23/11/2025
Jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da neman ɗaliban da ƴanbindiga s**a sace a makarantunsu cikin makon da ya gabata.
A ranar Alhamis da daddare ne wasu mahara s**a sace ɗalibai fiye da 300 a makarantar kwana ta garin Papiri na jihar Neja kwana biyar da sace ɗaliban jihar Kebbi.
Wannan al'amari ya janyo firgici da razani a ƙasar, lamarin da ya sa wasu jihohi masu maƙwabtaka s**a ɗauki matakin rufe makarantunsu.