Kanawa Post News

  • Home
  • Kanawa Post News

Kanawa Post News jaridar ta daya a arewa

Manya Yan siyasar Arewa sun shiga tattaunawa gabanin zaben 2027.Ana gudanar da wani taro na manyan ‘yan siyasar APC daga...
02/09/2026

Manya Yan siyasar Arewa sun shiga tattaunawa gabanin zaben 2027.

Ana gudanar da wani taro na manyan ‘yan siyasar APC daga Arewa, inda mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari, da mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA),Malam Nuhu Ribadu, sun halarci Zaman.

Sauran ‘yan siyasar Arewa da s**a halarci taron sun haɗa da Sanata Wamakko, Shugaban NDLEA, Buba Marwa, tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, tsohon Gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, da tsohon Gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar, da wasu da dama.

HOTUNA: Yadda aka yi ƙone-ƙone bayan rikici ya ɓarke a yankin Ikola da ke Alimosho a Jihar Legas inda aka samu asarar ra...
29/08/2026

HOTUNA: Yadda aka yi ƙone-ƙone bayan rikici ya ɓarke a yankin Ikola da ke Alimosho a Jihar Legas inda aka samu asarar rayuka da dukiyoyi mai yawa.

Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun tare wani direban Keke NAPEP tare da neman ya biya Naira 200 inda bayan ya ƙi biya s**a ƙwace masa keken, lamarin da ya janyo ya kira wasu mutane, inda daga bisani taƙaddamar ta ƙazance ta kai ka kashe-kashe da ƙone-ƙone,

Saudiyya ta kori wasu ƴan ƙasashen waje 3 bisa yin haya da motocin kan su ba tare da lasisi baHukumar Kula da Sufuri ta ...
19/08/2026

Saudiyya ta kori wasu ƴan ƙasashen waje 3 bisa yin haya da motocin kan su ba tare da lasisi ba

Hukumar Kula da Sufuri ta ƙasar Saudiyya (TGA) ta sanar da korar wasu ƴan kasashen waje uku daga kasar, bayan da aka same su da laifin yin haya da motocin da ba na haya ba kuma ba tare da lasisin yin hakan ba.

Hukumar ta ce an kuma ci tarar su ukun jimillar Riyal dubu 35,000 na Saudiyya.

Biyu daga cikin wadanda aka k**a, ɗaya ɗan ƙasar Egypt da ɗan ƙasar Indiya, an same su da laifin jigilar fasinjoji da motocin kansu ba tare da samun lasisin da ya dace ba.

An ci tarar kowannensu Riyal 12,000, tare da bayar da umarnin ficewa daga Saudiyya.

Shi kuwa mutum na uku, dan kasar Chadi, an ci shi tarar Riyal 11,000, sannan aka bayar da umarnin korarsa daga kasar.

A cewar Hukumar TGA, laifin da dan Chadin ya aikata shi ne yana shirin ɗaukar fasinjoji da motarsa ba tare da lasisi ba.

Hukumar ta jaddada cewa gudanar da ayyukan jigilar fasinjoji ba tare da lasisin da ake bukata ba, ya saba wa dokokin Saudiyya.

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta k**a Fitaccen fuska a kafafen sada zumunta da hannu a har...
19/08/2026

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta k**a Fitaccen fuska a kafafen sada zumunta da hannu a harkar safarar hodar iblis.

Kafin ranar Talata da tsakar rana, Afolabi Kazeem Micheal, wanda aka fi sani da ‘KayCee Luxury’, ya kasance wani fitaccen attajirin da ya shahara wajen nuna tarin kayayyakin alatu masu tsada a kafafen sada zumunta.

Ya kasance ɗaya daga cikin matasan attajiran Legas da ake iya auna arzikinsu ta hanyar yawan motocin da ke cikin garejinsu, ya shahara wajen saka riguna masu tsada musamman a shafukan Snapchat da ke nuna tafiye-tafiyensa zuwa Paris da Milan domin ci gaba da sayen kayan alatu.

Wannan salon rayuwa ya jawo masa dimbin masoya da masu sha’awar abin da yake wallafawa a sassan shafukan TikTok da Instagram.

Sai dai daga bisani, Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta bayyana shi ga duniya, inda ake zargin yana da alaƙa da kilogram 184.5 na hodar iblis (co***ne).

Hukumar ta bayyana cewa wannan samamen shi ne mafi girman k**a hodar iblis da aka taɓa yi daga hannun wani kamfanin aika kaya (courier company) a tarihin hukumar.

HOTUNA: Yadda Ma’aikatar Kasa da Safiyo ta yi rusau a wani wurin sayar da kayan marmari da ke kan titin Ahmadu Bello kus...
10/08/2026

HOTUNA: Yadda Ma’aikatar Kasa da Safiyo ta yi rusau a wani wurin sayar da kayan marmari da ke kan titin Ahmadu Bello kusa da Kano State Library.

Hoto: Facebook/Premier Radio 102.7

Hotunan Yanda Yan Majalisar Dokoki s**a yiwa Firayi Ministan Kasar Kosovo Ature da Kwai,yayin Da ya je Majalisar Don sha...
08/08/2026

Hotunan Yanda Yan Majalisar Dokoki s**a yiwa Firayi Ministan Kasar Kosovo Ature da Kwai,yayin Da ya je Majalisar Don shaida Zaben Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Kasar,inda ya Hadu da Fushin Yan Majalisar Ƙasar S**a Masa Jifan Shaidan Da Kwai.

Me zaku ce?

Daga Saifullahi Lawal Imam.

ICPC ta bankado wasu sabbin hukumomin bogi guda biyu yayin binciken PFIPCHukumar yaki da ayyukan rashawa a Nijeriya ICPC...
07/08/2026

ICPC ta bankado wasu sabbin hukumomin bogi guda biyu yayin binciken PFIPC

Hukumar yaki da ayyukan rashawa a Nijeriya ICPC ta bankado wasu sabbin hukumomin bogi guda biyu, yayin da take bincike kan hukumar PFIPC.

Shugaban hukumar ICPC Dr Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana haka, yayin da yek gabatar da rahoton bincike ga shugaban Nijeriya Bola Tinubu.

Ya kuma ce binciken nasu ya gano cewa Darakta Janar na hukumar bogi ta PFIPC Prince Adeyemi Adeniyi ne ya kirkiri sabbin hukumomin.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ganawar ƙarshe da gawar Mawaƙi Kosan Waƙa
02/08/2026

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ganawar ƙarshe da gawar Mawaƙi Kosan Waƙa

Hotuna: Gwamnatin jihar Kwara ta kammala tituna masu tsawon kilo mita 234.99Gwamna AbdulRahman Ya Ce Gina Hanyoyi Na Haɗ...
02/08/2026

Hotuna: Gwamnatin jihar Kwara ta kammala tituna masu tsawon kilo mita 234.99

Gwamna AbdulRahman Ya Ce Gina Hanyoyi Na Haɗa Jama'a Da Damar Ci Gaba

Gwamnatin Jihar Kwara ta ce tana ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan gine-ginen hanyoyi da nufin inganta sufuri, rage cunkoson ababen hawa da kuma buɗe ƙarin damar tattalin arziki ga al'ummomin jihar.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ƙarƙashin shirin Rahman Legacy Series, gwamnatin ta bayyana cewa manyan ayyuka irin su gadar sama ta General Tunde Idiagbon Flyover, da Dr. Ibrahim Sulu-Gambari (Unity) Flyover, tare da sake gina manyan hanyoyi a sassa daban-daban na jihar, sun taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga da haɗa al'ummomi da damammakin ci gaba.

Sanarwar ta ƙara da cewa an kammala gina hanyoyi masu tsawon kilomita 357.19, yayin da ake ci gaba da aikin wasu hanyoyi masu tsawon kilomita 234.99. Haka kuma, an aiwatar da fiye da ayyukan hanyoyi 160 na interlocking a faɗin jihar.

A cewar gwamnatin, waɗannan ayyukan sun sa ababen more rayuwa s**a zama muhimmin ginshiƙi na bunƙasa tattalin arziki da ci gaban al'umma a Jihar Kwara.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa manufar gwamnatin ba wai gina hanyoyi don sauƙaƙa zirga-zirga kaɗai ba ce, illa dai haɗa jama'a da damammakin rayuwa da ci gaba.

Kotu ta yanke wa wata budurwa hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan Yari saboda yanke al'aurar saurayinta a EkitiBabbar...
01/08/2026

Kotu ta yanke wa wata budurwa hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan Yari saboda yanke al'aurar saurayinta a Ekiti

Babbar kotun jihar Ekiti da ke zamanta a Ado-Ekiti ta yanke wa wata mata mai suna Joy Ikoja mai shekaru 35 hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari bayan samunta da laifin yanke gaban saurayinta, Ibrahim Usman.

An gurfanar da Ikoja ne kan tuhume-tuhume biyu da s**a hada da yunkurin kisa da kuma haddasa munanan raunuka, bayan wani rikici da ya faru a ranar 12 ga Afrilu, 2025.

Kotun ta ji cewa Ikoja ta k**a saurayinta tare da wata kawarta a daki, lamarin da ya haddasa rikici inda ake zarginta da murde masa al'aura, wanda ya janyo masa mummunan rauni har aka garzaya da shi asibiti domin ceto rayuwarsa.

A yayin shari'ar, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu hudu da hujjoji da s**a hada da rahoton likita da bayanan binciken 'yan sanda. Sai dai wacce ake tuhuma ta musanta aikata laifin tare da cewa ba ta jikkata saurayin nata ba.

A hukuncin da Mai Shari'a Oyinkansola Oluboyede ta yanke, kotun ta wanke Ikoja daga zargin yunkurin kisa saboda rashin isassun hujjojin da ke nuna niyyar kashe wanda abin ya shafa. Sai dai kotun ta same ta da laifin haddasa munanan raunuka, tare da yanke mata hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari.

Address

Zoo Road

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kanawa Post News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Kanawa Post News:

Shortcuts

  • Want your organization to be the top-listed Government Service?

Share