Molash Media Connect, Soba Local Government.

Molash Media Connect, Soba Local Government. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Molash Media Connect, Soba Local Government., Government Organization, Soba.

SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR SOBA A JIHAR KADUNA YA ƘADDAMAR DA RABON KAYAN AZUMI DA NA SALLAH A cikin yanayin da ake ciki n...
13/03/2026

SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR SOBA A JIHAR KADUNA YA ƘADDAMAR DA RABON KAYAN AZUMI DA NA SALLAH

A cikin yanayin da ake ciki na ibadar watan Ramadan, da kuma tunkarar bikin ƙaramar Sallah, shugaban ƙaramar hukumar Soba Hon. Muhammad Shehu Molash ya ƙaddamar da gagarumin rabo na musamman, da ya haɗa da shinkafa, da kuma zannuwa ga iyayen mu Mata, wanda ya gudana a ɗakin taro na sakateriyar ƙaramar hukumar Soba dake Maigana.

Rabon ya gudana ne bisa kyakkyawar jagorancinsa da yake gudanarwa na bai ɗaya, wanda hakan ke ba da damar kowa ya amfana ba tare da nuna bambancin jam'iya ko kuma gida-gida na siyasa ba. Mutane da dama sun amfana da s**a haɗa da; shuwagabannin jam'iya na kowane mataki, masu riƙe muƙaman gwamnati, 'yan siyasa, ƙungiyoyin Mata da Matasa, da sauran mutane daban-daban daga dukkanin lungu da saƙo na faɗin ƙaramar hukumar Soba.

Taron ya sami halartar mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Soba, shugaban ma'aikata / Kansilar ayuka na ƙaramar hukumar Soba, Kakakin Majalisar Kansiloli na ƙaramar hukumar Soba da sauran Kansilolin sa, dattawan jam'iyar APC na ƙaramar hukumar Soba, shugaban jami'ar APC na ƙaramar hukumar Soba da mataimakin sa, shuwagabannin jam'iyar APC na gundumomi da mambobin su, ƙungiyoyin Mata da Matasa daga dukkanin lungu da saƙo na ƙaramar hukumar Soba.

“A yayin jawabin shugaban ƙaramar hukumar na Soba, ya nuna jin daɗin sa, bisa ganin dandazon mutanen da za su amfana a dalilin wakilcin sa, kuma ya bayyana cewa in shaa Allahu wannan ba zai zama ƙarshe ba, kamar yadda ba shine farko ba. Bugu da ƙari, ya janyo hankulan mahalarta taron, da su mai da hankali wajen gudanar da addu'o'i ga ƙaramar hukumar, jihar Kaduna da Ƙasa baki ɗaya, cikin waɗannan kwanakin na goman ƙarshe cikin wannan wata mai albarka”.

13th March, 2026

Shugaban ƙaramar hukumar Soba Hon. Muhammad Shehu Molash, ya bi sahun takwarorin sa shuwagabannnin ƙananan hukumomi 23 n...
05/03/2026

Shugaban ƙaramar hukumar Soba Hon. Muhammad Shehu Molash, ya bi sahun takwarorin sa shuwagabannnin ƙananan hukumomi 23 na faɗin jihar Kaduna, wajen halartar taron kwamitin kasafi na asusun haɗin gwiwa (JAAC Meeting), wanda ya gudana a ɗakin taro na Sanata Uba Sani (Senator Uba Sani Conference Hall), dake ma'aikatan ƙananan hukumomin jihar Kaduna. Kwamishinan ƙananan hukumomi, Hon. Sadip Mamman Lagos shine ya jagoranci zaman.

3rd December, 2025

Today, the Executive Chairman of Soba Local Government, Hon. Muhammad Shehu Molash, attended the Technical Session of th...
05/03/2026

Today, the Executive Chairman of Soba Local Government, Hon. Muhammad Shehu Molash, attended the Technical Session of the Joint Account Allocation Committee (JAAC) meeting for the month of February 2026, chaired by the Honourable Commissioner of Local Government, Hon. Sadiq Mamman Lagos. The meeting held at the Senator Uba Sani Conference Hall, Ministry of Local Government Affairs, Kaduna.

5th February, 2026

YANZU YANZU: Shugaban ma'aikata / Kansilar ayuka na ƙaramar hukumar Soba Hamza Abdullahi Soba, ya wakilci shugaban ƙaram...
02/03/2026

YANZU YANZU: Shugaban ma'aikata / Kansilar ayuka na ƙaramar hukumar Soba Hamza Abdullahi Soba, ya wakilci shugaban ƙaramar hukumar Soba Hon. Muhammad Shehu Molash wajen ba da abincin azumi ga Limaman ƙaramar hukumar Soba su kimanin ɗari da saba'in da biyu (172).

Mai girma gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani CON shine ya aiko da kayan abincin a basu, ta hannun shugaban ƙaramar hukumar Soba, tare da alkawarin cewa za su ga saƙon kuɗin cefane ta asusun bankunansu nan ba da jimawa ba.

Yanda tsarin rabon zai kasance shine; kowane Limami zai karɓi buhun shinkafa 25kg guda biyu, jimla dukkanin su Limaman na ƙaramar hukumar Soba za su karɓi shinkafa 25kg buhu ɗari uku da arba'in da huɗu (344).

2nd March, 2026

ABIN SHA'AWA: A bayyanar da shugaban ƙaramar hukumar Soba Hon. Muhammad Shehu Molash ya yi jiya talata 24/02/2026 a gaba...
25/02/2026

ABIN SHA'AWA: A bayyanar da shugaban ƙaramar hukumar Soba Hon. Muhammad Shehu Molash ya yi jiya talata 24/02/2026 a gaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna domin gabatarwa tare da kare daftarin kasafin kuɗin ƙaramar hukumar Soba na shekarar 2026 a gaban kwamitin haɗin gwiwa kan kasafi da harkokin ƙananan hukumomi, ya gabatar da muhimman abubuwa da zai kawo cigaba na musamman karo na farko.

Zaman kare kasafin ya ba shugaban ƙaramar hukumar na Soba damar bayyana manyan manufofi da tsare-tsaren da gwamnatinsa ta sanya a gaba a wannan shekara ta 2026, inda kasafin kuɗin zai mayar da hankali kan bunƙasa ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, cigaban karkara, harkar noma, da kuma abinda ya shafi tsaro na rayuka da dukkanin dukiyoyin al'umma a dukkanin gundumomi goma sha ɗaya da muke da su a ƙaramar hukumar Soba.

Shugaban ƙaramar hukumar na Soba ya jaddada aniyar gwamnatinsa na cigaba da tafiya akan gaskiya, riƙon amana da kuma haɗe kawunan al'umma wuri guda, wanda ya yi daidai da manufofin gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin mai Girma Gwamna Malam Uba Sani.

A lokacin halartar taron, shugaban ƙaramar hukumar na Soba ya sami rakiyar Daraktan gudanarwa na kuɗi (DAF), tare da shugaban ma'aikata na gwamnatin ƙaramar hukumar Soba, da wasu daga cikin jami'an gwamnatin sa.

A ƙarshe, shugaban ƙaramar hukumar ya nuna jin daɗi tare da miƙa godiyar sa ga mataimakinsa, sakatariyar ƙaramar hukuma, Majalisar Kansiloli bisa shawarwari da s**a ba da, tare da aiki tuƙuru don ganin aikin ya kammala. Kuma ya tabbatar musu da cewa za'a aiwatar da kasafin kuɗin yadda ya kamata, domin cigaban al'ummar ƙaramar hukumar Soba baki ɗaya.

Sanya Hannu;
Yahuza Ibrahim Kinkiba
Babban Mataimaki na Musamman kan gudarwa na shafukan sa da zumunta, ga shugaban ƙaramar hukumar Soba.
25 ga Fabrairu, 2026

A zaman sa ofishi jiya litini 26/01/2026, shugaban ƙaramar hukumar Soba Hon. Muhammad Shehu Molash ya gabatar da muhimma...
27/01/2026

A zaman sa ofishi jiya litini 26/01/2026, shugaban ƙaramar hukumar Soba Hon. Muhammad Shehu Molash ya gabatar da muhimman uzurori kamar haka;

1- Ya karɓi baƙuncin Ɗaliban da s**a wakilci ƙaramar hukumar Soba a gasar faɗin kalmoni “Spelling B”, wacce Barr. Aysha Ahmad Mohammad ta shiryawa Ɗaliban shiyya ta ɗayan jihar Kaduna.

2- Ya gudanar da zama da dukkanin 'yan majalisun sa da s**a haɗa da; Kansiloli 11, kwamishinoni 3, masu ba da shawara 15, manyan mataimaka na musamman 25, da kuma masu taimakawa na musamman 80.

3- Ya shiga cikin garin Maigana, inda ya sake gabatar da ta'aziya karo na biyu ga Hon. Sani Mohd Iliyasu (Shahada) Maigana da dukkanin sauran 'yan uwansa, game da rasuwar Mahaifiyar su.


Halastaccen Shugaban ƙaramar Hukumar soba Hon. Muhammad Shehu Molash tare da rakiyar Mataimakinsa da kuma Shugaban Ma’ai...
25/01/2026

Halastaccen Shugaban ƙaramar Hukumar soba Hon. Muhammad Shehu Molash tare da rakiyar Mataimakinsa da kuma Shugaban Ma’aikata na fadar gwabnatin ƙaramar Hukumar Soba sun halarcin taron ƙarshe na gasar faɗin kalmomi (speeling bee), wanda Barr. Aysha Ahmad Muhammad ta shirya.

A yayin halartar taro Shugaban ƙaramar hukumar na Soba ya yaba da yadda ɗalibai s**a jajirce wurin fitar da al'ummar ƙaramar hukumar Soba kunya . Sanann ya jinjina ma Malamai da mahukunta Wanda s**a yi duk ƙoƙari don ganin ɗaliban mu sunzo wannan mataki .

Daga ƙarshe shugaban ƙaramar hukumar na Soba ya bama dukkan ɗaliban da s**a shiga gasar kyautar naira dubu ɗari (N100,000) ga kowanne su, domin ƙarfafamusu harkar karatu.

Muna addu’a Allah ya cigaba da ciyar da ƙaramar hukumar Soba gaba.

25-01-2026

Address

Soba

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Molash Media Connect, Soba Local Government. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share