Yanmaulu Town

Yanmaulu Town Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Yanmaulu Town, Public & Government Service, Yan Molo.

23/06/2025

Alhamdu Lillah.

Yau Litinin, 27 ga watan Dhul-Hijjah, 1446 AH.

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Yan uwa, da fatan mun tashi lafiya. Allah Ya ba marasa lafiya lafiya, Ya tsare mu daga sharri, kuma Ya azurta mu da alkhairan da ke cikin wannan rana. Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.

Ina yi wa kaina da ku nasiha ‘yan’uwa akan yawaita fadin wannan azkar mai girma:

"Laa ilaaha illallaahu wahdahu laa sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wahuwa ‘ala kulli shay’in qadeer."

Muyi ƙoƙari mu karanta wannan azkar aƙalla sau 100 kafin rana ta faɗi, domin tana ɗauke da tarin falaloli da lada mai yawa.

Allah Ya ba mu ikon aikata alkhairan da ke cikin wannan rana.
Ameen.

27 Dhul-Hijjah, 1446 AH

26/05/2025

Alhamdulillah! Ruwan sama na sauka a yau. Rahamar Allah ta sauko. Allah Ka sa ya zamo alheri garemu gaba ɗaya.”

20/05/2025

Al'ummar garin Yanmaulu mai martaba Sarkin Daura yana baku shawara. 😆

ILIYA MANTAU DA LAIFUFFUKANSA GA AL’UMMAR YANMAULUDaga cikin manyan zarge-zargen da al’ummarmu ke yi wa Iliya Mantau, ts...
20/05/2025

ILIYA MANTAU DA LAIFUFFUKANSA GA AL’UMMAR YANMAULU

Daga cikin manyan zarge-zargen da al’ummarmu ke yi wa Iliya Mantau, tsohon Wakilin Hakimin Yanmaulu, kuma tsohon Dagacin Mantau, akwai abubuwan da suke girgiza hankali:

Garkuwa da mutane tare da karɓar kuɗin fansa.

Kwace wa talakawa gidaje, gonaki da filaye ba tare da doka ba.

Zinace- zinace da kuma goyon baya ga karuwai Yan Gala.

Sihirce-sihirce domin tsoratar da bayin Allah.

Yin shari’a da cin-tara ga mutane ba bisa doka ba, ya maida kanshi kamar shine Alkali.

Hadin baki da Barayi kamar yadda mutane s**a dade suna zargin yana da hannu a ciki.

Wannan azzalumi ya dade yana mulkar jama’a da danniya da zalunci. Amma Allah baya barin zalunci ya ci gaba da cin karensa ba tare da babbaka ba.

Alhamdulillah! Sarkin Daura ya tabbatar da korarsa daga matsayin wakilin Hakimi, sannan kuma an koreshi daga yankin kasar Daura gaba ɗaya.

Wannan nasara ce ga al’umma, kuma muna roƙon Allah Ya tabbatar da hukuncin gaskiya a kansa har sai an tabbatar da adalci.

Zalunci yana da ƙarshe, kuma wannan ƙarshe ya fara bayyanuwa.

© Yanmaulu Town

Address

Yan Molo

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yanmaulu Town posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share