25/05/2026
Subhaanallah 😢
'Yan Sandan jihar Katsina sun Chafke Masu Garkuwa Da Mutane Domin Neman Kudin Fansa, A Ciki Hadda Wani Nura Aliyu Garwa Wanda SSA on Community Development na Goman jihar Katsina Mln Dikko Umar Radda, Wanda Ya Ajiye Muqamin shi bada dadewa ba domin yayi takara Kamar yadda Dokar zabe ta tanadar da duk Wanda keda Muqamin Siyasa Idan zaiyi takara to zai ajiye Muqamin sa.
Wannan Nura Ance shine Jagoran kungiyar Tasu, kuma maƙwabcine ga yaron da aka sace din mai shekaru takwas (8) a cikin birnin Katsina wanda akayi ta bada cigiyar shi.
Masu garkuwar sun nemi kuÉ—in fansa har Naira miliyan 50, amma an biya Naira miliyan 17 kafin a sako yaron.
Allah Ya Cigaba da tona Muku Asiri!!!..