15/01/2023
Na fi gamsuwa da alkalancin Dr. Marzuq Ungogo
Muhawarar âYan Takarar Gwamnan Kano: Fashin Baâki
Marzuq Ungogo, PhD
Muhawarar âyan Takarar Gwamnan Kano da BBC Hausa ta shirya kuma ta gabatar a yau ta mutuâkar âkayatar. Kwalliya ta biya kuâdin sabulu domin muhawarar ta haska mana kowanne âdan takara, kaifin basirarsa, shirye-shirye da iya magana. Ga nawa fashin baqin.
1. Shaâaban Sharaâda ya nuna bajintar fahimtar matsalolin alâumma da kuma kaifin basirar fito da hanyar gyara. Tabbas zaman Shaâaban a Abuja, gwagwarmayar da ya yi a Kano, da kuma âkasashen kewaye da ya zagaya ba su zube a banza ba.
2. Salihu Tanko Yakasai: shi ma ya nuna karsashi irin na Shaâaban, wajen fitar da alâkalumma da zayyana hanyoyin gyara na zamani. Sai dai kuma kash.âŠ. Shaâaban ya yi masa fintinkau.
3. Muhammad Abacha: Biyun âdaya, ko dai Abacha bai kai sauran âyan takara shiri ba ko kuma bai kai su hikimar zance ba. Abacha bai nuna wata bajinta ba wajen fahimtar matsalar talakan Kano ba, bai nuna sanin makamar aiki ba, sannan bai nuna karsashi ba.
4. Abba Kabir Yusuf: Abba ya nuna sanin makamar aiki sai dai duk aikin da ya bayyana zai yi to ba sabon abu ba ne. Abba maganarsa yawanci a kan ci gaba da âkoâkarin Kwankwaso ne. Abba ya ci alwashin daâkile rashawa. Abba ya tafka kuskuren barin muhawara ana cikin yi. Tabbas uzurinsa a Kaduna bai kai muhawarar nan muhimmanci ba.
5. Nasir Gawuna: Ya fi kowa nuna sanin gwamnati, matsaloli da hanyoyin da an gwada su ba su âbulle ba. Abun mamaki sauran âyan takara idan s**a ce za su yi abu, Gawuna sai ya ce ai sun gwada hakan tuntuni. Gawuna dai ya nuna zai ci gaba da aiyuka ma su kyau gwamnonin Kano guda uku da s**a gabata musamman ma Ganduje. Ya kuma jaddada zai gyara kura-kuren gwamnatocin baya tun da ya sansu.
âDauraya
1. A âkwarewa da cancanta, Gawuna ya fi Abba. Sai dai ba wani abun birgewa ba ne ya yi ta maimaita zai ci gaba da aiki ko salon Ganduje.
2. Matsalar Abba dogaro da yawa a kan Kwankwaso. Tambayar shine idan s**ai faâda, ya za a yi?
3. Shaâaban na da duk abin da Salihu Tanko ke da shi. Amman Salihu shi kuma ya gaza Shaâaban.
4. Muhammad Abacha bai shirya ba.
Daga âkarshe:
Mutane za su yi iya shahada su zabi Gawuna ko Abba. Ba dole su cika alqawarin ci gaba da aikin Kwankwaso ko Ganduje ba kamar yadda s**ai alqawari. Sai dai duk su biyun su na da nagarta da kishin Kano. Akwai alamun za su yiwa alâumma aiki.
Duk wanda ya ci zaâbe ya kirawo Shaâaban da âDawisu su taimake su wajen aiki. Abacha ya je ya ci gaba da kasuwancinsa da taimakon alâumma.