Ismail Dalha Kusada

Ismail Dalha Kusada Former Member House of Representative Ingawa/Kankia/Kusada Federal Constituency, Katsina State

05/12/2025

JUMA'A BABBAR RANA

An ruwaito daga Aws bn Aws(RA), Ya ce: Manzon Allah SAW Yace: "Yana daga cikin mafificin ranakunku ranar JUMU'AH, Saboda haka ku yawaita SALATI a gareni a cikinsa, domin a na bijiro min da salatinku".
Abu Dawud ya ruwaito

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’unMun samu labarin rasuwar babban malami, jagoran addini kuma fitaccen shehi Sheikh Dahi...
27/11/2025

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un

Mun samu labarin rasuwar babban malami, jagoran addini kuma fitaccen shehi Sheikh Dahiru Usman Bauchi da bakin ciki da jimami. Wannan babban rashi ne ba kawai ga iyalan marigayi ba, har ma da al'ummar Musulmi baki ɗaya a Najeriya da ma duniya.

Shehin malami ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi, zaman lafiya da kyawawan halaye. Ya koyar da dubban dalibai, kuma ya bar tarihi mai cike da darussa da girmamawa.

Muna rokon Allah (SWT) da Ya gafarta masa, Ya sa kabarinsa ya kasance cikin lambun Aljanna, Ya kuma bai wa iyalansa da mabiyansa hakurin jure wannan babban rashi. Ameen.

Allah ya jikan Sheikh Dahiru Usman Bauchi Ameen.

21/11/2025

Yana da kyau idan mutum zai yi addu'a ya nutsu ya halarto da zuciyansa, ya daga hannayensa sama, ya fukanci Ubangiji tare da qanqan da kai(khushu'i) da nuna gajiyawa, da marairaicewa da nuna kasawa, da sakankancewa Allah yana ganinka yana jinka kuma yana tare da kai, kuma shi ya ke biyan bukatu baki daya, da yawan maimaita YA RABBI a cikin addu'a.

Juma'at Mubarak

14/11/2025

Yin sakaci da Azkar din safe da Yamma kamar yin sakaci ne ka bar wata k'ofa da sharri ko cutarwa za su iso gareka!

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’unCike da alhini da jimami, muna sanar da rasuwar Bebejin Katsina Hakimin Kusada Alh Nuh...
13/11/2025

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un

Cike da alhini da jimami, muna sanar da rasuwar Bebejin Katsina Hakimin Kusada Alh Nuhu Yashe Allah ya jikan sa da rahama.

Ina mika sakon ta’aziyata ga ilahirin al’ummar karamar hukumar Kusada iyalan marigayi, fadar hakimi da daukacin jama’a.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya sanya aljanna ce makomarsa, ya kuma ba mu da iyalan sa hakurin jure wannan babban rashi.

19/10/2025

Assalamualaikum.

Ina mika sakon ta’aziyya da juyayi ga al’ummar da abin ya shafa a wasu yankuna na Kankia da Kusada sakamakon iftila’in hare-haren ’yan ta’addan daji.

Hakika wannan mummunan lamari ya tayar da hankali kuma ya sake jaddada bukatar tsauraran matakai daga hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Muna jajantawa iyalan wadanda s**a rasa rayukansu, muna fatan Allah ya jikan su da rahma, ya kuma bai wa iyayen gwiwa da hakuri. Ga wadanda abin ya shafa, muna fatan samun sauki da saukin radadin wannan musiba.

Duk da muna fatan gwamnati zata dauki matakin gaggawa, muna rokon al’umma da su kara hakuri, da kuma yin addu’a domin samun karshen wannan matsala.

Allah ya kare mu baki daya, ya dawo mana da zaman lafiya a wannan yanki da kasa baki daya amin.

18/07/2025

LOKACI SHINE RAYUWA

Duk wanda ya halakar da lokacinsa to ya halakar da rayuwarsa, wanda kuwa ya halakar da rayuwarsa zai yi nadama, kuma nadamar ba za ta amfaneshi ba.

Juma'at Mubarak

11/07/2025

KU LALUBI LOKACIN KARBAN ADDU'AR RANAR JUMA'A

Manzon Allah SAW yace:"A (Ranar) Juma'a a kwai wani lokaci da babu wani bawa musulmi da zai dace da ita, yana a tsaye yana sallah, sai ya rok'i Allah wani alkhairi face Allah ya bashi". Bukhary da Muslim

Magana mafi rinjaye shine wannan lokaci yana a tsakanin bayan la'asar ne zuwa faduwar rana.

Allah ya datar damu wannan lokaci ya amsa mana addu'oinmu.

Juma'at Mubarak

Address

Kusada
833

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ismail Dalha Kusada posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share