03/09/2025
TWO YEARS OF TRANSFORMATIVE LEADERSHIP AND QUALITATIVE REPRESENTATION.
THANK YOU Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi
1. Tallafawa manoman rani 220 da injinan ban ruwa tare da gina musu rijiyoyin ban ruwa na zamani don habaka nomansu, a dukkan mazabu 22 na Funtua da Dandume.
2. Aikin gyaran dam na Farar Kasa domin bunkasa noman rani a Karamar Hukumar Dandume.
3. Daukar nauyin gyaran famfo na rijiyoyin burtsatse 120 a mazabu 22.
4. Tallafawa manoma da buhunan takin zamani guda 2,000 da injinan ban ruwa a shekarar 2023.
5. Ba da kyautar mota da sabbin wayoyin hannu ga matasa 'yan soshiyal midiya.
6. Rabon kartonin taliya 1,000 ga al’umma don rage radadin rayuwa a shekarar 2023.
7. Rabon littattafan rubutu 20,000 ga makarantun firamare da sakandare.
8. Daukar nauyin mata 38 zuwa makarantar koyon aikin jinya da unguwar zoma a Malumfashi – irinta na farko a tarihi.
9. Samar da ayyukan dindindin (na ofis) ga mutane fiye da 31 a matakin jiha da na tarayya.
10. Gyaran gadon asibiti da raba katifu a Asibitin Dandume.
11. Daukar nauyin matasa 50 da horas da su kan sana'o'in zamani tare da ba kowane tallafin naira 50,000.
12. Sanya fitilun masu amfani da hasken rana 100 a manyan tituna a garuruwan Funtua da Dandume.
13. Nasarar kawo Jami’ar Kiwon Lafiya a garin Funtua.
14. Nasarar kawo Jami’ar Open University (NOUN) a Funtua.
15. Gina makarantar firamare ta zamani a Maigamji.
16. Gina karin ajujuwa a makarantar sakandire ta Community a Dandume.
17. Karin ajujuwa a makarantar Mare Firamare, Dandume.
18. Nasarar samar da fili mai matsakaicin girma donyin filin jirgin sama a Funtua.
19. Tallafin fiye da naira miliyan 40 lokutan bukukuwan Sallah (Karama da Babba) na shekarun 2023, 2024 da 2025.
20. Daukar nauyin yin aiki ga masu fama da matsalolin ido a dukkan mazabu na Funtua da Dandume.
21. Tallafin murnar Maulidin Annabi (SAW) da ya kai naira miliyan 5 a 2023 da 2024.
22. Gina babbar makarantar Islamiyya a garin Maska.
23. Gina karin ajujuwa a makarantar Shehu Abubakar Alti (RA), Funtua.
24. Gabatar da kudirin dokar magance matsalolin tsaro a gaban majalisa.
25. Hadin gwiwa da jami’an tsaro a sirrance don magance matsalar masu ba da bayanan sirri (informants) a Dandume.
26. Raba kekunan guragu 100 ga masu buƙata a Funtua da Dandume.
27. Horas da matasa 20 kan sana’o’in zamani tare da ba kowane kwamfutar zamani kirar HP mai darajar naira 500,000.
28. Daukar nauyin koyar da matasa fasahar canza injin man fetur zuwa na iskar gas (LPG).
29. Tallafawa mabiya addinin Kirista a lokutan bukukuwansu na Kirsimeti.
30. Ba da tallafin naira 100,000 ga dalibai 200 na manyan makarantu – jimilla naira miliyan 20 – a shekarar 2025.
31. Daukar nauyin sayen kayan daki gaba ɗaya ga wata marainiya a mazabar Dantankari.
32. Ba da tallafi ga mutane 30 masu buƙata ta musamman a Karamar Hukumar Dandume.
33. Daukar nauyin tafsirin Alƙur’ani mai girma na Sheikh Ahmed Tijjani Dandume da Sheikh Mahmud Adam a Martaba FM, Funtua.
34. Daukar nauyin shirin Mimbarin Ma’aiki (SAW) na Sheikh Liman Abdurrahman a Martaba FM.
35. Mika kudirin kafa makarantar koyon kiwon dabbobi ta ƙasa a garin Dandume.
36. Ba da katunan ganin likita 3,000 ga marasa lafiya a Asibitin General dake Funtua.
37. Gina da sauya famfo 17 masu amfani da hasken rana.
38. Tallafa wa iyalan wadanda harin ta’addanci ya shafa a Funtua da Dandume.
39. Gabatar da roko ga Gwamna. dan
Neman amincewar gina hanya daga Kasuwar Mata Funtua zuwa Nasarawa Dandume
40. Raba babura kirar Boxer 10 ga matasa a Funtua da Dandume.
41. Tallafin kayan azumin Ramadan da ya haɗa da buhunan shinkafa 3,000, masara 320 da gero 530 a 2023.
42. Ba da kyautar fom na JAMB ga dalibai 70 na yankin Funtua da Dandume a shekarar 2024.
43. Raba buhun shinkafa 5,500 (25kg) a lokacin azumin shekarar 2025.
44. Taimakawa marayu a unguwar Musa, Funtua don biyan kuɗin haya da siyan kayan abinci.
45. Daukar nauyin shirin refresher ga daliban shekarar ƙarshe a makarantun sakandare.
46. Ba da tallafi ga makarantar sakandire ta Dandume da kuma wani tallafin don siyan fili makabarta a yankin Magaji Wando da Mahuta.
47. Sanya transfoma guda biyu – ɗaya a Funtua da ɗaya a Dandume.
48. Tallafi kai tsaye ga Islamiyyu, masallatai, marayu, majiyanta da mabukata a kowane lokaci.
49. Daukar nauyin matasa 6 zuwa Katsina don koyon sana’o’in dogaro da kai.
50. Hada guiwa da hukumar hanasha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta hanyar daukar nauyin shirin wayar da kan matasa illar shan miyagun kwayoyi a Funtua.