Gaskiya Tafi Kwabo, Biu

Gaskiya Tafi Kwabo, Biu Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gaskiya Tafi Kwabo, Biu, Social service, Biu, Maiduguri.

26/03/2026

Matasan Biu kamata mu waye abinda ya faru a Gombe abin takaici ne Kuma cin mutuncin juna domin Gina duniyar wani ta haka nuna lalata lahirarku domin ginawa wani NASA duniyar wannan asara ce.

26/03/2026

Gaskia yaran Team da Forum basu yi kyakyawar wakilci wa Biu ba a Gombe. Shiyasa muke ganin jagaliyancin siyasa bashi da amfani Yan Biu mu waye.

06/03/2026

Anyi rabon kayan abinci da gwamna ya tura Fatan a bawa talakawa mabukata ba wa Yan siyasa kadai ba.

BARAZANAR TSARO DA BARIN TUBABBUN BOKO HARAM CIKIN GARIN BIU KAN IYA HAIFARWA Duk wani mai cikakkiyar hankali da hangen ...
27/02/2026

BARAZANAR TSARO DA BARIN TUBABBUN BOKO HARAM CIKIN GARIN BIU KAN IYA HAIFARWA

Duk wani mai cikakkiyar hankali da hangen nesa zai San cewa halin da Biu ke ciki a yau ya kai kololuwar damuwa. Barin wasu “tsoffin Boko Haram da s**a ce sun tuba” suna yawo cikin gari suna ɗauke da manyan makamai, ba tare da kulawa ba, kuma cikin hali na tsiya babbar barazana ce kai tsaye ga rayukan al’ummar garin Biu.

Binciken baya-bayan nan ya nuna mummunan salo na tashin hankali. Rahoton da ya bayyana cewa tubabbun Boko Haram sun harbi mutane huɗu saboda direba ya ƙi daukansu a mota kyauta, Wanda hakan ya tabbatar da cewa waɗannan mutanen har yanzu suna da tunanin yaki, halin cin zarafi, da gaggawar kashe mutum ba tare da wata hujja ba.

Babu wata ƙasa mai bin ƙa’ida da za ta bari irin waɗannan mutane su riƙe makamai a cikin gari musamman cikin gari.

Barin tubabbun Yan Boko haram da makamai cikin gari tamkar kitsa time bombn ne da zai iya tashi a kowane lokaci.

Ko makamin da suke ɗauke da shi kaɗai ya isa zama barazana ga jama’a, b***e kuma halin rashin hankalin da suke nunawa.

Mutanen Biu ba bukatar aminci—inda za su iya tafiya, bacci, da harkokinsu Wanda kasancewar tubabbun Boko Haram cikin gari barazana ne ga al'ummah Biu baki daya

Mun kira ga gwamnati da masu ruwa dabtsaki da hukumomi da abin ya shafa da a cire waɗannan tubabbun Boko Haram masu makamai daga cikin fararen hula, a dawo da cikakkiyar kulawar jami’an tsaro.

27/02/2026

Allah ya sada mu da manzo rahama ya zama mai ceton mu
Allah ka yarda da mu ka kyatata karshen mu

26/02/2026

TUBABBUN BOKO HARAM SUN HARBI WANI DRIVER A GARIN BIU

Muna masu alhini da Allah wadai game da harbin driver da was tubabbun Yan Boko Haram a garin Biu kawai don sun nem ya dauke subkyauta ya ki

Muna kira ga shugabbanin garin Biu da hukumomi da abin ya shafa su sauki mata kin gaggawa.

Mu mutanen Biu bamu bukatar tubabbun Boko Haram suna shigo mana cikin gari a dakatar dasu ana hanasu shigo mana cikin gari wannan shine bukatar mu.

26/02/2026
26/02/2026

Yaa Allah ka sada mu da masoyinmu Annabi Muhammad SAW ka sanya mu cikin tawagarsa a ranar lahira

Address

Biu
Maiduguri
60305

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gaskiya Tafi Kwabo, Biu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category