13/07/2026
BUILDING YOUR FUTURE AMBASSADORS' INITIATIVE (BYFAI)
GAISUWAR TA'AZIYYA
Shugabanci da ɗaukacin mambobin Building Your Future Ambassadors' Initiative (BYFAI) sun karɓi labarin rasuwar Alhaji Shamsudeen S. Ahmed (Kala) cikin matuƙar alhini da jimami.
Marigayin, wanda ya rasu a birnin Abuja, ya kasance Jami'in Hulɗa da Gwamnan Jihar Katsina a Ofishin Hulɗa na Gwamnatin Jihar Katsina da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja, sannan kuma tsohon Darakta Janar na Furotokol ga Gwamnan Jihar Katsina. Ya kasance mutum mai biyayya, ƙwazo, riƙon amana da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukan gwamnati da hidimtawa al'ummar Jihar Katsina.
A madadin shugabancin ƙungiyar, Darakta Janar na BYFAI, Dr. Isah Rabe Kambarawa, CPM, CPD , CHRM, yana miƙa saƙon ta'aziyya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda, CON, bisa wannan babban rashi da ya samu Katsina State Government.
Haka kuma, muna miƙa ta'aziyyarmu ga iyalan marigayin, 'yan uwansa, abokan aikinsa da duk masu alhini, tare da yin ta'aziyya ta musamman ga mambobin BYFAI da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi, inda marigayin ya fito, da ma Shiyyar Funtua baki ɗaya, da fatan Allah Ya ba su juriyar jure wannan babban rashi.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin, Ya yafe masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, sannan Ya bai wa iyalansa, Gwamnatin Jihar Katsina da daukacin al'ummar jihar haƙurin jure wannan babban rashi.
Lallai ga Allah muka fito, kuma gare Shi za mu koma.
Sanarwa:
Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa
Building Your Future Ambassadors' Initiative (BYFAI)
Litinin, 13 ga Yuli, 2026
28 ga Al-Muharram, 1448
Hannatu Musa Musawa
Alh. Ibrahim Kabir Masari
Gwagware Foundation
City Boy Movement Katsina State
Renewed Hope Katsina State
GMTD
Katsina State Television KTTV
Katsina State Radio Service -KTRS
@