Bafarawa Akida Sokoto North Local Govt

Bafarawa Akida Sokoto North Local Govt Wannan shafin ne na manufofin Akidar siyasar Bafarawa a karamar hukumar Mulkin sokoto Ta Arewa da kewayenta.

01/01/2026
Tsakaninmu da Bafarawa.Ku aje siyasa a gefe, hakika Mai girma Tsohon gwamna jahar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafara...
20/12/2025

Tsakaninmu da Bafarawa.

Ku aje siyasa a gefe, hakika Mai girma Tsohon gwamna jahar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa (Garkuwan Sokoto) ya cancanci samun ragowa da mutuntawa, ba sai ya shiga wata jam'iyya ko alakanta kansa da wasu yan siyasa ba.

Ya kasance a tun tashin sa, yana yiwa addinin Musulunci da al'umma hidima, bayar da goyon bayansa ga taimako da yada ababen alheri ga dorewa zaman lafiya da ci gaban kasa ba jahar sokoto kadai ba.

Mafi rinjayen wadanda suke rubutu na cin fuska ko batanci da shagube akan wannan shugaba, Bawan Allah idan sun koma gida zasu tarar uwayen su ko yan uwansu ko masu gidajen su duk mafi rinjaye sun ci amfanin Bafarawa a bangare dabam dabam na rayuwa kamin abin da yake faruwa a yau.

Uwayen nasu sun amfana da arzikinsa da taimakonsa ta hanyoyi iri iri kamin su kai matsayin da suke a bisa yau, koma na wadanda suke yiwa fadanci.

Ko shakka babu, Bafarawa ya taka muhimmiyar rawa da aiki ga baiwa jahar Sokoto alkibla, daraja ta tarbiyya addini da ilmin zamani, daukaka a fannoni iri iri kamin da bayan mulkinsa.

Yayi mulki a cikin natsuwa, ci gaba da tarbiyya ga samarwa jahar Sokoto makoma mai amfani da habaka zamantakewa da inganta rayuwa tun daga 1999 zuwa 2007.

Kashi 90% bisa dari na wadanda s**a rika mukamai ko zama wata tsiya a cikin tafiyar siyasa a jahar Sokoto daga koyarwarsa da taimakonsa ne.

Don haka, wadanda ke ganin yin butulci ga taimako da kauda ido garesa, har wasu yan yaran social media na gidajensu, yaran da basu kammala balaga da sanin ciwon kansu ba; suke cin zarafin akansa, hakika basu yiwa al'umma adalci da godiya ba.

Ra'ayin siyasa ko goyon baya, kacokan yana ga mutum ne akan abin da ya dauka ko yake so; Mai girma Attahiru Bafarawa a farko da inda aka fito Allah Ya bashi lamuni da mafi rinjaye na dukkan wadanda suke tinkaho da zama wata tsiya a Sokoto da Zamfara; tabbata daga gidan siyasa sa da kokarinsa s**a fito har yau suke wani abu a cikin al'umma.

Babu wani shugaba mai hankali da mutunci da zai yarda yaransa na kushe da cin zarafin wani dattijo ko babban mutum saboda banbancin ra'ayin siyasa , sai fa idan ya koma DATTIJON WUKARI

Don haka, yin shagube, ko tsokana ko cin zarafi ga na taking Tsohon gwamna jahar Sokoto, Garkuwan Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa tamkar cin mutunci jahar Sakkwato ne da al'ummarta, kasance wani Uba, Kaka, kuma jagora ga dukkan wani mai bugun gaba dan siyasa ne a Sokoto a yau.
Gidan Bafarawa a siyasa, tankard Makaranta ce ta Firamare inda anan aka fara Kyenkyeshe kowane anhu da minhu kamin ya samu admission na ci gaba da karatun tsayi da kafarsa har yayi nasa.

Don haka tsakaninmu da Bafarawa sai addu'a da yi masa fatan alheri na makoma tagari a gobe, sakamakon irin tafarki da tsarin da yabi na aza jahar Sakkwato da siyasa Sakkwato a lokacin da yake da dama bisa sadaukarwa, zaman lafiya, ci gaba, da'a, mutunci, alheri, amfani, tarbiyya da gaskiya.

Duk mafi rinjaye na wanda yake hankoron wata tsiya ne a yau; ga jahar Sokoto daga gidansa yayi baranta, yayi koyo ya karbi taimakonsa har ya zama abin da ake baiyana sa a yau.

Tarbiyarsa, karantarwasa da taimakonsa sun baiwa Sokoto da Sakkwatawa daraja da kima da dauka ka tun daga 1999 zuwa abin da ake Kwatance na soyayya.

Matasa su daina komawa yan kore, ko makamin cin zarafi da wulakanta wasu saboda cimma burin wasu dabam.

Allah Yayi mana mafita ya agaje mu ga shiga tarkon 'yan hawu!

- Yusuf Dingyadi

Nura Aminu Dalhatu
Bafarawa Media Aide
20th December, 2025

Fuska mai kwarjini da haiba da daraja da kima ga sakkwatawa.“Sakkwatawa bazasu taba mantawa da Alhairin da shubka zuwa g...
17/11/2025

Fuska mai kwarjini da haiba da daraja da kima ga sakkwatawa.

“Sakkwatawa bazasu taba mantawa da Alhairin da shubka zuwa garesu ba a lokacin mulkinka, kazama Uba garesu kuma Dattijo wanda yansan kimarsu.

“Godiya marar adadi ga mahaliccin samai da kassai da dukkan bayinsa da haliltunsa akan ni’imomin da kayiwa wannan Bawan Allah (Garkuwan sokoto) Alh Dr. Attahiru Bafarawa, wanda kaikadai adda sanin yawan ni’imomin.

Yadda ka’ni’imtashi anan duniya ta hanyoyi dabam dabam Allah ka ni’imtashi a ranar gobe kiyama ka ceceshi tare da zuri’arsa ranar da kowa ke neman cetonka tare da sauran Al’ummar musulmi baki daya.

Copied
Nura Aminu Dalhatu
Bafarawa Media Aide
17th November 2025

Rabe-raben ’Yan Siyasa (A cewar Bafarawa): “Akwai ‘yan siyasar kwangila, akwai ‘yan siyasar maula, akwai ‘yan siyasar ne...
21/09/2025

Rabe-raben ’Yan Siyasa
(A cewar Bafarawa):

“Akwai ‘yan siyasar kwangila, akwai ‘yan siyasar maula, akwai ‘yan siyasar neman mukami!”

Bafarawa ya fadi wannan ranar 18 ga watan September, 2025 a gaban dandazon magoya bayansa da s**a je domin yi mishi Barka da zuwa ta aziyar rasuwar wani makusancinsa ( Alhaji Kasimu Ummarun Kobo )

Fashin Baki

Sadiq Abba Abubakar Jr.
Saturday, September 20 2025

Yan siyasar kwangila: Wadanda ke shiga siyasa domin samun kwangiloli da amfanin kansu.

Yan siyasar maula: Wadanda ba sa da akida ko manufa, sai dai su jira a ba su.

Yan siyasar neman mukami: Wadanda ke shiga siyasa ba don wata hidima ba, sai kawai su samu wani mukami ko matsayi.

Sauyin sheka da rashin akida .

Bafarawa ya bayyana cewa:
Lokacin da yake mulki, wadannan mutane sun kasance tare da shi.
Da ya sauka, sai s**a koma wurin Wamakko.
Bayan Wamakko ya sauka, sai s**a koma wurin Tambuwal.
Yanzu da Tambuwal ya sauka, sun koma wurin Wamakko.

Wannan yana nuni da cewa wadannan mutane ba sa da cikakken biyayya ko akida, sai dai su bi wanda ke mulki a lokacin domin amfana.

“ Sakkwato ta Bello maida kasari zuma”

Wannan karin magana ana iya fassarashi da zance mai kyau ana kuma iya fasarashi da zance maras kyau .

Ana iya cewa:
Sakkwato tana da tarihinta na siyasa da sauya al’amari wato, ta iya juya duk wani yanayi ko matsala zuwa daga hagu zuwa dama domin biyan bukata .

Ko a nan, ana iya fassara hakan cewa ko da halin siyasa ya dagule, akwai fatan cewa za a iya gyara ta hanyar samun shugabanni na gari da ’yan siyasa masu kishin kasa.

Jawabin Bafarawa wani kira ne na fargaba da damuwa, musamman game da yadda siyasa ke tafiya a Jihar Sakkwato. Yana jaddada cewa siyasa ya kamata ta dogara da manufa da kishin kasa, ba son rai ko bin wanda ke da iko kawai ba.

Bai kamata Siyasa ta ci gaba da Kasancewa hanyar neman riba, mukami ko maula ba. Kuma hakan yana iya janyo ci baya a jihar da kasa baki daya.

Allah ya kyauta

“DALIBBAN MAKARANTAR ALHUDA COLLAGE OF NURSING SOKOTO WADANDA S**A FITO DAGA KARAMAR HUKUMAR ISA DA SABON BIRNI SUN SAMU...
18/09/2025

“DALIBBAN MAKARANTAR ALHUDA COLLAGE OF NURSING SOKOTO WADANDA S**A FITO DAGA KARAMAR HUKUMAR ISA DA SABON BIRNI SUN SAMU TAIMAKON TALLAFIN BIYAN KUDIN MAKARANTA HAR NAIRA 14,478,500.00 DAGA (GARKUWAN SOKOTO) ALH ATTAHIRU DALHATU BAFARAWA.

Ziyarar wadda matasan s**a kawo sunkawo ne domin su nuna jindadinsu akan wannan Babban taimakon da tsohon gwamna Bafarawa yayimusu tareda nemansa da yabari sudauki hoto su aje domin tarihi domin wata rana da zatazo Bayan kammala karatunsu su nuna godiyarsu ga Allah akan wannan dawainiyar da babansu kuma mai kaunarsu yayimusu.

Akan hakane s**azo su nuna jindadinsu da farin cikinsu afili garesa tareda yimasa kyakkyawar addu’a yadda yayimusu don inganta rayuwarsu Allah ya inganta rayuwar iyalansa haka, ya kuma karamasa lafiya da yawancin rai mai albarka da har yan’baya garesu zasuci moriyar Wannan bawan Allah (Garkuwan sokoto).

Muna rokon Allah da yabashi Aljanna firdausi tareda iyalansa da sauran Al’ummar musulmi akan yadda yake taimakon Al’ummar jahar sokoto Amin.

Copied
Nura Aminu Dalhatu

Allah sarki duniya Allah yajikanka da rahama yasa mutuwa tazama hutawa a gareka Ameen Alh kasimu Ummarun kwabbo. (Dangal...
13/09/2025

Allah sarki duniya Allah yajikanka da rahama yasa mutuwa tazama hutawa a gareka Ameen Alh kasimu Ummarun kwabbo. (Dangaladiman jarma).

Copied
Nura Aminu Dalhatu

BAFARAWA TSOHON GWAMNAN JIHAR SOKOTO YA JAGORANCI KADAMARDA KUNGIYAR AREWA COHESION A JIHAR KADUNA TAREDA WAKILLAN JIHOH...
10/07/2025

BAFARAWA TSOHON GWAMNAN JIHAR SOKOTO YA JAGORANCI KADAMARDA KUNGIYAR AREWA COHESION A JIHAR KADUNA TAREDA WAKILLAN JIHOHIN 19 DAKE AREWACIN KASAR.

An kaddamar da ƙungiyar Arewa Cohesion, wata sabuwar ƙungiya mai rajin haɗin kai da farfaɗo da tattalin arziki da tsaro a Arewacin Najeriya, karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa (Garkuwan sokoto).

Taron ƙaddamarwar na gudana ne a dakin taro na Arewa House da ke Jihar Kaduna.

Manufar ƙungiyar Arewa Cohesion shi ne kawo sauyi ta hanyar fuskantar matsalolin da s**a dabaibaye yankin Arewa, ciki har da tabarbarewar tsaro, talauci da koma-baya tattalin arziki da ke kara dagula rayuwar al’ummar yankin.

Ƙungiyar na kuma da nufin haɗa kan ’yan Arewa don fitar da hanyoyin warware waɗannan matsaloli ta hanyar haɗin gwiwar jiga-jigai, masana, matasa da sauran masu ruwa da tsaki.

Copied
Nura Aminu Dalhatu
Bafarawa Media Aide

Bafarawa Akida ta gudanarda taron masu ruwa da tsaki na magoya Bayan tsohon gwamnan jihar sokoto Alh Alhaji Attahiru Dal...
18/05/2025

Bafarawa Akida ta gudanarda taron masu ruwa da tsaki na magoya Bayan tsohon gwamnan jihar sokoto Alh Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa (Garkuwan Sokoto) a gidan shugaba Prof. Hamza Maishanu Yabo.

Taron wanda aka tattauna wasu batutuwa masu muhimanci da shuka shafi akidar siyasar Bafarawa domin ci cigaba da jadadda goyon Bayan ga Babban jagoran mu Garkuwan sokoto Alh Attahiru Dalhatu Bafarawa.

Taron wanda yasamu halartar Shugaban tafiyar magoya Bayan Bafarawa Prof Hamza Maishanu, Da mataimakinsa Alh Musa maiyadi, da Hon Sani Naguru, Alh Ahmad gerafshi, Alh kasimu Umarun kwabbo da wasu daga cikin co-ordinators na kananan hukumomin sokoto north, da south, da kuma wamakko, kware, da Gwadabawa, da sauran magoya baya.

An tattauna abubuwa masu muhimanci da shuka shafi tafiyar da cigaban tafiyar sauran bayannai nanan zuwa insha Allah.

Copied
Nura Aminu Dalhatu

Tsohon Dantakarar mataimakin gwamnan jihar sokoto HE. Sagir Attahiru Bafarawa yakai gaisuwar ta’aziyar rasuwar marigayiy...
25/04/2025

Tsohon Dantakarar mataimakin gwamnan jihar sokoto HE. Sagir Attahiru Bafarawa yakai gaisuwar ta’aziyar rasuwar marigayiya Maryam Umarun kwabo diyar jarman sokoto Alh Umarun kwabbo AA dake shiyar Polo club.

HE. Sagir Bafarawa yagabatarda ta’aziyarsa ga babansa Alh umarun kwabo AA jarman sokoto tareda rokon Allah yajikan Maryam da rahama yasa mutuwa tazama hutawa a gareta Amin.

Copied
Nura Aminu Dalhatu

GAYYATA GAYYATA GAYYATA………Amadadin lyalin Gidan Alhaji Kasimu Ummarun Kwabo A A (Dan Galadiman Jarman Sokoto ) Dana Alha...
24/04/2025

GAYYATA GAYYATA GAYYATA………

Amadadin lyalin Gidan Alhaji Kasimu Ummarun Kwabo A A (Dan Galadiman Jarman Sokoto ) Dana Alhaji Abdulkadir Kofar Marke Dukkansu Suna farin Cikin Gayyatar Yan' Uwa Masoyya da Abukkan Arziki Zuwa Wajen Addu ar Daurin Auren Ya’yansu kamar:-

Fatima Kasimu Ummarun Kwabo A A da Mubarak Abdulkadir Kofar Marke wanda za’ayi Kamar haka:.

Wuri Amasallacin Jumu’a na Abu Hurera Dake Kofar Gidan Alhaji Ummarun Kwabo A A Jarman Sokoto.

Ranar Jumua 25 ga Watan April 2025 Lokaci Bayan kammala sallar jumu’a

Nura Aminu Dalhatu
Bafarawa Media Aide
20th April, 2025

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Gada/Gonronyo Hon Comr Bashir Gorau yakai gaisuwar ta’aziyar rasuwar yar uwar tsohon ...
19/04/2025

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Gada/Gonronyo Hon Comr Bashir Gorau yakai gaisuwar ta’aziyar rasuwar yar uwar tsohon gwamnan sokoto Alh Attahiru Bafarawa Garkuwan sokoto da kuma P.A nashi Alh Ahmad yahaya da Allah yayimusu rasuwa.

Hon Bashir Gorau yana tareda rakkiyar Shugaban matasa na jam’iyyar PDP Alh Mustapha Binji, Dangaskiya, da shateeman goronyo.

Comr Bashin Gorau yamika ta’aziyarsa ga Garkuwan sokoto tareda rokon Allah yajikan su da rahama yasa mutuwa tazama hutawa agaresu Amin.

Copied
Nura Aminu Dalhatu

“Bafarawa Akida Wamakko local goverment karkashin jagorancin Majidadin Bafarawa Alh Ahmad gerafshi sunkawowa Garkuwan so...
16/04/2025

“Bafarawa Akida Wamakko local goverment karkashin jagorancin Majidadin Bafarawa Alh Ahmad gerafshi sunkawowa Garkuwan sokoto ziyara ta’aziya rasuwar yar’uwarsa da kuma Babban P.A nashi Ahmad yahaya dada.

Garkuwan sokoto wanda tun Bayan dawowarsa daga kasa maitsarki yake karbar Al’umma daban daban daga cikin garin sokoto da kananan hukumomi garin domin yin ta’aziya ga yar’uwarsa da kuma P.A nashi.

Anyi addu’oin masu yawa domin samun nasara awajen ubangijin Muna rokon Allah yakara sanyaya haske acikin kabarinsu Amin.

Nura Aminu Dalhatu
Bafarawa Media Aide
16th April, 2025

Address

Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bafarawa Akida Sokoto North Local Govt posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share