01/08/2026
SAKON GODIYA NA MUSAMMAN
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.
Cikin ikon Allah Maɗaukakin Sarki, Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa ya samu damar zuwa Jihar Yobe domin halartar Daurin Aure, inda ya samu kyakkyawar tarba da karamci daga Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Yobe, shugabannin jam’iyya, jagorori, dattawa, matasa, mata da sauran dimbin mambobin jam’iyyar PDP mai albarka a jihar.
Muna amfani da wannan dama domin miƙa saƙon godiya da matuƙar jin daɗi ga kowa da kowa da ya ba da gudummawarsa wajen ganin wannan ziyara ta kasance mai armashi da tarihi. Muna godiya ga dukkan shugabanni, jagororin jam’iyya, masu ruwa da tsaki, mambobi, magoya baya da duk wanda ya samu damar halarta ko ya bayar da gudummawa ta kowace hanya.
Hakika, irin wannan tarba da haɗin kai ya nuna cewa PDP a Jihar Yobe tana da ƙarfin zumunci da haɗin kai.
Muna kuma miƙa godiyarmu ta musamman ga Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Yobe da dukkanin jagororin jam’iyyar bisa kyakkyawar tarba da karamcin da aka nuna.
Muna addu’ar Allah Ya saka wa kowa da kowa da mafificin alheri, Ya ƙara haɗa kanmu, Ya ƙarfafa zumuncinmu da kishin jam’iyyarmu, sannan Ya ba Shugaban Jam’iyyar lafiya da ikon ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin nasara.
Allah Ya mayar da kowa gida lafiya, Ya kiyaye hanya, Ya albarkaci tafiyarku, Ya kuma sa wannan ziyara ta zama sanadin ƙarin haɗin kai da nasara.
Ameeen ya Allah