04/09/2026
Gudummawar Miliyan 3 Domin Mauludin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam a Misau da Dambam
Kamar kowace shekara, Hon. Bappa Aliyu Misau, FCNA, ya bayarda gudummawar kuɗi har naira miliyan Uku (₦3,000,000) domin gudanar da Maulidin Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama a gidajen Shehunai, zawiyoyi, majalisai da ƙungiyoyi da ke faɗin Misau da Dambam baki-ɗaya.
Kamar yadda ya saba, Hon. Bappa Aliyu Misau ya bayar da wannan gagarumar gudummawa ne domin masu shirye-shirye da tsara zagaye gari su samar da ruwa, abinci da sauran abubuwan buƙata ga baƙi da mahalarta Maulidin, tare da taimakawa wajen tabbatar da gudanar da bukukuwan cikin farin ciki, natsuwa, tsari, walwala da annashuwa.
Isar da Gudunmawar Zuwa ga Zawiyoyi da Majalisai
Jagorori da aka damƙa gudunmawa gare su, sun tsara yadda za a isar da wannan gudummawa cikin tsari, domin ta isa ga zawiyoyi, majalisai da gidajen Shehunai daban-daban da ke faɗin Misau da Dambam, ta yadda kowa zai samu damar cin moriyar wannan alheri.
Hon. Bappa Aliyu Misau, FCNA, ya miƙa wannan gudummawa ne ta hannun G7 FOR SARKIN YAMMA SUPPORT GROUP, ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Umar Danfisa, tare da majalisar masu shirya Maulud, domin tabbatar da isar da gudummawar zuwa wuraren da aka tsara.
Saƙon Godiya
A madadin gidajen Shehunai, Zawiyoyi, Majalisi, da kuma ɗaukacin mabiya ɗarikar Tijjaniyya na jahar Bauchi, musamman al'ummar Misau da Dambam, sun miƙa saƙon godiya da yabo ga Hon. Bappa Aliyu Misau, FCNA, bisa wannan gagarumar gudummawa da ya saba ba su a duk irin wannan lokaci domin gudanar da Maulidin Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama ta bakin Muƙaddamin Dambam.
Majalisar ta gabatar da addu'o'i Allah Ya saka masa da mafificin alkhairi, Ya karɓa nasa waɗannan kyawawan ayyuka da yake yi wa addini, Ya sanya ta zama sanadin albarka da ɗaukaka a gare shi duniya da lahira, Ya ƙara masa lafiya, arziki da ikon ci gaba da tallafa wa al'umma, da nasara a dukkan matakai da yake na siyasa.
Haka kuma, sun miƙa godiya ga G7 FOR SARKIN YAMMA SUPPORT GROUP, ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Umar Danfisa, bisa jajircewarsu da ƙoƙarinsu wajen tabbatar da isar da wannan gudummawa ga gidajen Shehunai, Zawiyoyi, Majalisai da suke shirya Maulud.
Allah Ya karɓa mana ibadunmu, Ya karɓi Maulidin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad, Ya ƙara mana ƙaunar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, haɗin kai da zaman lafiya a Misau da Dambam, jahar Bauchi da Najeriya baki-ɗaya. Amin
Amin Ya Rabbal Alamin 🤲
G-7 for Sarkin Yamma
3 ga watan Satumba 2026