11/03/2026
SANARWAR MANEMA LABARAI
Yunkurin Tabbatar da Tsaron Abinci: Shugaban UBRBDA Ya Nuna Shirin Aikin Ban-Ruwa na Geriyo Domin Tallafawa Manufar Renewed Hope ta Shugaba Tinubu
Yola, Jihar Adamawa | 11 ga Maris, 2026
A kokarin kara inganta tsaron abinci a karkashin manufar Renewed Hope ta Shugaban Najeriya, Asiwaju Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Manajan Darakta/ Babban Jami’in Gudanarwa na Upper Benue River Basin Development Authority, Amb. Dr. Mahmud Sanusi Mohammed, a ranar Talata ya jagoranci mambobin Correspondents Chapel Adamawa State zuwa rangadin duba shirin aikin ban-ruwa na Lake Geriyo Irrigation Project.
Ziyarar ta bai wa ‘yan jarida damar gani da idonsu matakin shirye-shiryen da aka kammala domin fara noman rani na shekarar 2025/2026, bayan jerin ayyukan fasaha da Hukumar ta aiwatar domin inganta yadda tsarin ban-ruwan ke aiki.
Da yake jawabi ga manema labarai yayin ziyarar, Dakta Mohammed ya jaddada cewa noman ban-ruwa na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.
Ya ce: "Inganta ayyukan ban-ruwa yana da matukar muhimmanci domin tabbatar da noman da ake yi duk shekara. Abubuwan da muke aiwatarwa a Geriyo suna daidai da burin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karfafa tsaron abinci a karkashin Renewed Hope Agenda.”
A cikin shirye-shiryen fara kakar noman rani, Hukumar ta gudanar da aikin cire laka da yashi (sediment) a wasu muhimman sassan Kogin Benue, tare da tsabtace manyan da kananan magudanan ruwa na ban-ruwa da kuma cire ciyayi masu hana ruwa gudana waɗanda s**a toshe hanyoyin shigar ruwa zuwa tsarin ban-ruwan.
Hakazalika, MD/CEO ya nuna sabbin injinan famfon ruwa da aka girka a aikin, waɗanda za su taimaka wajen inganta yadda ake ɗebo ruwa da rarraba shi ga manoman da ke aiki a karkashin tsarin ban-ruwan.
Bugu da kari, Hukumar ta gyara hanyar shiga Geriyo ta hanyar amfani da sabuwar fasahar biotechnology wadda ke rage sharar gini tare da kare muhalli.
Dr. Mohammed ya bayyana gamsuwarsa da matakin da aka kai, yana mai cewa hadin gwiwar wadannan ayyuka; gyaran hanyar kogin, tsabtace magudanan ruwa, cire ciyayi masu hana ruwa gudana, girka sabbin injinan famfo, da kuma gyaran hanya, sun kara inganta shirin aikin ban-ruwa na Geriyo domin fara kakar noman rani.
Mambobin Correspondents Chapel sun yabawa wannan shiri, inda s**a ce ziyarar ta ba su damar gani kai tsaye irin ci gaban da aka samu a aikin ban-ruwan da kuma kokarin Hukumar wajen farfado da ayyukan ban-ruwa domin tallafawa tsaron abinci a kasa.
A cikin tawagar da s**a raka MD/CEO yayin ziyarar akwai Babban Mataimaki na Fasaha ga MD, Manajan Workshop, Manajan Aikin Ban-Ruwa na Geriyo, tare da sauran ma’aikatan fasaha na Hukumar.
Upper Benue River Basin Development Authority ta sake jaddada kudurinta na kara bunkasa ayyukan ban-ruwa, inganta sarrafa albarkatun ruwa, da kuma tallafawa noman da ake yi duk shekara a yankin kogin Benue.mm