daga cikin manyan baƙin da s**a halarci taron akwai Ministan Gidaje da Raya Birane, Injiniya Muttaka Rabe Darma; Farfesa Sadiq Abdullahi; da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, wanda Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG) ya wakilta, tare da sauran manyan baki masu daraja.

Yayin da yake gabatar da saƙon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya bayyana muhimman nasarorin da aka samu ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda. Ya bayyana irin ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi wajen ƙarfafa tsaro, faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi ta hanyar Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) da shirye-shiryen Koyar da Sana'o'i da Fasahohin Aiki (TVET), bunƙasa cibiyoyin ilimi ta hannun TETFund, da kuma aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa kamar Titin Abuja–Kaduna–Zariya, Titin Zariya–Hunkuyi, da Babbar Hanyar Sokoto–Badagry.

Ya kuma jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na ci gaba da aiwatar da manyan sauye-sauye da za su haɓaka tattalin arziki, samar da damammaki ga 'yan ƙasa, tare da inganta rayuwar al'ummar Najeriya.

Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya yabawa masu shirya taron bisa ci gaba da gudanar da wannan taron na tunawa a duk shekara, yana mai bayyana hakan a matsayin kyakkyawar hanyar girmama rayuwa da tarihin marigayi Janar Hassan Usman Katsina, wanda kyawawan ɗabi'unsa na gaskiya, riƙon amana, jarumtaka, ladabtarwa da sadaukar da kai ke ci gaba da jagorantar muradun ƙasa.

Haka kuma ya sake jaddada ƙudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ƙarfafa haɗin kan ƙasa, inganta shugabanci nagari da tabbatar da isar da ribar dimokuraɗiyya ga al'umma ta hanyar shirin Renewed Hope Agenda.

A ƙarshe, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai tare da bai wa gwamnati cikakken goyon baya domin gina ƙasa mai zaman lafiya, tsaro da wadata ga kowa da kowa.

Ofishin Yaɗa Labarai
Ibrahim Masari Solidarity organisation (IMSO)

Shugaba Tinubu Ya Sanar da Nade-Nade Sababbi guda 26.​Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da nadin sababbin mukamai guda ...
20/07/2026

Shugaba Tinubu Ya Sanar da Nade-Nade Sababbi guda 26.

​Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da nadin sababbin mukamai guda 26 a hukumomi da kwamitocin gwamnatin tarayya guda 10, inda tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya zama shugaban Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), yayin da Laftanar Janar Junaid Bindawa ya zama shugaban Hukumar Kula da Albashi da Bada Tallafi na Kasa (National Salary and Wages Commission).

​Fayose ne zai jagoranci kwamitin gudanarwa na REA, tare da Alhaji Ahmadu Abubakar da Injiniya Ilyasu Ibrahim Makinta wadanda aka nada a matsayin mambobi kuma daraktoci ba na dindindin ba. Babban Darakta mai ci na hukumar, Abba Abubakar Aliyu, da sauran daraktoci guda uku da aka nada a baya su ne za su cike sauran mambobin kwamitin gudanarwar.

​Shugaba Tinubu ya kuma nada sauran mutane takwas a Hukumar Albashin tare da Maj. Gen. Bindawa. Tsohuwar mamba a Majalisar Wakilai daga jihar Lagos, Olajumoke Okoya-Thomas, ita ce sabuwar sakatariyar hukumar. Dr Ogbole Ene Lilian, Oladele Olatubosun, da Yakubu Umar Barde, wadanda ke wakiltar jihohin Benue, Oyo, da Kaduna, an nada su a matsayin kwamishinoni.

​Dr Mai Adamu Yau (daga Borno), Ginika Florence Tor (Enugu), Injiniya Lawrence Okoh (Edo), da Bello Morenike Iyabode (Kogi) an nada su a matsayin mambobin Hukumar.
​Tosin Johnson Adeyanju, wanda a baya aka nada a matsayin Babban Sakatare na Asusun Amintattu na C**a na Kasa (NLTF), yanzu an mayar da shi zuwa Hukumar Rabon Kudi da Tsara Rarraba Arziki ta Kasa (RMAFC) a matsayin Sakatare.

​Haka zalika, Shugaba Tinubu ya nada Dr Abuh Mohammed a matsayin Babban Darakta na Hukumar Kididdigar Jama'a ta Kasa (NPC), Dr Akinola Odeyemi a matsayin Shugaban Kamfanin Sayen Wutar Lantarki na Nijeriya (NBET), da kuma Dr Anthony Inalegwu Godwin a matsayin Shugaba/Shugaban Gudanarwa na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Nijeriya (NAEC). Injiniya Julius Oloro, tsohon shugaban karamar hukuma, shi ne sabon Babban Darakta na Cibiyar Kula da Kayan Noma ta Kasa (NCAM) da ke Kwara, wanda ya karbi ragamar daga hannun Dr A.R. Kamal, wanda ya rasu a watan Janairu na shekarar da ta gabata.

​Shugaba Tinubu ya kafa kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Hakkin Sanya Kudi a Fannin Kuɗi (Fiscal Responsibility Commission), tare da nada Dr Abdullahi Maikano Saidu a matsayin shugaba. Mambobin kwamitin sun hada da Mohammed Asmau, Mohammed Aliyu Makama, Dr Suleiman Gidado, Louis O. Ndukwe, Amaechi Ugwele, da Olaniyi Idowu Onikola.
​Shuni Muhammad Dahiru shi ne sabon Babban Sakatare na Hukumar Yaki da Rashin Imi, Ilimin Manya da Na Waje da Makanta (NMEC), wanda ya karbi gurbin Prof. Shu'aibu Shehu Aliyu, wanda aka mayar zuwa Asusun Tallafawa Bunkasa Fannin Fetur (PTDF) a watan Afrilu.

​Domin maye gurbin Mathias Byuan, tsohon daraktan kudi na Hukumar Gidaje ta Tarayya (FHA) wanda ya yi murabus don tsayawa takarar gwamna a jihar Benue, Shugaba Tinubu ya nada Gisaor Vincent Iorja. Iorja masanin tattalin arziki ne, masanin shari'a, kuma malamin jami'a mai ci a yanzu a matsayin sakataren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Benue (BSIEC).

​Dukkanin wadannan nadade-nadade za su fara aiki nan take.

​Bayo Onanuga
Babban Mai Taimakawa Shugaban Kasa na Musamman
(Ayyukan Watsa Labarai da Tsare-Tsare)
20 Yuli, 2026

Mai Girma, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mai ba Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Lamuran Siyasa da Sauran Al'amura, ...
13/07/2026

Mai Girma, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mai ba Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Lamuran Siyasa da Sauran Al'amura, ya kai ziyarar ta'aziyya ga Alhaji Hadi Maidawa na garin Malumfashi, tsohon Akanta kuma Sakataren Karamar Hukumar Kafur, biyo bayan rasuwar mai dakinsa, marigayiya Hajiya Fatima Hadi Maidawa.

​Yayin ziyarar, ya nuna alhininsa da jaje ga Alhaji Hadi Maidawa da daukacin iyalansa bisa wannan babban rashi, inda ya roki Allah Madaukakin Sarki (SWT) da ya yafe wa marigayiyar kurakuranta, ya yi mata rahama, kuma ya ba ta masauki a Aljannatul Firdausi.

​Ya bayyana cewa rashin masoyi babban jarrabawa ne mai wahala, sai dai ya tunatar da iyalan cewa kowace rai za ta dandani mutuwa a lokacin da Allah S.W.T ya tsara mata. Don haka ya bukace su da su karbi kaddarar Ubangiji cikin hakuri, kuma su ci gaba da yi wa marigayiyar addu'ar samun gafarar Ubangiji SWT.

​Haka kuma, ya karfafa gwiwar iyalan na Alh Hadi Maidawa ta hanyar dogaro ga Allah madaukakin sarki da kuma kyakkyawan tarihin rayuwa da halaye na kwarai da marigayiya Hajiya Fatima Hadi Maidawa ta bari, tare da rokon Allah (SWT) ya ba su juriya da karfin gwiwar jure wannan babban rashi.

Da karshe ​Ya kuma yi addu'ar Allah (SWT) ya sanyaya wa iyalan zukata, Allah ya haskaka kabarin marigayiyar, Allah ya sanyara a Aljannatul Firdausi.

​Muna rokon Allah Madaukakin Sarki (SWT) ya jikan marigayiya Hajiya Fatima Hadi Maidawa, ya karbi ayyukanta na kwarai, ya ba ta hutu na har abada a Aljannatul Firdausi, sannan ya bai wa iyalanta hakuri da karfin gwiwa a wannan lokaci na zaman makoki. Amin.

​Sanya Hannu:
Ofishin Yada Labarai,
Kungiyar Solidarity ta Ibrahim Masari (IMSO)

10/07/2026

Address

No:2&3 Nanaco Plaza, 001 Gidan Dawa, Commercial Layout
Katsina
820101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ibrahim Masari Solidarity Organisation IMSO posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share