Ya-Ibadeeh

Ya-Ibadeeh Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ya-Ibadeeh, Library, No. 7 Yahya madaki Way katsina, Abuja.

14/03/2025

*👉🏼Ya shafi al'amuran Addini domin musan ibadah da hukunce hukunce da Fatawoyin Malamai Masana ingantattun hadisan Fiqhu domin sanin yadda za'a bautawa Allah Musamman Mata domin amfanin kan mu.*

*Ba'a fira aciki sai darussa da fatawa,*

👇🏼
https://chat.whatsapp.com/ISjoy10h9vF1bxM3LQWEJY

Al-islam🙏🏼. 👇🏼

11/03/2025

____________
*SADQATUJJARIYA*
Ku saka taro ko sisi Ciyarwa ga mabukata tare da cibiyar *YA-IBADEEH & ELFARI FOUNDATION*
Musamman a wannan lokaci
*ASUSUN TALLAFI* 👇🏼
1-Acc. No. 6117395590
Name:- Fari Hamisu
Opay
2-Acc. No. 1000000007
Name:- Fari Hamisu
Tenn bank.
_______________________
Atayamu isar da saƙo ta hanyar turawa sauran zaurukan.
________________________
Facebook 👇🏼
https://www.facebook.com/profile.php?id=100065016631053
Community 👇🏼
https://chat.whatsapp.com/ISjoy10h9vF1bxM3LQWEJY
_____________________
*»👉🏼 YA-IBADEEH COMMUNITY*📖🕋

Library

12/02/2023

*MIJINA YANA SADUWA DANI A RANAR GIRKIN KISHIYATA*

*Tambaya:*
Asslmu alaikum Mun kasance mu biyu awajen mijinmu, Sai yakasance yar'uwata bata iya gamsar dashi, to ko ranar girkinta yakan shigo ya sadu dani da rana ko da daddare, Tambaya
anan shi ne malam shi hakan ya halasta?
Kuma idan na mishi magana ya daina zuwa bayaji, ba gidanmu daya ba, Dan Allah hukuncin hakan da mafita?

*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Ya wajaba ya nemi izininta, tunda hakkinta ne, in har ta sadaukar ya halatta ya sadu dake aranar kwananki da kwananta.

Saboda lokacin da Nana Saudah ta tsufa ta ji tsoron kada Annabi ﷺ ya saketa, ta dauki kwananta ta bawa Nana
A'isha,k**ar yadda Bukhari ya rawaito. Bayan haka Annabi ﷺ
yana yin kwana dai-dai a dakunan matansa guda bakwai, ita kuma Nana Aisha yana mata kwana biyu, Saudat kuwa baya kwana da ita, saboda ta sadaukar da hakkınta.

Ya wajaba mai gida ya guji dukkan abin da zai kawo matsala da fitintinu a tsakanin iyalansa, adalci yana tabbatar da zaman lafiya.

Allah ne mafi sani.
____________________
Amsawa;- Dr Jamilu Zarewa
________________________
*Za'a iya bibiyar darussan mu a👇🏼*

Facebook👉🏼 https://mobile.facebook.com/Ya-Ibadeeh-105630640871237.
_____________________
*»👉🏼DAGA ZAUREN YA- IBADEEH*📖🕋

12/02/2023

*_HUKUNCIN FADIN (JUMA'AT MUBARAK)_*

*Tambaya*
Assalamu Alaikum. Dr ko ya halatta Musulmi yayi wa dan'uwansa murna da zagayowar juma'a ta hanyar sako a wayar sailula k**ar ace JUMA'A KAREEM ko JUMA'A MUBARAK? Allah yaqara sani.

*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Akwai malaman da su ka hana hakan, suna ganin ba shi da asali a addini, Amma abin da yake zahiri hakan ya fi k**a da al'ada, wannan yasa haramta shi yake bukatar Nassi, tun da babin al'adu da mu'amaloli a bude yake, sai abin da sharia ta haramta. Duk Wanda yake yi ba tare da ya riya cewa ibada ba ce hana shi ko bidi'antar da aikinsa yana da wuya, k**ar yadda Ibnu Uthaimin ya yi nuni zuwa haka a fatawar da aka yi masa.

Saidai duk da haka ya k**ata kar Musulmi ya zamar da shi al-adarsa kowace juma'a, don kar wasu su fahimci ibada ne.

Allah ne mafi sani.
____________________
*Amsawa;- Dr Jamilu Zarewa*
____________________
Ku kasance damu a👇🏼
Facebook 👉🏼 https://mobile.facebook.com/Ya-Ibadeeh-105630640871237
_____________________
*»👉🏼DAGA ZAUREN YA- IBADEEH*📖

12/02/2023

*BURI NE YA YIWA ’YAN MATA YAWA, AMMA AKWAI MAZAJEN AURE*

*Prof. Mansur Ibrahim Sokoto*

Akwai mazaje ma ba miji ba, suna can buhu-buhu a gidan kallon bal. Saboda irin burin da mata su ka ci ne ya sa samarin su ka fita harkarsu su ka koma kallon ball tukuru.

Masu mutuwar zuciya daga cikin mazan su ka koma neman auren-jari. Kun ga anyi ‘balance’ ke nan. Don haka kowa sai ya ci wuya. Shi babu mata, ke kuma babu miji saboda kowa ya dauko “dala ba gammo”.

A shekarun baya, mata sun wahalar da maza a fannin soyayya. Sai a samu mace daya tana wasan-kura da samari goma kuma kowa a cikinsu so ya ke ta ce shi ta ke so ya aureta. Ita kuma tana ta wajigasu k**ar kwallon ludo.Ita dama duniya rawar ‘yan mata ce, yau kana gaba, gobe sai ka dawo baya. Ba zan manta ba, akwai wacce na sani har lissafa sunayen motocin da ake zuwa wajenta da su wajenta ta ke yi saboda buri da karya. Yadda ta dama, haka samarin s**a dinga sha amma a karshe kauye mu ka kaita.Duk irin misalan da su ke a doron kasa ba sa zama izina a wajen matan yanzu. Yawancin masu cewa sun rasa miji dinnan sun samu damar aure su ka yi wasa da ita saboda buri.

Ita dama yar talaka ta shiga uku idan tace buri, ke a suwa kuma? Bayan kin san rayuwa a gidanku. To suma ‘ya’yan masu kudin jikinsu gaya musu yake b***e kuma ke. Mai karatu tafi cikin GRA ko Abuja ka sha mamaki, sai ka samu mace ta kai shekara 40 a zaune, ta zama sanata a gidansu.

Allah na tuba, duk sanda mace ta kai 40 a gida kuma ta cigaba da jiran mai kudi ai ta samu matsalar kwakwalwa. Ahirr dinku ‘yan uwana mata, bahaushe yace “Da babu gwara ba dadi” Kuma idan hagu taki sai a koma dama.

Wannan dalilin ne yasa kuke ta bushewa, kullum a rame, cikin tunani da rashin lafiya. Ga kuma uwa da yan uwa sun sako ki gaba da maganganu na neman kau da ke. Saboda kin tare mata hanya, ga kawayenki can sai haihuwa su ke yi, sai dai idan kun hadu su baki raino ki ‘dana rainon jariri. Allah ya aurar da kowa da alheri.

Allah ta'ala yakara ganar damu.
____________________

10/02/2023

*SHIN WAJIBI NE SAI MIJIN KI YA SADU DA KE A DUKKAN ƊARE, WATO JIMA'I.*

*TAMBAYA*
Assalamu alaikum Malam Don Allah sau nawa Miji ya k**ata ya sadu da matar sa, kullum ne ko kuma a'a,domin ina samun matsala da miji na Nagode.

*AMSA*
Wa Alaikis Salaam Wa Ramatullahi Wa Barkatuhu: Toh Malamai Sun Yi Saɓani Akan Wannan Maganar. Akwai Maganganun Malamai Har Guda (4)

(1) Abu Hanifa Allah Ya Kara Yarda Gare Shi Yana Cewa Jima'i Hakkin Namiji Ne, Mace Tana da Hakkin Jima'i a Wajen Mijin ta a Rayuwar ta Sau 1 tak a Shekara, Sauran Kuma Hakkin Namiji ne Idan Ya Ga Dama Ya Sadu da ita Idan ya Ga Dama ya Bar ta a Haka. Amma Kuma Yace Namiji Yayi Abinda Ya Dace, Yayi Abinda Zai Yi Domin Zaman Auren Su Yayi Ƙyau yayi Ɗaɗi. Abinda Yake Nufi Shine Idan Mijin Ki Ya Sadu dake Sau Ɗaya a Shekara toh Ya Sauke Hakkin ki, Sauran Nashi Ne Idan Ya Ga Dama Ya Sadu dake Idan ya ga Dama Ya Bar ki. Amma Kuma Yayi Adalci Yayi Abinda ya ga Zai iya Domin Auren ku a Samun Zaman Lafiya.

(2) Imamul Shafi'i Allah Ya Kara Yarda Gare Shi Yace Bai Zama Wajibi a Tilastawa Miji Wai Ya Sadu da Matar sa ba, Yace Domin Kamar Misalin ne Mutum Ya Gina Gidan Haya ga Ɗakuna Masu Ƙyau Idan Ya ga Dama ya Sa Masu Haya a Ɗakunan Idan Ya ga Dama Kuma Ya Bar Ɗaukunan a Haka ba Tare da Ya Sa kowa ba Tunda Nashi Mallakin Sa ne. Yace toh Haka Misalin Mace da Mijin ta Yake Idan ya ga Dama Ya Sadu dake idan ya ga Dama ya bar ki. Amma Kuma Shima Yace Namiji Yayi Abinda ya ga Zai iya Domin Samun Zaman Lafiya mai Ɗaurewa a Zamantakewar Auren Su tsakanin Sa da Matar shi.

(3) Imam Malik Allah Ya Kara Yarda Gare Shi, Yana Cewa Namiji Yanada Hakkin Ya Sadu da Matar Sa a Kowanne Bayan Ƙwana (4) Sau 1 Tak, yace Domin Allah Yace Ayi Mata 4 ne, Saboda haka Hakki ne Akan Namiji Duk Bayan Ƙwana 4 yayi Jima'i da Matar Sa. Idan Matan Shi Uku ne toh Duk Bayan Ƙwana Uku ya Sadu da Mace 1. Sannan Shima Yana Cewa Abinda Ya Dace Shine Namiji Yayi Abinda Ya ga Zai Iya Domin Auren Su ya Ɗaure a Samu Zaman Lafiya.

10/02/2023

*ALLAH BAI KAYYADE LOKACIN RAMA AZUMI BA!*

'''Tambaya:'''

_ Assalamu alaikum, Dr. Mace ce ta sha Azumin shekara uku ajere saboda ciwon ulcer, kuma abin da zasu kai baki gagararsu yake ballatana ta ciyar, Menene mafita? _
'''Amsa:'''

_ Wa alaikum assalam ta jira har Allah ya bata lafiya sai ta rama, Allah madaukakin sarki a cikin Suratul Ba}ara aya ta: (185) ya sanya Ramuwar azumi ga mara lafiya a wasu kwanaki na daban don ya nuna abin a bude yake, zuwa lokacin da aka samu dama, ba tare da yin sakaci ba Allah ta'ala yasan aikin dagangan.

*Allah ne mafi sani*

_ *✍🏼DR. JAMILU YUSUF ZAREWA* _
________________________
*Za'a iya bibiyar darussan mu a👇🏼*

Facebook👉🏼 https://mobile.facebook.com/Ya-Ibadeeh-105630640871237.
_____________________
*»👉🏼DAGA ZAUREN YA- IBADEEH*📖🕋

10/02/2023

*TA KI YARDA DA MIJINTA SABODA TANA AZUMIN NAFILA?*

'''Tambaya:'''

_ AssalamuAlaikum, Malam ina da tambaya? Yaya,hukuncin Matar da miji ya bukaceta sannan tana Azumin sunna, taki ta Amince mishi. _

'''Amsa:'''

_ Wa alaikum assalam, ta yi kuskure ya k**ata ta amsa,kiran mijinta, saboda azumin sunna ya halatta a karya shi ko da babu dalili, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: * “Mai azumin nafila sarkin kansa ne ina ya ga dama ya cigaba da azumin, in kuma ya so yakarya” *.k**ar yadda Tirmizi ya rawaito a Sunan. _

Amma ya dace ta dinga shawartar mijinta aduk lokacin da zatayi Azumin nafila din domin samun sahalawa da daidaita al'amurra.

*Allah ne mafi sani*

_ *✍🏼Dr Jamilu Zarewa *_
________________________
*Za'a iya bibiyar darussan mu a👇🏼*

Facebook👉🏼 https://mobile.facebook.com/Ya-Ibadeeh-105630640871237.
_____________________
*»👉🏼DAGA ZAUREN YA- IBADEEH*📖🕋

Address

No. 7 Yahya Madaki Way Katsina
Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ya-Ibadeeh posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category