Suleja emirate council

Suleja emirate council Dont say anything unless you have a reason

25/07/2026

Great news for Argentine's 👀

25/07/2026
25/07/2026

🚨 STATEMENT ISSUED 🚨

They've been forced to speak out.

25/07/2026

Hold your World Cup my boy

17/07/2025

KISSA!!!

A zamanin khalifa Umar dan Khattaab, wasu mutane uku s**a zo masa suna rike da wani saurayi s**a ce, Ya Amiral muminina! Wannan mutum ya kashe mana mahaifin mu.

Umar: kai don me ka kashe musu uba?

Saurayi: Ni makiyayi ne, rakumata ce ta ci itaciyar gonar mahaifin su, sai mahaifin su ya bugi rakumin da dutsi, rakuma ta mutu, ni kuma na É—auki dutsin na buge shi ya mutu.

Umar: saboda haka zan tsaida haddi akanka.

SAURAYI: ka saurara mini kwana uku, mahaifina ya mutu ya barni da kanwata da kuma dukiya, idan ka kasheni dukiyar da yar'uwata zasu tozarta Kamini Uzuri naje na raba Dukiyar.

Umar: wa zai lamunceka?

Saurayi ya duba cikin mutane sai ya nuna Sahabi "Abu Dhar".

Umar: ka lamunce masa Ya Aba Dharr?

Abu Dharri: na'am

Umar: ba ka san mutum ba ka lamunce, to idan ya gudu haddi zai koma kanka.

Abu Dharr: na yarda.

Saurayi ya tafi, aka kwana biyu, an shiga na so uku, saurayi bai zo ba,

Hankalin kowa ya tashi akan Abu Dharri kar haddi ya koma kansa.

Kafin sallar magariba sai ga saurayi ya zo a gajiye, ya tsaya a gaban khalifa Umar.

Saurayi: na mika dukiyar ga kawuna yanzu ina hanunka, ka tsaida haddi
akaina.

Cikin mamaki Umar ya ce: me ya dawo da kai bayan ka sami dama da za ka
iya gudu abinka?

Saurayi: na ji tsoro, Kar a ce cika alkawari ya Kare cikin mutane.

Umar ya juya ga Abu Dharr: me ya sa ka lamunce masa?

Abu Dharr: na ji tsoro, kar a ce alheri ya Kare cikin mutane.

Wannan jawabi ya yi tasiri ga masu Neman jinin ubansu, s**a ce sun yafewa
saurayi.

Umar: don me?

S**a ce: muna tsoro, kar a ce afuwa ta Kare a cikin mutane.

Ni ma na isar muku da wannan labari ne don ina tsoron kar a ce kira/tunatarwa zuwaga aikata alkhairi (wato da'awa) ya Kare cikin mutane. Don Allah kai ma ka tura kar ace yada alheri ya qare cikin mutane.

Allah Kaji Kan Malamanmu da sauran yan'uwan mu da s**a Rigamu Gidan Gaskiya, Allah yasa aljannah ce mahadar mu

Address

Second Gate Suleja
Suleja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Suleja emirate council posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share