GYARA KAYAN KA

GYARA KAYAN KA Wannan page mun buɗe shi ne domin faɗakarwa ilmantar wa zuwaga yan'uwa musulmai

06/11/2025
06/11/2025

RUWA CIKIN COKALI,
Ra'ayin: Abdallah Amdaz
Ba zanga laifin sauran Qungiyoyi addinin musulunci rinsu Tijjaniya Qadiriyya da sauransu, idan sun kai karar Mallam Lawan Kotu ba, tunda adalci suke bukata sai kotu tayi musu irin wanda zai gamsar dasu tunda shura ta gaza gamsar dasu da hukuncinta.

Sai a gayyaci mallam lawan kotu ya sake zabga sabon karatu, irin dai abinda akayi a shura in gaskiya ta fito sai a karba, in kuma ya gaza sai a hukuntashi da laifinsa, wannan dai dai ne kuma normal ne.

To amma dakata, menene ya kawo maganar interfaith a sabgar Annabi Muhammad صلى الله عليه وسلم ? Shin basu bane masu akidar kowa yai addininsa yanda yaga dama, a hada kai da masu bautar wanin Allah? Ko nine bagane ba a fahimtar dani.

Shin basune suke ganin da wanda yace Allah nada ‘ya’ya da wanda yace Allah daya ne duk tafiyarsu daya bace imani ne?.

Koba su bane suke yaki da abinda Annabi Muhammad صلى الله عليه وسلم ya koyar na tauhidi da kyawawan dabi’un salihan bayi da koyarwar alqur’ani, saboda tunaninki raunanne?

Kuma sai a gurbin kare Annabi Muhammad Allah ya kara yarda da aminci gareshi, sai su shiga ciki anya wannan abun kuwa ba tafiyar kura bace!

Ko kuma kokarin kare kungiyanci wanda kusan shi ne ummul aba’isin wannan dambarwa?

Ni a nawa tunanin Indai maganar Annabi Muhammad صلى الله عليه وسلم ake gaskiyar magana ku cire interfaith, domin ita kanta kalmar ma ta sabawa Allah.

Don a akidar interfaith dake fakewa da sunan zaman lafiya akwai sabawa Tauhidi tunda wajen tattaunawa an amince da abinda wasu addinai suke babu sukar juna babu yi musu wa’azi koda sunce Allah yana da yaya da sauran kafurci iyazan billah, wa’azinka na almajiranka ne da wanda sukai imani dakai. Tab dirkaniya to Aida tun farkon duniya babu Annabin da zai yada tauhidi kuma gashi Allah yace sakon Annabawa duk daya ne.

Allah ya kyauta! Nayi shiru abuna!

Karka min comment idan baka fahimci abinda na rubuta ba, idan kamin comment bad Allah ya isa ban yafe ma kowaye ba, don nasan manufata ta yin wannan alkairi ce da kaunar musulmai da janibin Annabi Muhammad صلى الله عليه وسلم , don haka idan wani wanda bai fahimci kansa bama ba dashi nake magana ba.

Ka fara sanin ma’anar interfaith a musulunci sannan kasan shi a duniyar yau sai kayi comment ya rage ya naku kungiyoyi zaku bi da son zuciyar malamai ko Allah da manzonsa صلى الله عليه وسلم

01/11/2025

Ka faɗi gaskiya, Allah saka ma da Alkhairi

01/11/2025
16/10/2025

اللَّهُمَّ اجْلِبْ إِلَيَّ الزَّبَائِنَ الصَّالِحِينَ، وَاجْعَلْ فِي بَيْعِي وَشِرَائِي بَرَكَةً دَائِمَةً

Ajami:
Allahumma ajlib ilayya az-zabā’inaṣ-salihin, waj‘al fī bay‘ī wa shirā’ī barakatan dā’imah

Fassara:
“Ya Allah, Ka jawo mini kwastomomi nagari, Ka sanya albarka a saye-da-sayarwata kullum.

16/10/2025

Hadin kan Darika da Tatsine Zeyiyu Kuwa Kalli Bulalan da Dan Gidan Sheikh Dahiru Bauchi Yama Su Dan Tatsine Masussuka,

Address

Birnin Kebbi
Kebbi
234

Telephone

+2348060644339

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GYARA KAYAN KA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category