2015 Kano a Bamu Mu Gyara

  • Home
  • 2015 Kano a Bamu Mu Gyara

2015 Kano a Bamu Mu Gyara Kano a bamu mu gyara,shafi ne da yake addu'ar Allah ya sa a 2015 mulkin Kano ya fada hannun dan jama'iyar ACP domin kawar da:

1. Dawo da shari'ar Allah
3.

Isgilancin da ake yiwa addini
2. Dawo da a daidaita sahu, dss.

23/03/2014

...KANO A BAMU MU GYARA A 2015...

ALLAH MUNA ROKONKA DA SUNAYENKA KYAWAWA,ALLAH KAI KE BA DA MULKI GA WANDA KAKE SO A LOKACIN DA KAKE SO.ALLAH KA BA MALAM SALHU SAGIR TAKAI GWAMNAN KANO A 2015!!!

RA'AYIN TAKAI MU KE YI,DOMIN YANA DA HALI NA GARI.

TAKAI MU KE YIWA ADDU'AR ZAMA GWAMNA,SABODA RIKON ADDININSA.

ALLAH DAN ISAR MANZON ALLAH (S.A.W.) ALLAH KA BA TAKAI GWAMNA A 2015!!!

ALLAH KA BA TAKAI GWAMNA SARDAUNA KUMA SANATA A 2015!!!
16/12/2013

ALLAH KA BA TAKAI GWAMNA SARDAUNA KUMA SANATA A 2015!!!

01/11/2013

...KITSO DA KWARKWATA...

APC jama'iya ce mai manufa da aka kafa don ceto kasarmu daga halin mulkin rashi gaskiyar da ake yi mana.Wannan ita ce babbar manufar kafa wannan jama'iya,amma yanzu naga ana neman a jawo mana mutanen da s**a saka kasarmu a halin da na fada a baya.To ku sani ba fa PDP ba ce mai laifi mutanen cikinta ne masu laifi.Kuma a lokacin da ake kokarin kafa wannan jama'iya sai da aka yadda da za a yi aiki tare ba maganar tuna baya,amma yanzu sai naga ana neman yin walakeluwa da wasu daga cikin wanda s**a sha wuya wajen kafa APC,to ku sani Allah dai baya bacci.

APC suna neman zawarcin B7 ko G7,sun manta da cewa duk tsawon shekarun da aka shafe ana yin wannan gurbataccen mulki da su aka yi.Kuma ni ina da ja a kan cewar wai suna rigima ne saboda kishi,ni dai a ganina kyashi ne ba kishi ba.Dalili a nan shi ne suna ganin sun gama mulki a jihohinsu,don haka suna neman mafita ne kawai.

Zaku yarda da ni idan na ce muku duk wanda ya ga a jiharsa ba zai samu yadda zai ja ragamar jama'iyar ba to ba zai yarda a yi tafiyar da shi ba.

Misali:
Tunda yanzu za a yi zaben kananan hukumomi a jihohin Kano da Jigawa,in har don Allah suke yi kuma don talakawa to su shigo kafin a yi zaben don suma APCn su samu shugabannin.

Don haka wallahi duk mutumin da ya bari aka hada baki da shi aka mayar da mu gidan jiya ba zamu taba yafe masa ba.

Ku sani wadannan mutane zasu iya yin kafar ungulu wajen kafa shugabanci a kasa daga baya kuma su koma PDPn su tare da tawagarsu.

Allah duk wanda ba don Allah da gyaran kasa yake yin APC ba,Allah ka yi mana waje da shi in kuma dama a wajen yake Allah ka hana shi shigowa cikinta don alfarmar ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA.

Address

GYADI-GYADI Court ROAD

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when 2015 Kano a Bamu Mu Gyara posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to 2015 Kano a Bamu Mu Gyara:

  • Want your organization to be the top-listed Government Service?

Share