Clicky

VOA Hausa

VOA Hausa Sashen Hausa na VOA na daya daga cikin manyan majiyoyin labarai daga Najeriya da na duk fadin duniya baki daya. An kafa sashen Hausa na Muryar Amurka ran 21 ga watan Junairu, shekara ta 1979, domin watsa labaran duniya da shirye-shirye zuwa ga Hausawa da masu jin harshen Hausa a duk fadin duniya, musamman ma yammacin Afirka kamar kasashen Nigeria, Ghana, Nijar, Chadi, Libya, Cote d’Ivoire da wasu sassan janhuriyar Benin.

Sashen Hausa na watsa sa’oi 13.5 na shirye-shirye a kowace mako, ta radiyo da yanar intanet. Sashen kuma na buga labaran gida Najeria, da sauran duniya, da bidiyon manyan labaran Afirka daga ran Litinin zuwa Juma’a akan shafinsa na intanet. Shirye-shiryen sashen sun hada da labarai masu zafi , da rahotannin wakilai daga duk fadin duniya, tattaunawa da manyan jami’an gwamnatoci, ganawa da masu fash

Sashen Hausa na watsa sa’oi 13.5 na shirye-shirye a kowace mako, ta radiyo da yanar intanet. Sashen kuma na buga labaran gida Najeria, da sauran duniya, da bidiyon manyan labaran Afirka daga ran Litinin zuwa Juma’a akan shafinsa na intanet. Shirye-shiryen sashen sun hada da labarai masu zafi , da rahotannin wakilai daga duk fadin duniya, tattaunawa da manyan jami’an gwamnatoci, ganawa da masu fash

Operating as usual

🗞 🇳🇬 A Wani matakin kara tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar, Laftanar Janaral F...
03/17/2022
Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya Ya Kira Taron Manyan Kwamandojin Kasar

🗞 🇳🇬 A Wani matakin kara tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar, Laftanar Janaral Farouk Yahaya na can na gudanar da wani gagarumin taro da baki dayan manyan kwamandojin rundunonin sojin kasar.

A Wani matakin kara tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar, Laftanar Janaral Farouk Yahaya na can na gudanar da wani gagarumin taro da baki dayan manyan kwamandojin rundunonin sojin kasar.

🎧 A cikin shirin na wannan makon mun ci gaba da nazarin matsalar yawan mace-macen aure a Jamhuriyar Nijar da hanyoyin sh...
03/17/2022
DOMIN IYALI: Nazari Kan Matsalar Yawan Mace-Macen Aure a Jamhuriyar Nijar-Kashi Na Hudu, Maris, 17, 2022

🎧 A cikin shirin na wannan makon mun ci gaba da nazarin matsalar yawan mace-macen aure a Jamhuriyar Nijar da hanyoyin shawo kan matsalar, a yau, shirin ya maida hankali kan rawar da mata ke takawa a wannan lamarin.

Shiga shafin a saurari shirin cikin sauti.

A ci gaba da nazarin matsalar yawan mace-macen aure a Jamhuriyar Nijar da hanyoyin shawo kan matsalar, a yau, shirin ya maida hankali kan rawar da mata ke takawa a wannan lamarin. Saurari tattaunawar da Souley Mummuni Barma ya jagoranta: DOMIN IYALI: Nazari Kan Matsalar Yawan Mace-Macen Aure...

🗞 🇳🇪 ‘Yan bindiga sun afka wa wata motar jigila mai dauke da fasinjoji sama da 40 akan hanyarsu ta zuwa birnin Yamai bay...
03/17/2022
‘Yan Bindiga Sun Kashe Gwamman Fasinjoji A Farmaki Da Su Ka Kai Akan Wata Motar Jigila

🗞 🇳🇪 ‘Yan bindiga sun afka wa wata motar jigila mai dauke da fasinjoji sama da 40 akan hanyarsu ta zuwa birnin Yamai bayan da suka fito daga birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, cikinsu har da ‘yan sanda uku.

‘Yan bindiga sun afka wa wata motar jigila mai dauke da fasinjoji sama da 40 akan hanyarsu ta zuwa birnin Yamai bayan da suka fito daga birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, cikinsu har da ‘yan sanda uku.

🎧 CIKI DA GASKIYA: A cikin shirin na wannan makon mun shiga yankin Mayine da ke karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, ...
03/16/2022
Ciki Da Gaskiya: Miji Ya Saka 'Yan Sanda Sun Ci Zarafin Matarsa, 14 Maris 2022

🎧 CIKI DA GASKIYA: A cikin shirin na wannan makon mun shiga yankin Mayine da ke karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, inda wata mata mai suna Lantana Isyaka ta nemi mijin ta mai suna Umaru Ibrahim Sarkin Fawa da ya sake ta don ba ta gamsu da dabi’un sa ba, don ba ciyarwa ga yawan zagi da ya ke yi ma ta, don haka ta nemi a sauwake ma ta ta hanyar KUL’I wato ta biya mijin ladan abun da ya kashe na aure.

Shiga shafin a saurari shirin cikin sauti.

Shirin ya shiga yankin Mayine da ke karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, inda wata mata mai suna Lantana Isyaka ta nemi mijin ta mai suna Umaru Ibrahim Sarkin Fawa da ya sake ta don ba ta gamsu da dabi’un sa ba, don ba ciyarwa ga yawan zagi da ya ke yi ma ta, don haka ta nemi a sauwake ma ta...

🗞 🇳🇬 Jama'a da dama na nuni da yadda matsaloli suka yi wa kasar katutu, kama daga batun karancin man na fetur da kuma ra...
03/16/2022
Harkoki Sun Tsaya Cik Saboda Rashin Wutar Lantarki - Wasu Mazauna Legas

🗞 🇳🇬 Jama'a da dama na nuni da yadda matsaloli suka yi wa kasar katutu, kama daga batun karancin man na fetur da kuma rashin wutar lantarki. Lamarin da ya sa kanfanoni ke kukan rashin wutan lantarki da kuma tsadar man fetur dana diesel, makamashin da ake amfani da su wajen amfanin da injinan samar da hasken wutan lantarki.

Jama'a da dama na nuni da yadda matsaloli suka yi wa kasar katutu, kama daga batun karancin man na fetur da kuma rashin wutar lantarki.

🗞 🇳🇬 Kamfanoni 12 ne kawai ke aikin sarrafa wutar lantarki a kasar, bayan samun raguwar Ƙarfin wutar daga megawatts dubu...
03/16/2022
An shiga Yini Na Uku Da Katsewar Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Najeriya

🗞 🇳🇬 Kamfanoni 12 ne kawai ke aikin sarrafa wutar lantarki a kasar, bayan samun raguwar Ƙarfin wutar daga megawatts dubu 3 zuwa dubu 1,758. Akalla kwanaki uku kenan da wasu birane a Najeriya suka auka cikin duhu sakamokon lalacewar tushen wutar lantarkin kasar

Kamfanoni 12 ne kawai ke aikin sarrafa wutar lantarki a kasar, bayan samun raguwar Ƙarfin wutar daga megawatts dubu 3 zuwa dubu 1,758.

🗞 🇳🇬 Lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan sanda suka yi musayar wuta da 'yan bindigar yayin da suke kokarin kubutar da w...
03/16/2022
'Yan bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda 6 A Kebbi

🗞 🇳🇬 Lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan sanda suka yi musayar wuta da 'yan bindigar yayin da suke kokarin kubutar da wasu 'yan kasar waje a kamfanin sarrafa tumatir da ke garin Ngaski.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan sanda suka yi musayar wuta da 'yan bindigar yayin da suke kokarin kubutar da wasu 'yan kasar waje a kamfanin sarrafa tumatir da ke garin Ngaski.

03/16/2022
Ukrainian President Volodymyr Zelenskyy’s Speech to the US Congress

Jawabin Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy a gaban Majalisar Dokokin Amurka

Zelenskyy ya gabatar da makamancin wannan jawabi ta kafar bidiyo a gaban Majalisar Dokokin Birtaniya, Canada da ta Kungiyar Tarayyar Turai a ‘yan makonnin nan, inda ya yi kira ga kasashen duniya da a kai masa agaji.

#ukrainecrisis #voaukrainecrisis

🗞 🇳🇬 Jam'iyyar APC ta fitar da sanarwar kudin sayan fom Naira miliyan 20 don takarar shugaba da kuma na mataimakin shuga...
03/16/2022
APC Ta Sanya Naira Miliyan 20 Kudin Fom Na Takarar Shugabancin Jam’iyyar

🗞 🇳🇬 Jam'iyyar APC ta fitar da sanarwar kudin sayan fom Naira miliyan 20 don takarar shugaba da kuma na mataimakin shugaban jam'iyyar Naira miliyan 10. Duk sauran mukamai Naira miliyan 5.

Jam'iyyar APC ta fitar da sanarwar kudin sayan fom Naira miliyan 20 don takarar shugaba da kuma na mataimakin shugaban jam'iyyar Naira miliyan 10. Duk sauran mukamai Naira miliyan 5.

🗞 🇳🇪 Kungiyar REJEA mai fafitikar samar da ruwan sha ta shirya wani taron hadin guiwa da gidauniyar Noor ta uwargidan sh...
03/16/2022
NIJAR: Kungiyar REJEA Ta Gudanar Da Taron Nazarin Hanyoyin Samar Da Ruwan Sha A Karkara

🗞 🇳🇪 Kungiyar REJEA mai fafitikar samar da ruwan sha ta shirya wani taron hadin guiwa da gidauniyar Noor ta uwargidan shugaban kasa Hajiya Hadiza Bazoum da nufin tayar da hukumomi da masu hannu da shuni daga barci akan maganar samar da wadatar ruwan sha mai tsafta.

Kungiyar REJEA mai fafitikar samar da ruwan sha ta shirya wani taron hadin guiwa da gidauniyar Noor ta uwargidan shugaban kasa Hajiya Hadiza Bazoum da nufin tayar da hukumomi da masu hannu da shuni daga barci akan maganar samar da wadatar ruwan sha mai tsafta .

🗞 🇳🇬 A daidai lokacin da kamfanonin jiragen saman Najeriya suka yi barazanan janye aikinsu na jigilan fasinjoji a fadin ...
03/16/2022
NNPC Ta Warware Matsalar Tashin Farashin Makamashi Tsakanin ‘Yan Kasuwar Mai Da Kamfanonin Jiragen Sama

🗞 🇳🇬 A daidai lokacin da kamfanonin jiragen saman Najeriya suka yi barazanan janye aikinsu na jigilan fasinjoji a fadin kasar sakamakon tsadan makamashin tafiyar da jiragensu nan da kwanaki biyu, kamfanin NNPC tare da hadin gwiwan mataimakin kakakin majalisar wakilan kasar sun shiga tsakanin bangarorin .

A daidai lokacin da kamfanonin jiragen saman Najeriya suka yi barazanan janye aikinsu na jigilan fasinjoji a fadin kasar sakamakon tsadan makamashin tafiyar da jiragensu nan da kwanaki biyu, kamfanin NNPC tare da hadin gwiwan mataimakin kakakin majalisar wakilan kasar sun shiga tsakanin bangarorin .

🗞 🇳🇬 Rahotanni dai sun tabbatar da cewa maharan dauke da bindigogi akan babura sun aukawa ofishin ‘yan sanda na garin Na...
03/16/2022
‘Yan Bindiga Sun Hallaka DPO Da Wasu Jami’an ‘Yan Sanda A Jihar Neja

🗞 🇳🇬 Rahotanni dai sun tabbatar da cewa maharan dauke da bindigogi akan babura sun aukawa ofishin ‘yan sanda na garin Nasko hedikwatar karamar kukumar Naskon inda suka bude wuta da ya yi sanadiyyar hallaka wannan DPO na ‘yan sandan.

Wasu 'yan bindiga sun hallaka wani babban jami’in ‘yan sanda wato DPO tare da wasu jami’an tsaro guda takwas a jihar Neja dake Arewacin Najeriya.

🗞 🇳🇬 A karo na biyu cikin watanni biyu da rabi , an samu rugujewar cibiyar wutar lantarki ta kasa a Najeriya, lamarin da...
03/15/2022
Jihohi Bakwai, Birnin Tarayya Na Fama Da Matsalar Katsewar Wutar Lantarki A Najeriya

🗞 🇳🇬 A karo na biyu cikin watanni biyu da rabi , an samu rugujewar cibiyar wutar lantarki ta kasa a Najeriya, lamarin da ya jefa jihohi bakwai da babban Birnin Tarayya Abuja cikin duhu. Wannan matsala ta jawo kiraye-kiraye ga gwamnatin tarayya da ta sake duba harkar sayar da hannun jarin wutar lantarki da aka yi a kasar.

A karo na biyu cikin watanni biyu da rabi , an samu rugujewar cibiyar wutar lantarki ta kasa a Najeriya, lamarin da ya jefa jihohi bakwai da babban Birnin Tarayya Abuja cikin duhu.

🗞 🇺🇸 Jami’an Amurka sun ce mummunan harin da Rasha ta kai bangaren yammacin kasar Ukraine jiya Lahadi, kusa da kan iyaka...
03/15/2022
Harin Da Rasha Ta Kai Wa Yammacin Ukraine Bai Zo Da Mamaki Ba-Jami'an Amurka

🗞 🇺🇸 Jami’an Amurka sun ce mummunan harin da Rasha ta kai bangaren yammacin kasar Ukraine jiya Lahadi, kusa da kan iyaka da Poland, wani abu ne da suka yi tsammani.

Jami’an Amurka sun ce mummunan harin da Rasha ta kai bangaren yammacin kasar Ukraine jiya Lahadi, kusa da kan iyaka da Poland, wani abu ne da suka yi tsammani.

🎧 TSAKA MAI WUYA: A cikin shirin na wannan makon mun leka Najeriya a jihar Zamfara, jihar da take ta fama da sace-sacen ...
03/15/2022
TSAKA MAI WUYA: Mun Leka Jihar Zamfara Da Ke Fama Da Sace Sacen Mutane

🎧 TSAKA MAI WUYA: A cikin shirin na wannan makon mun leka Najeriya a jihar Zamfara, jihar da take ta fama da sace-sacen mutane musamman ‘yan makaranta a ‘yan kwanakin nan.

Shiga shafin a saurari shirin cikin sauti.

TSAKA MAI WUYA: A cikin shirin na wannan makon mun leka Najeriya a jihar Zamfara, jihar da take ta fama da sace-sacen mutane musamman ‘yan makaranta a ‘yan kwanakin nan. TSAKA MAi WUYA: Mun Leka Jihar Zamfara Da Ke Fama Da Sace Sacen Mutane

🗞 🇳🇬 Kungiyar malamaman jami’o’in Najeriya wato ASUU ta bayyana cewa ta tsawaita yajin aikin gargadi da ta fara a watan ...
03/14/2022
ASUU Ta Tsawaita Yajin Aikin Da Ta Ke Da Wata Biyu

🗞 🇳🇬 Kungiyar malamaman jami’o’in Najeriya wato ASUU ta bayyana cewa ta tsawaita yajin aikin gargadi da ta fara a watan jiya, wanda ta fara wata daya tak da ya gabata.

Kungiyar malamaman jami’o’in Najeriya wato ASUU ta bayyana cewa ta tsawaita yajin aikin gargadi da ta fara a watan jiya, wanda ta fara wata daya tak da ya gabata. Kungiyar dai ta sanar da wannan matsayin na ta ne bayan taron kolinta da ta gudanar a ofishinta da ke cikin jami’ar birnin tarayya....

🗞 🇳🇬 A jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin kasar wasu mahara sun tare hanyar garin Goronyo da ke gabashin jihar jiy...
03/14/2022
Arewacin Najeriya Na Ci Gaba Da Kokawa Kan Matsalolin Rashin Tsaro Da Suka Ki Ci Suka Ki Cinyewa

🗞 🇳🇬 A jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin kasar wasu mahara sun tare hanyar garin Goronyo da ke gabashin jihar jiya Lahadi, ranar da kasuwar garin ke ci, abin da ya kara daga hankalin jama'a, musamman duba da wani hari da suka saba kaiwa a kasuwar wanda yayi sanadin salwantar rayuka da dama.

A Najeriya matsalolin rashin tsaro na ci gaba da tayar da hankulan jama'a inda har su ka fara yanke kauna ko za su fita daga yanayin.

🗞 🇳🇬 Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana wa maigidansa shugaba Buhari aniyarsa ta tsayawa tak...
03/14/2022
Osinbajo Ya Fada Ma Shugaba Buhari Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Shugabancin Najeriya

🗞 🇳🇬 Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana wa maigidansa shugaba Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a kakar zaben shekara 2023 mai karatowa, domin ya karasa aikin alkhairin da suka fara tun shekara 2015 da suka dare kan karagar mulki.

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana wa maigidansa shugaba Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a kakar zaben shekara 2023 mai karatowa, domin ya karasa aikin alkhairin da suka fara tun shekara 2015 da suka dare kan karagar mulki. Wannan fitowa fili da...

🗞 🇳🇪 A yayin da hukumomin Nijer suka ayyana shirin gabatar wa majalisar dokokin kasa bukatar samun hadin kanta wajen gir...
03/14/2022
Faransa Ta Fasa Girke Dakarun Barkhane A Nijer A Cewar Kwamandan Rundunar

🗞 🇳🇪 A yayin da hukumomin Nijer suka ayyana shirin gabatar wa majalisar dokokin kasa bukatar samun hadin kanta wajen girke dakarun rundunar Barkhane a kasar bayan ficewar rundunar daga Mali, kwamandan rundunar ta kasar Faransa ya ce kai tsaye zasu koma gida a maimakon zuwa wata kasar waje.

A yayin da hukumomin Nijer suka ayyana shirin gabatar wa majalisar dokokin kasa bukatar samun hadin kanta wajen girke dakarun rundunar Barkhane a kasar bayan ficewar rundunar daga Mali, kwamandan rundunar ta kasar Faransa ya ce kai tsaye zasu koma gida a maimakon zuwa wata kasar waje.

🎧 A BARI YA HUCE: A cikin shirin na wannan makon mun karrama marigayi Gremah Boucar, shugaban gidan Radio da Talabijin n...
03/14/2022
A BARI YA HUCE: Karrama Marigayi Gremah Boucar- Maris, 12, 2022

🎧 A BARI YA HUCE: A cikin shirin na wannan makon mun karrama marigayi Gremah Boucar, shugaban gidan Radio da Talabijin na Amfani a Jamhuriyar Nijar, daya daga cikin tashohi masu zaman kansu na farko da suka kulla yajejeniyar aiki da Muryar Amurka.

Shiga shafin a saurari shirin cikin sauti.

A shirin A Bari Ya Huce na wannan makon mun karrama marigayi Gremah Boucar, shugaban gidan Radio da Talabijin na Amfani a Jamhuriyar Nijar, daya daga cikin tashohi masu zaman kansu na farko da suka kulla yajejeniyar aiki da Muryar Amurka. Saurari cikakken shirin ka ji tarihin marigayi Grema...

🗞 🇳🇬 Matasa da su ka yi gwagwarmayar amincewa da dokar rage shekarun tsayawa takara, sun jaddada fatar cewa shugaba Buha...
03/14/2022
Matasa Sun Lashi Takobin Karbe Shugabancin Najeriya A Zaben 2023

🗞 🇳🇬 Matasa da su ka yi gwagwarmayar amincewa da dokar rage shekarun tsayawa takara, sun jaddada fatar cewa shugaba Buhari zai cika mu su alkawarin da ya yi a lokacin sanya hannu kan dokar na mika mu su ragamar mulki a 2023.

Matasa da su ka yi gwagwarmayar amincewa da dokar rage shekarun tsayawa takara, sun jaddada fatar cewa shugaba Buhari zai cika mu su alkawarin da ya yi a lokacin sanya hannu kan dokar na mika mu su ragamar mulki a 2023.

🗞 🇳🇬 Muhawarar mulkin karba-karba tsakanin arewa da kudu ba ta yi sanyi ba musamman tsakanin ‘yan manyan jam’iyyu biyu n...
03/14/2022
Najeriya: Da Alamar Arewa Na Kokarin Kaucewa Tsarin Mulkin Karba-Karba

🗞 🇳🇬 Muhawarar mulkin karba-karba tsakanin arewa da kudu ba ta yi sanyi ba musamman tsakanin ‘yan manyan jam’iyyu biyu na APC da PDP. Tuni jam’iyyar APC ta nuna alkibilar ta ta tura takarar kudu, biyo bayan ayyana wanda zai zama shugaban jam’iyya zai fito ne daga arewa ta tsakiya.

Muhawarar mulkin karba-karba tsakanin arewa da kudu ba ta yi sanyi ba musamman tsakanin ‘yan manyan jam’iyyu biyu na APC da PDP. Tuni jam’iyyar APC ta nuna alkibilar ta ta tura takarar kudu, biyo bayan ayyana wanda zai zama shugaban jam’iyya zai fito ne daga arewa ta tsakiya.

🎧 DUNIYAR AMURKA: A cikin shirin na wannan makon mun tabo batun tallafin biliyoyin daloli da Amurka za ta bai wa Ukraine...
03/14/2022
DUNIYAR AMURKA: Amurka Za Ta Tallafawa Ukraine Da Biliyoyin Daloli, Maris 11, 2022

🎧 DUNIYAR AMURKA: A cikin shirin na wannan makon mun tabo batun tallafin biliyoyin daloli da Amurka za ta bai wa Ukraine, bayan da Majalisar Dokoki ta amince da shirin tallafin, yayin da Rasha ke ci gaba da kai mamaya sannan Ukraine ba tare da ta takale ta ba.

Shiga shafin a saurari shirin cikin sauti.

Shirin Duniyar Amurka na wannan mako ya tabo batun tallafin biliyoyin daloli da Amurka za ta bai wa Ukraine, bayan da Majalisar Dokoki ta amince da shirin tallafin, yayin da Rasha ke ci gaba da kai mamaya sannan Ukraine ba tare da ta takale ta ba.

🎧 MANUNIYA: A cikin shirin na wannan makon mun yi dubi ne akan rikichin cikin gidan Jam'iyyar APC da kuma takaddamar shu...
03/14/2022
MANUNIYA: Takaddamar Shugabancin A Jam'iyyar APC, 11 Maris, 2022

🎧 MANUNIYA: A cikin shirin na wannan makon mun yi dubi ne akan rikichin cikin gidan Jam'iyyar APC da kuma takaddamar shugabanchin kwamitin riko na Jam'iyyar APC a Kasa sai kuma maganar watsi da bukatar kwaskwarimar dokokin zabe da majalissar dattijai da sauran batutuwan siyasa.

Shiga shafin a saurari shirin ciki sauti.

Shirin Manuniya na wannan mako ya yi dubi ne akan rikichin cikin gidan Jam'iyyar APC da kuma takaddamar shugabanchin kwamitin riko na Jam'iyyar APC a Kasa sai kuma maganar watsi da bukatar kwaskwarimar dokokin zabe da majalissar dattijai da sauran batutuwan siyasa.

Address

330 INDEPENDANCE AVE SW
Washington D.C., DC
20237

Metro, VRE, MARC, Various Shuttle bus services from suburban Maryland and Northern Virginia

Telephone

(202) 203-4077

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when VOA Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to VOA Hausa:

Videos


Other Washington D.C. government services

Show All

Comments

Daga hawanshi mulki kawo YANZU ko kuna,iya tuna ko Dan,AREWA nawane yashiga matsala mulkinsa yazama annoba ga yan arewa kada Allah ya maimaita,
Start Online Part-Time Job and get paid Weekly.
Start Online Part-Time Job and get paid Weekly.
Godiya nake kuma ina muku fatan Allah ya tsare ya kara daukaka
Aslm.gabako
Aslm allatama zamanlafiya
Aslm.sashen hausa na voa,barkanmu da kwana ya aiki?Daman kira nake so ku yi kan shuwa gabannin mu na nigeria ya k**ata su san cewa lokaci fa yakusa dawowa na 'zabe'ga shi kuma talakkawan kasarmu na cikin tsadar rayuwa ta kowane fanni,ya k**ata gwamnati ta tsaya ta duba farashin kayan masa rufi da kuma maganar tsaro saboda yanzun haka wasu mahallansu sunfi karfinsu 'yan ta adda sun addabesu babu zaman lafiya.kan haka nake roko ga voa da tayi kira ga shuwa ga bannin nigeria su tashi daga barci dan allah dan darajar annabi muhammadu s.a.w.-sako daga naku m.salisu ibrahim liman gatakawa town kankara katsina state.sai naji ku
Ya sunan fir,auna?
Sunday. Sunday Sabo
SALAM VOA HAUSA,Kuban dama nai tambaya ga shugaban kasar mu Nigeria wato baba buhari,tambayata ga baba buhari wai yaushe za,a kawo karshan matsalar tsaro a arewacin kasar mu Nigeria ,kosai zaban 2023 ya gabato za,a samar da tsaro ,domin samun damar yin zabe,Allah kai mana maganin abin da yadame mu a Nigeria amin.
Aslm