12/06/2026
Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da sayen nau'o'in taki, ingantattun irorin amfanin gona da magungunan noma da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.652 domin ƙara wa kayan aikin noma da ƙananan hukumomin jihar s**a riga s**a samar wa manoma ƙarfi.
An bayyana hakan ne bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar ranar Alhamis a zauren majalisar da ke Gidan Gwamnatin Jihar Sokoto.
An bayyana cewa wannan mataki na sayen taki, ingantattun irori da magungunan noma na da nufin tabbatar da cewa manoma sun samu kayan aikin noman tun farkon damina domin su amfana da su yadda ya kamata a lokacin noman bana.
Har ila yau, Majalisar ta amince da sayen babura kirar Daylong guda 1,200 da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.609. Za a bai wa ma'aikatan gwamnati baburan ne ta hanyar tsarin rance.
Wannan na daga cikin alkawarin da Gwamna Ahmed Aliyu ya yi wa ma'aikata yayin bikin ranar Ma'aikata ta bana a jihar.
Haka kuma, Majalisar ta amince da ɗaga darajar Asibitin Kula da Lafiya na Farko na Gagi zuwa Babban Asibiti (General Hospital) kan kudi Naira miliyan 592.1.
Majalisar ta kuma amince da gina Cibiyar Kula da Lafiya ta Farko a Majemar Korino da ke yankin Tudun Wada a Ƙaramar Hukumar Sokoto ta Kudu kan kudi Naira miliyan 143.4, tare da gina ginin gudanarwa a cibiyar lafiya da ke kan titin Kontagora kan kudi Naira miliyan 192.9.
Bugu da ƙari, an amince da aikin gaggawa na siminti da gyaran magudanan ruwa da bututun ruwa da s**a rushe a bayan hanyar Rima Radio/Tudun Wada, wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 246.9.
Majalisar ta kuma amince da girkawa da kula da tsarin hasken filin jirgin sama (Airfield Ground Lighting – AGL) a Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa na Sultan Abubakar III da ke Sokoto, kan kudi Naira miliyan 113.4.
Source BBG Hausa